2 Timothy 4 (BOHCB)

1 A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni. 2 Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. 3 Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. 4 Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi. 5 Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka. 6 Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi. 7 Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. 8 Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa. 9 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri, 10 gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. 11 Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata. 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisa. 13 Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba. 14 Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi. 15 Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu. 16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. 19 Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus. 20 Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus. 21 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina. Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa. 22 Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku.

In Other Versions

2 Timothy 4 in the ANGEFD

2 Timothy 4 in the ANTPNG2D

2 Timothy 4 in the AS21

2 Timothy 4 in the BAGH

2 Timothy 4 in the BBPNG

2 Timothy 4 in the BBT1E

2 Timothy 4 in the BDS

2 Timothy 4 in the BEV

2 Timothy 4 in the BHAD

2 Timothy 4 in the BIB

2 Timothy 4 in the BLPT

2 Timothy 4 in the BNT

2 Timothy 4 in the BNTABOOT

2 Timothy 4 in the BNTLV

2 Timothy 4 in the BOATCB

2 Timothy 4 in the BOATCB2

2 Timothy 4 in the BOBCV

2 Timothy 4 in the BOCNT

2 Timothy 4 in the BOECS

2 Timothy 4 in the BOGWICC

2 Timothy 4 in the BOHCV

2 Timothy 4 in the BOHLNT

2 Timothy 4 in the BOHNTLTAL

2 Timothy 4 in the BOICB

2 Timothy 4 in the BOILNTAP

2 Timothy 4 in the BOITCV

2 Timothy 4 in the BOKCV

2 Timothy 4 in the BOKCV2

2 Timothy 4 in the BOKHWOG

2 Timothy 4 in the BOKSSV

2 Timothy 4 in the BOLCB

2 Timothy 4 in the BOLCB2

2 Timothy 4 in the BOMCV

2 Timothy 4 in the BONAV

2 Timothy 4 in the BONCB

2 Timothy 4 in the BONLT

2 Timothy 4 in the BONUT2

2 Timothy 4 in the BOPLNT

2 Timothy 4 in the BOSCB

2 Timothy 4 in the BOSNC

2 Timothy 4 in the BOTLNT

2 Timothy 4 in the BOVCB

2 Timothy 4 in the BOYCB

2 Timothy 4 in the BPBB

2 Timothy 4 in the BPH

2 Timothy 4 in the BSB

2 Timothy 4 in the CCB

2 Timothy 4 in the CUV

2 Timothy 4 in the CUVS

2 Timothy 4 in the DBT

2 Timothy 4 in the DGDNT

2 Timothy 4 in the DHNT

2 Timothy 4 in the DNT

2 Timothy 4 in the ELBE

2 Timothy 4 in the EMTV

2 Timothy 4 in the ESV

2 Timothy 4 in the FBV

2 Timothy 4 in the FEB

2 Timothy 4 in the GGMNT

2 Timothy 4 in the GNT

2 Timothy 4 in the HARY

2 Timothy 4 in the HNT

2 Timothy 4 in the IRVA

2 Timothy 4 in the IRVB

2 Timothy 4 in the IRVG

2 Timothy 4 in the IRVH

2 Timothy 4 in the IRVK

2 Timothy 4 in the IRVM

2 Timothy 4 in the IRVM2

2 Timothy 4 in the IRVO

2 Timothy 4 in the IRVP

2 Timothy 4 in the IRVT

2 Timothy 4 in the IRVT2

2 Timothy 4 in the IRVU

2 Timothy 4 in the ISVN

2 Timothy 4 in the JSNT

2 Timothy 4 in the KAPI

2 Timothy 4 in the KBT1ETNIK

2 Timothy 4 in the KBV

2 Timothy 4 in the KJV

2 Timothy 4 in the KNFD

2 Timothy 4 in the LBA

2 Timothy 4 in the LBLA

2 Timothy 4 in the LNT

2 Timothy 4 in the LSV

2 Timothy 4 in the MAAL

2 Timothy 4 in the MBV

2 Timothy 4 in the MBV2

2 Timothy 4 in the MHNT

2 Timothy 4 in the MKNFD

2 Timothy 4 in the MNG

2 Timothy 4 in the MNT

2 Timothy 4 in the MNT2

2 Timothy 4 in the MRS1T

2 Timothy 4 in the NAA

2 Timothy 4 in the NASB

2 Timothy 4 in the NBLA

2 Timothy 4 in the NBS

2 Timothy 4 in the NBVTP

2 Timothy 4 in the NET2

2 Timothy 4 in the NIV11

2 Timothy 4 in the NNT

2 Timothy 4 in the NNT2

2 Timothy 4 in the NNT3

2 Timothy 4 in the PDDPT

2 Timothy 4 in the PFNT

2 Timothy 4 in the RMNT

2 Timothy 4 in the SBIAS

2 Timothy 4 in the SBIBS

2 Timothy 4 in the SBIBS2

2 Timothy 4 in the SBICS

2 Timothy 4 in the SBIDS

2 Timothy 4 in the SBIGS

2 Timothy 4 in the SBIHS

2 Timothy 4 in the SBIIS

2 Timothy 4 in the SBIIS2

2 Timothy 4 in the SBIIS3

2 Timothy 4 in the SBIKS

2 Timothy 4 in the SBIKS2

2 Timothy 4 in the SBIMS

2 Timothy 4 in the SBIOS

2 Timothy 4 in the SBIPS

2 Timothy 4 in the SBISS

2 Timothy 4 in the SBITS

2 Timothy 4 in the SBITS2

2 Timothy 4 in the SBITS3

2 Timothy 4 in the SBITS4

2 Timothy 4 in the SBIUS

2 Timothy 4 in the SBIVS

2 Timothy 4 in the SBT

2 Timothy 4 in the SBT1E

2 Timothy 4 in the SCHL

2 Timothy 4 in the SNT

2 Timothy 4 in the SUSU

2 Timothy 4 in the SUSU2

2 Timothy 4 in the SYNO

2 Timothy 4 in the TBIAOTANT

2 Timothy 4 in the TBT1E

2 Timothy 4 in the TBT1E2

2 Timothy 4 in the TFTIP

2 Timothy 4 in the TFTU

2 Timothy 4 in the TGNTATF3T

2 Timothy 4 in the THAI

2 Timothy 4 in the TNFD

2 Timothy 4 in the TNT

2 Timothy 4 in the TNTIK

2 Timothy 4 in the TNTIL

2 Timothy 4 in the TNTIN

2 Timothy 4 in the TNTIP

2 Timothy 4 in the TNTIZ

2 Timothy 4 in the TOMA

2 Timothy 4 in the TTENT

2 Timothy 4 in the UBG

2 Timothy 4 in the UGV

2 Timothy 4 in the UGV2

2 Timothy 4 in the UGV3

2 Timothy 4 in the VBL

2 Timothy 4 in the VDCC

2 Timothy 4 in the YALU

2 Timothy 4 in the YAPE

2 Timothy 4 in the YBVTP

2 Timothy 4 in the ZBP