2 Corinthians 1 (BOHCB)

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya. 2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. 3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. 7 Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu. 8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. 9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu, 11 yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa. 12 Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba. 13 Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa, 14 kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo. 15 Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. 16 Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya. 17 Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”? 18 Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce. 19 Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum. 20 Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. 21 Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, 22 ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba. 23 Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba. 24 Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.

In Other Versions

2 Corinthians 1 in the ANGEFD

2 Corinthians 1 in the ANTPNG2D

2 Corinthians 1 in the AS21

2 Corinthians 1 in the BAGH

2 Corinthians 1 in the BBPNG

2 Corinthians 1 in the BBT1E

2 Corinthians 1 in the BDS

2 Corinthians 1 in the BEV

2 Corinthians 1 in the BHAD

2 Corinthians 1 in the BIB

2 Corinthians 1 in the BLPT

2 Corinthians 1 in the BNT

2 Corinthians 1 in the BNTABOOT

2 Corinthians 1 in the BNTLV

2 Corinthians 1 in the BOATCB

2 Corinthians 1 in the BOATCB2

2 Corinthians 1 in the BOBCV

2 Corinthians 1 in the BOCNT

2 Corinthians 1 in the BOECS

2 Corinthians 1 in the BOGWICC

2 Corinthians 1 in the BOHCV

2 Corinthians 1 in the BOHLNT

2 Corinthians 1 in the BOHNTLTAL

2 Corinthians 1 in the BOICB

2 Corinthians 1 in the BOILNTAP

2 Corinthians 1 in the BOITCV

2 Corinthians 1 in the BOKCV

2 Corinthians 1 in the BOKCV2

2 Corinthians 1 in the BOKHWOG

2 Corinthians 1 in the BOKSSV

2 Corinthians 1 in the BOLCB

2 Corinthians 1 in the BOLCB2

2 Corinthians 1 in the BOMCV

2 Corinthians 1 in the BONAV

2 Corinthians 1 in the BONCB

2 Corinthians 1 in the BONLT

2 Corinthians 1 in the BONUT2

2 Corinthians 1 in the BOPLNT

2 Corinthians 1 in the BOSCB

2 Corinthians 1 in the BOSNC

2 Corinthians 1 in the BOTLNT

2 Corinthians 1 in the BOVCB

2 Corinthians 1 in the BOYCB

2 Corinthians 1 in the BPBB

2 Corinthians 1 in the BPH

2 Corinthians 1 in the BSB

2 Corinthians 1 in the CCB

2 Corinthians 1 in the CUV

2 Corinthians 1 in the CUVS

2 Corinthians 1 in the DBT

2 Corinthians 1 in the DGDNT

2 Corinthians 1 in the DHNT

2 Corinthians 1 in the DNT

2 Corinthians 1 in the ELBE

2 Corinthians 1 in the EMTV

2 Corinthians 1 in the ESV

2 Corinthians 1 in the FBV

2 Corinthians 1 in the FEB

2 Corinthians 1 in the GGMNT

2 Corinthians 1 in the GNT

2 Corinthians 1 in the HARY

2 Corinthians 1 in the HNT

2 Corinthians 1 in the IRVA

2 Corinthians 1 in the IRVB

2 Corinthians 1 in the IRVG

2 Corinthians 1 in the IRVH

2 Corinthians 1 in the IRVK

2 Corinthians 1 in the IRVM

2 Corinthians 1 in the IRVM2

2 Corinthians 1 in the IRVO

2 Corinthians 1 in the IRVP

2 Corinthians 1 in the IRVT

2 Corinthians 1 in the IRVT2

2 Corinthians 1 in the IRVU

2 Corinthians 1 in the ISVN

2 Corinthians 1 in the JSNT

2 Corinthians 1 in the KAPI

2 Corinthians 1 in the KBT1ETNIK

2 Corinthians 1 in the KBV

2 Corinthians 1 in the KJV

2 Corinthians 1 in the KNFD

2 Corinthians 1 in the LBA

2 Corinthians 1 in the LBLA

2 Corinthians 1 in the LNT

2 Corinthians 1 in the LSV

2 Corinthians 1 in the MAAL

2 Corinthians 1 in the MBV

2 Corinthians 1 in the MBV2

2 Corinthians 1 in the MHNT

2 Corinthians 1 in the MKNFD

2 Corinthians 1 in the MNG

2 Corinthians 1 in the MNT

2 Corinthians 1 in the MNT2

2 Corinthians 1 in the MRS1T

2 Corinthians 1 in the NAA

2 Corinthians 1 in the NASB

2 Corinthians 1 in the NBLA

2 Corinthians 1 in the NBS

2 Corinthians 1 in the NBVTP

2 Corinthians 1 in the NET2

2 Corinthians 1 in the NIV11

2 Corinthians 1 in the NNT

2 Corinthians 1 in the NNT2

2 Corinthians 1 in the NNT3

2 Corinthians 1 in the PDDPT

2 Corinthians 1 in the PFNT

2 Corinthians 1 in the RMNT

2 Corinthians 1 in the SBIAS

2 Corinthians 1 in the SBIBS

2 Corinthians 1 in the SBIBS2

2 Corinthians 1 in the SBICS

2 Corinthians 1 in the SBIDS

2 Corinthians 1 in the SBIGS

2 Corinthians 1 in the SBIHS

2 Corinthians 1 in the SBIIS

2 Corinthians 1 in the SBIIS2

2 Corinthians 1 in the SBIIS3

2 Corinthians 1 in the SBIKS

2 Corinthians 1 in the SBIKS2

2 Corinthians 1 in the SBIMS

2 Corinthians 1 in the SBIOS

2 Corinthians 1 in the SBIPS

2 Corinthians 1 in the SBISS

2 Corinthians 1 in the SBITS

2 Corinthians 1 in the SBITS2

2 Corinthians 1 in the SBITS3

2 Corinthians 1 in the SBITS4

2 Corinthians 1 in the SBIUS

2 Corinthians 1 in the SBIVS

2 Corinthians 1 in the SBT

2 Corinthians 1 in the SBT1E

2 Corinthians 1 in the SCHL

2 Corinthians 1 in the SNT

2 Corinthians 1 in the SUSU

2 Corinthians 1 in the SUSU2

2 Corinthians 1 in the SYNO

2 Corinthians 1 in the TBIAOTANT

2 Corinthians 1 in the TBT1E

2 Corinthians 1 in the TBT1E2

2 Corinthians 1 in the TFTIP

2 Corinthians 1 in the TFTU

2 Corinthians 1 in the TGNTATF3T

2 Corinthians 1 in the THAI

2 Corinthians 1 in the TNFD

2 Corinthians 1 in the TNT

2 Corinthians 1 in the TNTIK

2 Corinthians 1 in the TNTIL

2 Corinthians 1 in the TNTIN

2 Corinthians 1 in the TNTIP

2 Corinthians 1 in the TNTIZ

2 Corinthians 1 in the TOMA

2 Corinthians 1 in the TTENT

2 Corinthians 1 in the UBG

2 Corinthians 1 in the UGV

2 Corinthians 1 in the UGV2

2 Corinthians 1 in the UGV3

2 Corinthians 1 in the VBL

2 Corinthians 1 in the VDCC

2 Corinthians 1 in the YALU

2 Corinthians 1 in the YAPE

2 Corinthians 1 in the YBVTP

2 Corinthians 1 in the ZBP