1 John 5 (BOHCB)
1 Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2 Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3 Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4 domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. 5 Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne. 6 Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya. 7 Akwai shaidu uku, wato, 8 Ruhu, da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. 9 Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10 Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. 11 Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. 12 Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai. 13 Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. 14 Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. 15 In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan. 16 Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba. 17 Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa. 18 Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba. 19 Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun. 20 Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada. 21 ’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka.
In Other Versions
1 John 5 in the ANGEFD
1 John 5 in the ANTPNG2D
1 John 5 in the AS21
1 John 5 in the BAGH
1 John 5 in the BBPNG
1 John 5 in the BBT1E
1 John 5 in the BDS
1 John 5 in the BEV
1 John 5 in the BHAD
1 John 5 in the BIB
1 John 5 in the BLPT
1 John 5 in the BNT
1 John 5 in the BNTABOOT
1 John 5 in the BNTLV
1 John 5 in the BOATCB
1 John 5 in the BOATCB2
1 John 5 in the BOBCV
1 John 5 in the BOCNT
1 John 5 in the BOECS
1 John 5 in the BOGWICC
1 John 5 in the BOHCV
1 John 5 in the BOHLNT
1 John 5 in the BOHNTLTAL
1 John 5 in the BOICB
1 John 5 in the BOILNTAP
1 John 5 in the BOITCV
1 John 5 in the BOKCV
1 John 5 in the BOKCV2
1 John 5 in the BOKHWOG
1 John 5 in the BOKSSV
1 John 5 in the BOLCB
1 John 5 in the BOLCB2
1 John 5 in the BOMCV
1 John 5 in the BONAV
1 John 5 in the BONCB
1 John 5 in the BONLT
1 John 5 in the BONUT2
1 John 5 in the BOPLNT
1 John 5 in the BOSCB
1 John 5 in the BOSNC
1 John 5 in the BOTLNT
1 John 5 in the BOVCB
1 John 5 in the BOYCB
1 John 5 in the BPBB
1 John 5 in the BPH
1 John 5 in the BSB
1 John 5 in the CCB
1 John 5 in the CUV
1 John 5 in the CUVS
1 John 5 in the DBT
1 John 5 in the DGDNT
1 John 5 in the DHNT
1 John 5 in the DNT
1 John 5 in the ELBE
1 John 5 in the EMTV
1 John 5 in the ESV
1 John 5 in the FBV
1 John 5 in the FEB
1 John 5 in the GGMNT
1 John 5 in the GNT
1 John 5 in the HARY
1 John 5 in the HNT
1 John 5 in the IRVA
1 John 5 in the IRVB
1 John 5 in the IRVG
1 John 5 in the IRVH
1 John 5 in the IRVK
1 John 5 in the IRVM
1 John 5 in the IRVM2
1 John 5 in the IRVO
1 John 5 in the IRVP
1 John 5 in the IRVT
1 John 5 in the IRVT2
1 John 5 in the IRVU
1 John 5 in the ISVN
1 John 5 in the JSNT
1 John 5 in the KAPI
1 John 5 in the KBT1ETNIK
1 John 5 in the KBV
1 John 5 in the KJV
1 John 5 in the KNFD
1 John 5 in the LBA
1 John 5 in the LBLA
1 John 5 in the LNT
1 John 5 in the LSV
1 John 5 in the MAAL
1 John 5 in the MBV
1 John 5 in the MBV2
1 John 5 in the MHNT
1 John 5 in the MKNFD
1 John 5 in the MNG
1 John 5 in the MNT
1 John 5 in the MNT2
1 John 5 in the MRS1T
1 John 5 in the NAA
1 John 5 in the NASB
1 John 5 in the NBLA
1 John 5 in the NBS
1 John 5 in the NBVTP
1 John 5 in the NET2
1 John 5 in the NIV11
1 John 5 in the NNT
1 John 5 in the NNT2
1 John 5 in the NNT3
1 John 5 in the PDDPT
1 John 5 in the PFNT
1 John 5 in the RMNT
1 John 5 in the SBIAS
1 John 5 in the SBIBS
1 John 5 in the SBIBS2
1 John 5 in the SBICS
1 John 5 in the SBIDS
1 John 5 in the SBIGS
1 John 5 in the SBIHS
1 John 5 in the SBIIS
1 John 5 in the SBIIS2
1 John 5 in the SBIIS3
1 John 5 in the SBIKS
1 John 5 in the SBIKS2
1 John 5 in the SBIMS
1 John 5 in the SBIOS
1 John 5 in the SBIPS
1 John 5 in the SBISS
1 John 5 in the SBITS
1 John 5 in the SBITS2
1 John 5 in the SBITS3
1 John 5 in the SBITS4
1 John 5 in the SBIUS
1 John 5 in the SBIVS
1 John 5 in the SBT
1 John 5 in the SBT1E
1 John 5 in the SCHL
1 John 5 in the SNT
1 John 5 in the SUSU
1 John 5 in the SUSU2
1 John 5 in the SYNO
1 John 5 in the TBIAOTANT
1 John 5 in the TBT1E
1 John 5 in the TBT1E2
1 John 5 in the TFTIP
1 John 5 in the TFTU
1 John 5 in the TGNTATF3T
1 John 5 in the THAI
1 John 5 in the TNFD
1 John 5 in the TNT
1 John 5 in the TNTIK
1 John 5 in the TNTIL
1 John 5 in the TNTIN
1 John 5 in the TNTIP
1 John 5 in the TNTIZ
1 John 5 in the TOMA
1 John 5 in the TTENT
1 John 5 in the UBG
1 John 5 in the UGV
1 John 5 in the UGV2
1 John 5 in the UGV3
1 John 5 in the VBL
1 John 5 in the VDCC
1 John 5 in the YALU
1 John 5 in the YAPE
1 John 5 in the YBVTP
1 John 5 in the ZBP