Colossians 3 (BOHCB)
1 Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. 2 Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. 3 Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. 4 Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka. 5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. 7 Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11 A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya. 15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa. 18 Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji. 19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi. 20 ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji. 21 Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya. 22 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25 Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
In Other Versions
Colossians 3 in the ANGEFD
Colossians 3 in the ANTPNG2D
Colossians 3 in the AS21
Colossians 3 in the BAGH
Colossians 3 in the BBPNG
Colossians 3 in the BBT1E
Colossians 3 in the BDS
Colossians 3 in the BEV
Colossians 3 in the BHAD
Colossians 3 in the BIB
Colossians 3 in the BLPT
Colossians 3 in the BNT
Colossians 3 in the BNTABOOT
Colossians 3 in the BNTLV
Colossians 3 in the BOATCB
Colossians 3 in the BOATCB2
Colossians 3 in the BOBCV
Colossians 3 in the BOCNT
Colossians 3 in the BOECS
Colossians 3 in the BOGWICC
Colossians 3 in the BOHCV
Colossians 3 in the BOHLNT
Colossians 3 in the BOHNTLTAL
Colossians 3 in the BOICB
Colossians 3 in the BOILNTAP
Colossians 3 in the BOITCV
Colossians 3 in the BOKCV
Colossians 3 in the BOKCV2
Colossians 3 in the BOKHWOG
Colossians 3 in the BOKSSV
Colossians 3 in the BOLCB
Colossians 3 in the BOLCB2
Colossians 3 in the BOMCV
Colossians 3 in the BONAV
Colossians 3 in the BONCB
Colossians 3 in the BONLT
Colossians 3 in the BONUT2
Colossians 3 in the BOPLNT
Colossians 3 in the BOSCB
Colossians 3 in the BOSNC
Colossians 3 in the BOTLNT
Colossians 3 in the BOVCB
Colossians 3 in the BOYCB
Colossians 3 in the BPBB
Colossians 3 in the BPH
Colossians 3 in the BSB
Colossians 3 in the CCB
Colossians 3 in the CUV
Colossians 3 in the CUVS
Colossians 3 in the DBT
Colossians 3 in the DGDNT
Colossians 3 in the DHNT
Colossians 3 in the DNT
Colossians 3 in the ELBE
Colossians 3 in the EMTV
Colossians 3 in the ESV
Colossians 3 in the FBV
Colossians 3 in the FEB
Colossians 3 in the GGMNT
Colossians 3 in the GNT
Colossians 3 in the HARY
Colossians 3 in the HNT
Colossians 3 in the IRVA
Colossians 3 in the IRVB
Colossians 3 in the IRVG
Colossians 3 in the IRVH
Colossians 3 in the IRVK
Colossians 3 in the IRVM
Colossians 3 in the IRVM2
Colossians 3 in the IRVO
Colossians 3 in the IRVP
Colossians 3 in the IRVT
Colossians 3 in the IRVT2
Colossians 3 in the IRVU
Colossians 3 in the ISVN
Colossians 3 in the JSNT
Colossians 3 in the KAPI
Colossians 3 in the KBT1ETNIK
Colossians 3 in the KBV
Colossians 3 in the KJV
Colossians 3 in the KNFD
Colossians 3 in the LBA
Colossians 3 in the LBLA
Colossians 3 in the LNT
Colossians 3 in the LSV
Colossians 3 in the MAAL
Colossians 3 in the MBV
Colossians 3 in the MBV2
Colossians 3 in the MHNT
Colossians 3 in the MKNFD
Colossians 3 in the MNG
Colossians 3 in the MNT
Colossians 3 in the MNT2
Colossians 3 in the MRS1T
Colossians 3 in the NAA
Colossians 3 in the NASB
Colossians 3 in the NBLA
Colossians 3 in the NBS
Colossians 3 in the NBVTP
Colossians 3 in the NET2
Colossians 3 in the NIV11
Colossians 3 in the NNT
Colossians 3 in the NNT2
Colossians 3 in the NNT3
Colossians 3 in the PDDPT
Colossians 3 in the PFNT
Colossians 3 in the RMNT
Colossians 3 in the SBIAS
Colossians 3 in the SBIBS
Colossians 3 in the SBIBS2
Colossians 3 in the SBICS
Colossians 3 in the SBIDS
Colossians 3 in the SBIGS
Colossians 3 in the SBIHS
Colossians 3 in the SBIIS
Colossians 3 in the SBIIS2
Colossians 3 in the SBIIS3
Colossians 3 in the SBIKS
Colossians 3 in the SBIKS2
Colossians 3 in the SBIMS
Colossians 3 in the SBIOS
Colossians 3 in the SBIPS
Colossians 3 in the SBISS
Colossians 3 in the SBITS
Colossians 3 in the SBITS2
Colossians 3 in the SBITS3
Colossians 3 in the SBITS4
Colossians 3 in the SBIUS
Colossians 3 in the SBIVS
Colossians 3 in the SBT
Colossians 3 in the SBT1E
Colossians 3 in the SCHL
Colossians 3 in the SNT
Colossians 3 in the SUSU
Colossians 3 in the SUSU2
Colossians 3 in the SYNO
Colossians 3 in the TBIAOTANT
Colossians 3 in the TBT1E
Colossians 3 in the TBT1E2
Colossians 3 in the TFTIP
Colossians 3 in the TFTU
Colossians 3 in the TGNTATF3T
Colossians 3 in the THAI
Colossians 3 in the TNFD
Colossians 3 in the TNT
Colossians 3 in the TNTIK
Colossians 3 in the TNTIL
Colossians 3 in the TNTIN
Colossians 3 in the TNTIP
Colossians 3 in the TNTIZ
Colossians 3 in the TOMA
Colossians 3 in the TTENT
Colossians 3 in the UBG
Colossians 3 in the UGV
Colossians 3 in the UGV2
Colossians 3 in the UGV3
Colossians 3 in the VBL
Colossians 3 in the VDCC
Colossians 3 in the YALU
Colossians 3 in the YAPE
Colossians 3 in the YBVTP
Colossians 3 in the ZBP