Hebrews 9 (BOHCB)

1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya. 2 An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki. 3 Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki, 4 wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari. 5 A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba. 6 Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu. 7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani. 8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye. 9 Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba. 10 Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau. 11 Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba. 12 Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. 13 In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje, 14 balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai! 15 Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. 16 Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, 17 domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. 18 Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini. 19 Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen. 20 Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.” 21 Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima. 22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara. 23 Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau. 24 Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu. 25 Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba. 26 Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. 27 Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, 28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

In Other Versions

Hebrews 9 in the ANGEFD

Hebrews 9 in the ANTPNG2D

Hebrews 9 in the AS21

Hebrews 9 in the BAGH

Hebrews 9 in the BBPNG

Hebrews 9 in the BBT1E

Hebrews 9 in the BDS

Hebrews 9 in the BEV

Hebrews 9 in the BHAD

Hebrews 9 in the BIB

Hebrews 9 in the BLPT

Hebrews 9 in the BNT

Hebrews 9 in the BNTABOOT

Hebrews 9 in the BNTLV

Hebrews 9 in the BOATCB

Hebrews 9 in the BOATCB2

Hebrews 9 in the BOBCV

Hebrews 9 in the BOCNT

Hebrews 9 in the BOECS

Hebrews 9 in the BOGWICC

Hebrews 9 in the BOHCV

Hebrews 9 in the BOHLNT

Hebrews 9 in the BOHNTLTAL

Hebrews 9 in the BOICB

Hebrews 9 in the BOILNTAP

Hebrews 9 in the BOITCV

Hebrews 9 in the BOKCV

Hebrews 9 in the BOKCV2

Hebrews 9 in the BOKHWOG

Hebrews 9 in the BOKSSV

Hebrews 9 in the BOLCB

Hebrews 9 in the BOLCB2

Hebrews 9 in the BOMCV

Hebrews 9 in the BONAV

Hebrews 9 in the BONCB

Hebrews 9 in the BONLT

Hebrews 9 in the BONUT2

Hebrews 9 in the BOPLNT

Hebrews 9 in the BOSCB

Hebrews 9 in the BOSNC

Hebrews 9 in the BOTLNT

Hebrews 9 in the BOVCB

Hebrews 9 in the BOYCB

Hebrews 9 in the BPBB

Hebrews 9 in the BPH

Hebrews 9 in the BSB

Hebrews 9 in the CCB

Hebrews 9 in the CUV

Hebrews 9 in the CUVS

Hebrews 9 in the DBT

Hebrews 9 in the DGDNT

Hebrews 9 in the DHNT

Hebrews 9 in the DNT

Hebrews 9 in the ELBE

Hebrews 9 in the EMTV

Hebrews 9 in the ESV

Hebrews 9 in the FBV

Hebrews 9 in the FEB

Hebrews 9 in the GGMNT

Hebrews 9 in the GNT

Hebrews 9 in the HARY

Hebrews 9 in the HNT

Hebrews 9 in the IRVA

Hebrews 9 in the IRVB

Hebrews 9 in the IRVG

Hebrews 9 in the IRVH

Hebrews 9 in the IRVK

Hebrews 9 in the IRVM

Hebrews 9 in the IRVM2

Hebrews 9 in the IRVO

Hebrews 9 in the IRVP

Hebrews 9 in the IRVT

Hebrews 9 in the IRVT2

Hebrews 9 in the IRVU

Hebrews 9 in the ISVN

Hebrews 9 in the JSNT

Hebrews 9 in the KAPI

Hebrews 9 in the KBT1ETNIK

Hebrews 9 in the KBV

Hebrews 9 in the KJV

Hebrews 9 in the KNFD

Hebrews 9 in the LBA

Hebrews 9 in the LBLA

Hebrews 9 in the LNT

Hebrews 9 in the LSV

Hebrews 9 in the MAAL

Hebrews 9 in the MBV

Hebrews 9 in the MBV2

Hebrews 9 in the MHNT

Hebrews 9 in the MKNFD

Hebrews 9 in the MNG

Hebrews 9 in the MNT

Hebrews 9 in the MNT2

Hebrews 9 in the MRS1T

Hebrews 9 in the NAA

Hebrews 9 in the NASB

Hebrews 9 in the NBLA

Hebrews 9 in the NBS

Hebrews 9 in the NBVTP

Hebrews 9 in the NET2

Hebrews 9 in the NIV11

Hebrews 9 in the NNT

Hebrews 9 in the NNT2

Hebrews 9 in the NNT3

Hebrews 9 in the PDDPT

Hebrews 9 in the PFNT

Hebrews 9 in the RMNT

Hebrews 9 in the SBIAS

Hebrews 9 in the SBIBS

Hebrews 9 in the SBIBS2

Hebrews 9 in the SBICS

Hebrews 9 in the SBIDS

Hebrews 9 in the SBIGS

Hebrews 9 in the SBIHS

Hebrews 9 in the SBIIS

Hebrews 9 in the SBIIS2

Hebrews 9 in the SBIIS3

Hebrews 9 in the SBIKS

Hebrews 9 in the SBIKS2

Hebrews 9 in the SBIMS

Hebrews 9 in the SBIOS

Hebrews 9 in the SBIPS

Hebrews 9 in the SBISS

Hebrews 9 in the SBITS

Hebrews 9 in the SBITS2

Hebrews 9 in the SBITS3

Hebrews 9 in the SBITS4

Hebrews 9 in the SBIUS

Hebrews 9 in the SBIVS

Hebrews 9 in the SBT

Hebrews 9 in the SBT1E

Hebrews 9 in the SCHL

Hebrews 9 in the SNT

Hebrews 9 in the SUSU

Hebrews 9 in the SUSU2

Hebrews 9 in the SYNO

Hebrews 9 in the TBIAOTANT

Hebrews 9 in the TBT1E

Hebrews 9 in the TBT1E2

Hebrews 9 in the TFTIP

Hebrews 9 in the TFTU

Hebrews 9 in the TGNTATF3T

Hebrews 9 in the THAI

Hebrews 9 in the TNFD

Hebrews 9 in the TNT

Hebrews 9 in the TNTIK

Hebrews 9 in the TNTIL

Hebrews 9 in the TNTIN

Hebrews 9 in the TNTIP

Hebrews 9 in the TNTIZ

Hebrews 9 in the TOMA

Hebrews 9 in the TTENT

Hebrews 9 in the UBG

Hebrews 9 in the UGV

Hebrews 9 in the UGV2

Hebrews 9 in the UGV3

Hebrews 9 in the VBL

Hebrews 9 in the VDCC

Hebrews 9 in the YALU

Hebrews 9 in the YAPE

Hebrews 9 in the YBVTP

Hebrews 9 in the ZBP