2 Thessalonians 1 (BOHCB)
1 Bulus, da Sila, da Timoti, Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi. 2 Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. 3 Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4 Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha. 5 Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. 6 Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala 7 yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. 8 Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. 9 Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa 10 a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku. 11 Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. 12 Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.
In Other Versions
2 Thessalonians 1 in the ANGEFD
2 Thessalonians 1 in the ANTPNG2D
2 Thessalonians 1 in the BBPNG
2 Thessalonians 1 in the BBT1E
2 Thessalonians 1 in the BNTABOOT
2 Thessalonians 1 in the BNTLV
2 Thessalonians 1 in the BOATCB
2 Thessalonians 1 in the BOATCB2
2 Thessalonians 1 in the BOBCV
2 Thessalonians 1 in the BOCNT
2 Thessalonians 1 in the BOECS
2 Thessalonians 1 in the BOGWICC
2 Thessalonians 1 in the BOHCV
2 Thessalonians 1 in the BOHLNT
2 Thessalonians 1 in the BOHNTLTAL
2 Thessalonians 1 in the BOICB
2 Thessalonians 1 in the BOILNTAP
2 Thessalonians 1 in the BOITCV
2 Thessalonians 1 in the BOKCV
2 Thessalonians 1 in the BOKCV2
2 Thessalonians 1 in the BOKHWOG
2 Thessalonians 1 in the BOKSSV
2 Thessalonians 1 in the BOLCB
2 Thessalonians 1 in the BOLCB2
2 Thessalonians 1 in the BOMCV
2 Thessalonians 1 in the BONAV
2 Thessalonians 1 in the BONCB
2 Thessalonians 1 in the BONLT
2 Thessalonians 1 in the BONUT2
2 Thessalonians 1 in the BOPLNT
2 Thessalonians 1 in the BOSCB
2 Thessalonians 1 in the BOSNC
2 Thessalonians 1 in the BOTLNT
2 Thessalonians 1 in the BOVCB
2 Thessalonians 1 in the BOYCB
2 Thessalonians 1 in the DGDNT
2 Thessalonians 1 in the GGMNT
2 Thessalonians 1 in the IRVM2
2 Thessalonians 1 in the IRVT2
2 Thessalonians 1 in the KBT1ETNIK
2 Thessalonians 1 in the MKNFD
2 Thessalonians 1 in the MRS1T
2 Thessalonians 1 in the NBVTP
2 Thessalonians 1 in the NIV11
2 Thessalonians 1 in the PDDPT
2 Thessalonians 1 in the SBIAS
2 Thessalonians 1 in the SBIBS
2 Thessalonians 1 in the SBIBS2
2 Thessalonians 1 in the SBICS
2 Thessalonians 1 in the SBIDS
2 Thessalonians 1 in the SBIGS
2 Thessalonians 1 in the SBIHS
2 Thessalonians 1 in the SBIIS
2 Thessalonians 1 in the SBIIS2
2 Thessalonians 1 in the SBIIS3
2 Thessalonians 1 in the SBIKS
2 Thessalonians 1 in the SBIKS2
2 Thessalonians 1 in the SBIMS
2 Thessalonians 1 in the SBIOS
2 Thessalonians 1 in the SBIPS
2 Thessalonians 1 in the SBISS
2 Thessalonians 1 in the SBITS
2 Thessalonians 1 in the SBITS2
2 Thessalonians 1 in the SBITS3
2 Thessalonians 1 in the SBITS4
2 Thessalonians 1 in the SBIUS
2 Thessalonians 1 in the SBIVS
2 Thessalonians 1 in the SBT1E
2 Thessalonians 1 in the SUSU2
2 Thessalonians 1 in the TBIAOTANT
2 Thessalonians 1 in the TBT1E
2 Thessalonians 1 in the TBT1E2
2 Thessalonians 1 in the TFTIP
2 Thessalonians 1 in the TGNTATF3T
2 Thessalonians 1 in the TNTIK
2 Thessalonians 1 in the TNTIL
2 Thessalonians 1 in the TNTIN
2 Thessalonians 1 in the TNTIP
2 Thessalonians 1 in the TNTIZ
2 Thessalonians 1 in the TTENT