1 Corinthians 15 (BOHCB)

1 To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai. 2 Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan. 3 Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi, 4 cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi, 5 cewa ya bayyana ga Bitrus, sa’an nan ga Sha Biyun. 6 Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ’yan’uwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci. 7 Sa’an nan ya bayyana ga Yaƙub, sa’an nan ga dukan manzannin, 8 a ƙarshe duka, ya bayyana a gare ni, kamar wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba. 9 Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah. 10 Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne. 11 To, ko ni ne, ko su ne, wannan shi ne abin da muke wa’azi, shi ne kuma abin da kuka gaskata. 12 Amma in ana wa’azi cewa Kiristi ya tashi daga matattu, yaya waɗansu a cikinku suke cewa babu tashin matattu? 13 In babu tashin matattu, to, ba a tā da Kiristi ma ba ke nan. 14 In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, wa’azinmu, da bangaskiyarku banza ne. 15 Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a tā da matattu. 16 Gama in ba a tā da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan. 17 In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan. 18 Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan. 19 In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane. 20 Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci. 21 Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum. 22 Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi. 23 Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa. 24 Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. 25 Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. 26 Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa. 27 Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi. 28 Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome. 29 To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a tā da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su? 30 Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace sa’a? 31 Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. 32 In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai,“Sai mu ci mu sha,da yake gobe za mu mutu.” 33 Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.” 34 Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba, na faɗi wannan ne don ku kunyata. 35 Amma wani yana iya tambaya yă ce, “Ta yaya ake tā da matattun? Da wane irin jiki za su tashi?” 36 Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu. 37 Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam. 38 Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta. 39 Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu. 40 Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take. 41 Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja. 42 Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; 43 akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; 44 akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya.In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma. 45 Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. 46 Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. 47 Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. 48 Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. 49 Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama. 50 Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. 51 Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu 52 farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. 53 Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. 54 Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” 55 “Ya ke mutuwa, ina nasararki?Ya ke mutuwa, ina dafinki?” 56 Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

In Other Versions

1 Corinthians 15 in the ANGEFD

1 Corinthians 15 in the ANTPNG2D

1 Corinthians 15 in the AS21

1 Corinthians 15 in the BAGH

1 Corinthians 15 in the BBPNG

1 Corinthians 15 in the BBT1E

1 Corinthians 15 in the BDS

1 Corinthians 15 in the BEV

1 Corinthians 15 in the BHAD

1 Corinthians 15 in the BIB

1 Corinthians 15 in the BLPT

1 Corinthians 15 in the BNT

1 Corinthians 15 in the BNTABOOT

1 Corinthians 15 in the BNTLV

1 Corinthians 15 in the BOATCB

1 Corinthians 15 in the BOATCB2

1 Corinthians 15 in the BOBCV

1 Corinthians 15 in the BOCNT

1 Corinthians 15 in the BOECS

1 Corinthians 15 in the BOGWICC

1 Corinthians 15 in the BOHCV

1 Corinthians 15 in the BOHLNT

1 Corinthians 15 in the BOHNTLTAL

1 Corinthians 15 in the BOICB

1 Corinthians 15 in the BOILNTAP

1 Corinthians 15 in the BOITCV

1 Corinthians 15 in the BOKCV

1 Corinthians 15 in the BOKCV2

1 Corinthians 15 in the BOKHWOG

1 Corinthians 15 in the BOKSSV

1 Corinthians 15 in the BOLCB

1 Corinthians 15 in the BOLCB2

1 Corinthians 15 in the BOMCV

1 Corinthians 15 in the BONAV

1 Corinthians 15 in the BONCB

1 Corinthians 15 in the BONLT

1 Corinthians 15 in the BONUT2

1 Corinthians 15 in the BOPLNT

1 Corinthians 15 in the BOSCB

1 Corinthians 15 in the BOSNC

1 Corinthians 15 in the BOTLNT

1 Corinthians 15 in the BOVCB

1 Corinthians 15 in the BOYCB

1 Corinthians 15 in the BPBB

1 Corinthians 15 in the BPH

1 Corinthians 15 in the BSB

1 Corinthians 15 in the CCB

1 Corinthians 15 in the CUV

1 Corinthians 15 in the CUVS

1 Corinthians 15 in the DBT

1 Corinthians 15 in the DGDNT

1 Corinthians 15 in the DHNT

1 Corinthians 15 in the DNT

1 Corinthians 15 in the ELBE

1 Corinthians 15 in the EMTV

1 Corinthians 15 in the ESV

1 Corinthians 15 in the FBV

1 Corinthians 15 in the FEB

1 Corinthians 15 in the GGMNT

1 Corinthians 15 in the GNT

1 Corinthians 15 in the HARY

1 Corinthians 15 in the HNT

1 Corinthians 15 in the IRVA

1 Corinthians 15 in the IRVB

1 Corinthians 15 in the IRVG

1 Corinthians 15 in the IRVH

1 Corinthians 15 in the IRVK

1 Corinthians 15 in the IRVM

1 Corinthians 15 in the IRVM2

1 Corinthians 15 in the IRVO

1 Corinthians 15 in the IRVP

1 Corinthians 15 in the IRVT

1 Corinthians 15 in the IRVT2

1 Corinthians 15 in the IRVU

1 Corinthians 15 in the ISVN

1 Corinthians 15 in the JSNT

1 Corinthians 15 in the KAPI

1 Corinthians 15 in the KBT1ETNIK

1 Corinthians 15 in the KBV

1 Corinthians 15 in the KJV

1 Corinthians 15 in the KNFD

1 Corinthians 15 in the LBA

1 Corinthians 15 in the LBLA

1 Corinthians 15 in the LNT

1 Corinthians 15 in the LSV

1 Corinthians 15 in the MAAL

1 Corinthians 15 in the MBV

1 Corinthians 15 in the MBV2

1 Corinthians 15 in the MHNT

1 Corinthians 15 in the MKNFD

1 Corinthians 15 in the MNG

1 Corinthians 15 in the MNT

1 Corinthians 15 in the MNT2

1 Corinthians 15 in the MRS1T

1 Corinthians 15 in the NAA

1 Corinthians 15 in the NASB

1 Corinthians 15 in the NBLA

1 Corinthians 15 in the NBS

1 Corinthians 15 in the NBVTP

1 Corinthians 15 in the NET2

1 Corinthians 15 in the NIV11

1 Corinthians 15 in the NNT

1 Corinthians 15 in the NNT2

1 Corinthians 15 in the NNT3

1 Corinthians 15 in the PDDPT

1 Corinthians 15 in the PFNT

1 Corinthians 15 in the RMNT

1 Corinthians 15 in the SBIAS

1 Corinthians 15 in the SBIBS

1 Corinthians 15 in the SBIBS2

1 Corinthians 15 in the SBICS

1 Corinthians 15 in the SBIDS

1 Corinthians 15 in the SBIGS

1 Corinthians 15 in the SBIHS

1 Corinthians 15 in the SBIIS

1 Corinthians 15 in the SBIIS2

1 Corinthians 15 in the SBIIS3

1 Corinthians 15 in the SBIKS

1 Corinthians 15 in the SBIKS2

1 Corinthians 15 in the SBIMS

1 Corinthians 15 in the SBIOS

1 Corinthians 15 in the SBIPS

1 Corinthians 15 in the SBISS

1 Corinthians 15 in the SBITS

1 Corinthians 15 in the SBITS2

1 Corinthians 15 in the SBITS3

1 Corinthians 15 in the SBITS4

1 Corinthians 15 in the SBIUS

1 Corinthians 15 in the SBIVS

1 Corinthians 15 in the SBT

1 Corinthians 15 in the SBT1E

1 Corinthians 15 in the SCHL

1 Corinthians 15 in the SNT

1 Corinthians 15 in the SUSU

1 Corinthians 15 in the SUSU2

1 Corinthians 15 in the SYNO

1 Corinthians 15 in the TBIAOTANT

1 Corinthians 15 in the TBT1E

1 Corinthians 15 in the TBT1E2

1 Corinthians 15 in the TFTIP

1 Corinthians 15 in the TFTU

1 Corinthians 15 in the TGNTATF3T

1 Corinthians 15 in the THAI

1 Corinthians 15 in the TNFD

1 Corinthians 15 in the TNT

1 Corinthians 15 in the TNTIK

1 Corinthians 15 in the TNTIL

1 Corinthians 15 in the TNTIN

1 Corinthians 15 in the TNTIP

1 Corinthians 15 in the TNTIZ

1 Corinthians 15 in the TOMA

1 Corinthians 15 in the TTENT

1 Corinthians 15 in the UBG

1 Corinthians 15 in the UGV

1 Corinthians 15 in the UGV2

1 Corinthians 15 in the UGV3

1 Corinthians 15 in the VBL

1 Corinthians 15 in the VDCC

1 Corinthians 15 in the YALU

1 Corinthians 15 in the YAPE

1 Corinthians 15 in the YBVTP

1 Corinthians 15 in the ZBP