1 Corinthians 12 (BOHCB)
1 To, game da baye-baye na ruhaniya, ’yan’uwa, ba na so ku kasance da rashin sani. 2 Kun san cewa sa’ad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana. 3 Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi. 4 Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. 5 Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne. 6 Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane. 7 An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10 Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. 11 Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so. 12 Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi. 13 Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko ’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha. 14 To, ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa. 15 Da ƙafa za tă ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba. 16 Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba. 17 Da a ce dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma a ce dukan jiki kunne ne, da me za a sansana? 18 Tabbatacce, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama. 19 Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20 Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya. 21 Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!” 22 A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci. 23 Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Sa’an nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu, 24 gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani, 25 don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna. 26 In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare. 27 To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28 A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri. 29 Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki? 30 Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara? 31 Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma.Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.
In Other Versions
1 Corinthians 12 in the ANGEFD
1 Corinthians 12 in the ANTPNG2D
1 Corinthians 12 in the BNTABOOT
1 Corinthians 12 in the BOATCB
1 Corinthians 12 in the BOATCB2
1 Corinthians 12 in the BOGWICC
1 Corinthians 12 in the BOHLNT
1 Corinthians 12 in the BOHNTLTAL
1 Corinthians 12 in the BOILNTAP
1 Corinthians 12 in the BOITCV
1 Corinthians 12 in the BOKCV2
1 Corinthians 12 in the BOKHWOG
1 Corinthians 12 in the BOKSSV
1 Corinthians 12 in the BOLCB2
1 Corinthians 12 in the BONUT2
1 Corinthians 12 in the BOPLNT
1 Corinthians 12 in the BOTLNT
1 Corinthians 12 in the KBT1ETNIK
1 Corinthians 12 in the SBIBS2
1 Corinthians 12 in the SBIIS2
1 Corinthians 12 in the SBIIS3
1 Corinthians 12 in the SBIKS2
1 Corinthians 12 in the SBITS2
1 Corinthians 12 in the SBITS3
1 Corinthians 12 in the SBITS4
1 Corinthians 12 in the TBIAOTANT
1 Corinthians 12 in the TBT1E2