1 Thessalonians 3 (BOHCB)
1 Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai. 2 Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku, 3 don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. 4 Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani. 5 Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza. 6 Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku. 7 Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku. 8 Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji. 9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10 Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku. 11 Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku. 12 Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku. 13 Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.
In Other Versions
1 Thessalonians 3 in the ANGEFD
1 Thessalonians 3 in the ANTPNG2D
1 Thessalonians 3 in the BBPNG
1 Thessalonians 3 in the BBT1E
1 Thessalonians 3 in the BNTABOOT
1 Thessalonians 3 in the BNTLV
1 Thessalonians 3 in the BOATCB
1 Thessalonians 3 in the BOATCB2
1 Thessalonians 3 in the BOBCV
1 Thessalonians 3 in the BOCNT
1 Thessalonians 3 in the BOECS
1 Thessalonians 3 in the BOGWICC
1 Thessalonians 3 in the BOHCV
1 Thessalonians 3 in the BOHLNT
1 Thessalonians 3 in the BOHNTLTAL
1 Thessalonians 3 in the BOICB
1 Thessalonians 3 in the BOILNTAP
1 Thessalonians 3 in the BOITCV
1 Thessalonians 3 in the BOKCV
1 Thessalonians 3 in the BOKCV2
1 Thessalonians 3 in the BOKHWOG
1 Thessalonians 3 in the BOKSSV
1 Thessalonians 3 in the BOLCB
1 Thessalonians 3 in the BOLCB2
1 Thessalonians 3 in the BOMCV
1 Thessalonians 3 in the BONAV
1 Thessalonians 3 in the BONCB
1 Thessalonians 3 in the BONLT
1 Thessalonians 3 in the BONUT2
1 Thessalonians 3 in the BOPLNT
1 Thessalonians 3 in the BOSCB
1 Thessalonians 3 in the BOSNC
1 Thessalonians 3 in the BOTLNT
1 Thessalonians 3 in the BOVCB
1 Thessalonians 3 in the BOYCB
1 Thessalonians 3 in the DGDNT
1 Thessalonians 3 in the GGMNT
1 Thessalonians 3 in the IRVM2
1 Thessalonians 3 in the IRVT2
1 Thessalonians 3 in the KBT1ETNIK
1 Thessalonians 3 in the MKNFD
1 Thessalonians 3 in the MRS1T
1 Thessalonians 3 in the NBVTP
1 Thessalonians 3 in the NIV11
1 Thessalonians 3 in the PDDPT
1 Thessalonians 3 in the SBIAS
1 Thessalonians 3 in the SBIBS
1 Thessalonians 3 in the SBIBS2
1 Thessalonians 3 in the SBICS
1 Thessalonians 3 in the SBIDS
1 Thessalonians 3 in the SBIGS
1 Thessalonians 3 in the SBIHS
1 Thessalonians 3 in the SBIIS
1 Thessalonians 3 in the SBIIS2
1 Thessalonians 3 in the SBIIS3
1 Thessalonians 3 in the SBIKS
1 Thessalonians 3 in the SBIKS2
1 Thessalonians 3 in the SBIMS
1 Thessalonians 3 in the SBIOS
1 Thessalonians 3 in the SBIPS
1 Thessalonians 3 in the SBISS
1 Thessalonians 3 in the SBITS
1 Thessalonians 3 in the SBITS2
1 Thessalonians 3 in the SBITS3
1 Thessalonians 3 in the SBITS4
1 Thessalonians 3 in the SBIUS
1 Thessalonians 3 in the SBIVS
1 Thessalonians 3 in the SBT1E
1 Thessalonians 3 in the SUSU2
1 Thessalonians 3 in the TBIAOTANT
1 Thessalonians 3 in the TBT1E
1 Thessalonians 3 in the TBT1E2
1 Thessalonians 3 in the TFTIP
1 Thessalonians 3 in the TGNTATF3T
1 Thessalonians 3 in the TNTIK
1 Thessalonians 3 in the TNTIL
1 Thessalonians 3 in the TNTIN
1 Thessalonians 3 in the TNTIP
1 Thessalonians 3 in the TNTIZ
1 Thessalonians 3 in the TTENT