John 10 (BOHCB)

1 “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2 Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. 3 Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. 4 Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. 5 Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.” 6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba. 7 Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba. 9 Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. 10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace. 11 “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. 12 Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su. 13 Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba. 14 “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni, 15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin. 16 Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma. 17 Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma. 18 Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.” 19 Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa. 20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?” 21 Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?” 22 Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa. 23 Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon, 24 sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.” 25 Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni. 26 Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. 27 Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. 30 Da ni da Uba ɗaya ne.” 31 Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, 32 amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?” 33 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.” 34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’? 35 Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’ 36 to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’ 37 In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.” 39 Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu. 40 Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna 41 mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42 A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.

In Other Versions

John 10 in the ANGEFD

John 10 in the ANTPNG2D

John 10 in the AS21

John 10 in the BAGH

John 10 in the BBPNG

John 10 in the BBT1E

John 10 in the BDS

John 10 in the BEV

John 10 in the BHAD

John 10 in the BIB

John 10 in the BLPT

John 10 in the BNT

John 10 in the BNTABOOT

John 10 in the BNTLV

John 10 in the BOATCB

John 10 in the BOATCB2

John 10 in the BOBCV

John 10 in the BOCNT

John 10 in the BOECS

John 10 in the BOGWICC

John 10 in the BOHCV

John 10 in the BOHLNT

John 10 in the BOHNTLTAL

John 10 in the BOICB

John 10 in the BOILNTAP

John 10 in the BOITCV

John 10 in the BOKCV

John 10 in the BOKCV2

John 10 in the BOKHWOG

John 10 in the BOKSSV

John 10 in the BOLCB

John 10 in the BOLCB2

John 10 in the BOMCV

John 10 in the BONAV

John 10 in the BONCB

John 10 in the BONLT

John 10 in the BONUT2

John 10 in the BOPLNT

John 10 in the BOSCB

John 10 in the BOSNC

John 10 in the BOTLNT

John 10 in the BOVCB

John 10 in the BOYCB

John 10 in the BPBB

John 10 in the BPH

John 10 in the BSB

John 10 in the CCB

John 10 in the CUV

John 10 in the CUVS

John 10 in the DBT

John 10 in the DGDNT

John 10 in the DHNT

John 10 in the DNT

John 10 in the ELBE

John 10 in the EMTV

John 10 in the ESV

John 10 in the FBV

John 10 in the FEB

John 10 in the GGMNT

John 10 in the GNT

John 10 in the HARY

John 10 in the HNT

John 10 in the IRVA

John 10 in the IRVB

John 10 in the IRVG

John 10 in the IRVH

John 10 in the IRVK

John 10 in the IRVM

John 10 in the IRVM2

John 10 in the IRVO

John 10 in the IRVP

John 10 in the IRVT

John 10 in the IRVT2

John 10 in the IRVU

John 10 in the ISVN

John 10 in the JSNT

John 10 in the KAPI

John 10 in the KBT1ETNIK

John 10 in the KBV

John 10 in the KJV

John 10 in the KNFD

John 10 in the LBA

John 10 in the LBLA

John 10 in the LNT

John 10 in the LSV

John 10 in the MAAL

John 10 in the MBV

John 10 in the MBV2

John 10 in the MHNT

John 10 in the MKNFD

John 10 in the MNG

John 10 in the MNT

John 10 in the MNT2

John 10 in the MRS1T

John 10 in the NAA

John 10 in the NASB

John 10 in the NBLA

John 10 in the NBS

John 10 in the NBVTP

John 10 in the NET2

John 10 in the NIV11

John 10 in the NNT

John 10 in the NNT2

John 10 in the NNT3

John 10 in the PDDPT

John 10 in the PFNT

John 10 in the RMNT

John 10 in the SBIAS

John 10 in the SBIBS

John 10 in the SBIBS2

John 10 in the SBICS

John 10 in the SBIDS

John 10 in the SBIGS

John 10 in the SBIHS

John 10 in the SBIIS

John 10 in the SBIIS2

John 10 in the SBIIS3

John 10 in the SBIKS

John 10 in the SBIKS2

John 10 in the SBIMS

John 10 in the SBIOS

John 10 in the SBIPS

John 10 in the SBISS

John 10 in the SBITS

John 10 in the SBITS2

John 10 in the SBITS3

John 10 in the SBITS4

John 10 in the SBIUS

John 10 in the SBIVS

John 10 in the SBT

John 10 in the SBT1E

John 10 in the SCHL

John 10 in the SNT

John 10 in the SUSU

John 10 in the SUSU2

John 10 in the SYNO

John 10 in the TBIAOTANT

John 10 in the TBT1E

John 10 in the TBT1E2

John 10 in the TFTIP

John 10 in the TFTU

John 10 in the TGNTATF3T

John 10 in the THAI

John 10 in the TNFD

John 10 in the TNT

John 10 in the TNTIK

John 10 in the TNTIL

John 10 in the TNTIN

John 10 in the TNTIP

John 10 in the TNTIZ

John 10 in the TOMA

John 10 in the TTENT

John 10 in the UBG

John 10 in the UGV

John 10 in the UGV2

John 10 in the UGV3

John 10 in the VBL

John 10 in the VDCC

John 10 in the YALU

John 10 in the YAPE

John 10 in the YBVTP

John 10 in the ZBP