Acts 23 (BOHCB)

1 Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.” 2 Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. 3 Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!” 4 Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?” 5 Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’” 6 Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.” 7 Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu. 8 (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.) 9 Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?” 10 Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja. 11 Kashegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.” 12 Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus. 13 Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci. 14 Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus. 15 Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.” 16 Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus. 17 Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.” 18 Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan.Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.” 19 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?” 20 Saurayin ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus. 21 Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.” 22 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya sallami saurayin ya kwaɓe shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka faɗa mini wannan.” 23 Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai saba’in da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan. 24 Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.” 25 Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka, 26 Kalaudiyus Lisiyas.Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis.Gaisuwa. 27 Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne. 28 Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu. 29 Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a daure shi. 30 Sa’ad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka. 31 Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris. 32 Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja. 33 Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus. 34 Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne, 35 sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Sa’an nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus.

In Other Versions

Acts 23 in the ANGEFD

Acts 23 in the ANTPNG2D

Acts 23 in the AS21

Acts 23 in the BAGH

Acts 23 in the BBPNG

Acts 23 in the BBT1E

Acts 23 in the BDS

Acts 23 in the BEV

Acts 23 in the BHAD

Acts 23 in the BIB

Acts 23 in the BLPT

Acts 23 in the BNT

Acts 23 in the BNTABOOT

Acts 23 in the BNTLV

Acts 23 in the BOATCB

Acts 23 in the BOATCB2

Acts 23 in the BOBCV

Acts 23 in the BOCNT

Acts 23 in the BOECS

Acts 23 in the BOGWICC

Acts 23 in the BOHCV

Acts 23 in the BOHLNT

Acts 23 in the BOHNTLTAL

Acts 23 in the BOICB

Acts 23 in the BOILNTAP

Acts 23 in the BOITCV

Acts 23 in the BOKCV

Acts 23 in the BOKCV2

Acts 23 in the BOKHWOG

Acts 23 in the BOKSSV

Acts 23 in the BOLCB

Acts 23 in the BOLCB2

Acts 23 in the BOMCV

Acts 23 in the BONAV

Acts 23 in the BONCB

Acts 23 in the BONLT

Acts 23 in the BONUT2

Acts 23 in the BOPLNT

Acts 23 in the BOSCB

Acts 23 in the BOSNC

Acts 23 in the BOTLNT

Acts 23 in the BOVCB

Acts 23 in the BOYCB

Acts 23 in the BPBB

Acts 23 in the BPH

Acts 23 in the BSB

Acts 23 in the CCB

Acts 23 in the CUV

Acts 23 in the CUVS

Acts 23 in the DBT

Acts 23 in the DGDNT

Acts 23 in the DHNT

Acts 23 in the DNT

Acts 23 in the ELBE

Acts 23 in the EMTV

Acts 23 in the ESV

Acts 23 in the FBV

Acts 23 in the FEB

Acts 23 in the GGMNT

Acts 23 in the GNT

Acts 23 in the HARY

Acts 23 in the HNT

Acts 23 in the IRVA

Acts 23 in the IRVB

Acts 23 in the IRVG

Acts 23 in the IRVH

Acts 23 in the IRVK

Acts 23 in the IRVM

Acts 23 in the IRVM2

Acts 23 in the IRVO

Acts 23 in the IRVP

Acts 23 in the IRVT

Acts 23 in the IRVT2

Acts 23 in the IRVU

Acts 23 in the ISVN

Acts 23 in the JSNT

Acts 23 in the KAPI

Acts 23 in the KBT1ETNIK

Acts 23 in the KBV

Acts 23 in the KJV

Acts 23 in the KNFD

Acts 23 in the LBA

Acts 23 in the LBLA

Acts 23 in the LNT

Acts 23 in the LSV

Acts 23 in the MAAL

Acts 23 in the MBV

Acts 23 in the MBV2

Acts 23 in the MHNT

Acts 23 in the MKNFD

Acts 23 in the MNG

Acts 23 in the MNT

Acts 23 in the MNT2

Acts 23 in the MRS1T

Acts 23 in the NAA

Acts 23 in the NASB

Acts 23 in the NBLA

Acts 23 in the NBS

Acts 23 in the NBVTP

Acts 23 in the NET2

Acts 23 in the NIV11

Acts 23 in the NNT

Acts 23 in the NNT2

Acts 23 in the NNT3

Acts 23 in the PDDPT

Acts 23 in the PFNT

Acts 23 in the RMNT

Acts 23 in the SBIAS

Acts 23 in the SBIBS

Acts 23 in the SBIBS2

Acts 23 in the SBICS

Acts 23 in the SBIDS

Acts 23 in the SBIGS

Acts 23 in the SBIHS

Acts 23 in the SBIIS

Acts 23 in the SBIIS2

Acts 23 in the SBIIS3

Acts 23 in the SBIKS

Acts 23 in the SBIKS2

Acts 23 in the SBIMS

Acts 23 in the SBIOS

Acts 23 in the SBIPS

Acts 23 in the SBISS

Acts 23 in the SBITS

Acts 23 in the SBITS2

Acts 23 in the SBITS3

Acts 23 in the SBITS4

Acts 23 in the SBIUS

Acts 23 in the SBIVS

Acts 23 in the SBT

Acts 23 in the SBT1E

Acts 23 in the SCHL

Acts 23 in the SNT

Acts 23 in the SUSU

Acts 23 in the SUSU2

Acts 23 in the SYNO

Acts 23 in the TBIAOTANT

Acts 23 in the TBT1E

Acts 23 in the TBT1E2

Acts 23 in the TFTIP

Acts 23 in the TFTU

Acts 23 in the TGNTATF3T

Acts 23 in the THAI

Acts 23 in the TNFD

Acts 23 in the TNT

Acts 23 in the TNTIK

Acts 23 in the TNTIL

Acts 23 in the TNTIN

Acts 23 in the TNTIP

Acts 23 in the TNTIZ

Acts 23 in the TOMA

Acts 23 in the TTENT

Acts 23 in the UBG

Acts 23 in the UGV

Acts 23 in the UGV2

Acts 23 in the UGV3

Acts 23 in the VBL

Acts 23 in the VDCC

Acts 23 in the YALU

Acts 23 in the YAPE

Acts 23 in the YBVTP

Acts 23 in the ZBP