John 13 (BOHCB)

1 Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa. 2 Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu. 3 Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah; 4 saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. 5 Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura. 6 Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?” 7 Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.” 8 Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.”Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9 Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!” 10 Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.” 11 Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.” 12 Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku? 13 Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake. 14 Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. 15 Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku. 16 Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi. 17 Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su. 18 “Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’ 19 “Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi. 20 Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ” 21 Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22 Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake. 23 Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi. 24 Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?” 25 Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?” 26 Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman. 27 Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi.Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.” 28 Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29 Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu. 30 Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi. 31 Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa. 32 In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take. 33 “’Ya’yana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu. Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba. 34 “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.” 36 Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?”Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.” 37 Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.” 38 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!

In Other Versions

John 13 in the ANGEFD

John 13 in the ANTPNG2D

John 13 in the AS21

John 13 in the BAGH

John 13 in the BBPNG

John 13 in the BBT1E

John 13 in the BDS

John 13 in the BEV

John 13 in the BHAD

John 13 in the BIB

John 13 in the BLPT

John 13 in the BNT

John 13 in the BNTABOOT

John 13 in the BNTLV

John 13 in the BOATCB

John 13 in the BOATCB2

John 13 in the BOBCV

John 13 in the BOCNT

John 13 in the BOECS

John 13 in the BOGWICC

John 13 in the BOHCV

John 13 in the BOHLNT

John 13 in the BOHNTLTAL

John 13 in the BOICB

John 13 in the BOILNTAP

John 13 in the BOITCV

John 13 in the BOKCV

John 13 in the BOKCV2

John 13 in the BOKHWOG

John 13 in the BOKSSV

John 13 in the BOLCB

John 13 in the BOLCB2

John 13 in the BOMCV

John 13 in the BONAV

John 13 in the BONCB

John 13 in the BONLT

John 13 in the BONUT2

John 13 in the BOPLNT

John 13 in the BOSCB

John 13 in the BOSNC

John 13 in the BOTLNT

John 13 in the BOVCB

John 13 in the BOYCB

John 13 in the BPBB

John 13 in the BPH

John 13 in the BSB

John 13 in the CCB

John 13 in the CUV

John 13 in the CUVS

John 13 in the DBT

John 13 in the DGDNT

John 13 in the DHNT

John 13 in the DNT

John 13 in the ELBE

John 13 in the EMTV

John 13 in the ESV

John 13 in the FBV

John 13 in the FEB

John 13 in the GGMNT

John 13 in the GNT

John 13 in the HARY

John 13 in the HNT

John 13 in the IRVA

John 13 in the IRVB

John 13 in the IRVG

John 13 in the IRVH

John 13 in the IRVK

John 13 in the IRVM

John 13 in the IRVM2

John 13 in the IRVO

John 13 in the IRVP

John 13 in the IRVT

John 13 in the IRVT2

John 13 in the IRVU

John 13 in the ISVN

John 13 in the JSNT

John 13 in the KAPI

John 13 in the KBT1ETNIK

John 13 in the KBV

John 13 in the KJV

John 13 in the KNFD

John 13 in the LBA

John 13 in the LBLA

John 13 in the LNT

John 13 in the LSV

John 13 in the MAAL

John 13 in the MBV

John 13 in the MBV2

John 13 in the MHNT

John 13 in the MKNFD

John 13 in the MNG

John 13 in the MNT

John 13 in the MNT2

John 13 in the MRS1T

John 13 in the NAA

John 13 in the NASB

John 13 in the NBLA

John 13 in the NBS

John 13 in the NBVTP

John 13 in the NET2

John 13 in the NIV11

John 13 in the NNT

John 13 in the NNT2

John 13 in the NNT3

John 13 in the PDDPT

John 13 in the PFNT

John 13 in the RMNT

John 13 in the SBIAS

John 13 in the SBIBS

John 13 in the SBIBS2

John 13 in the SBICS

John 13 in the SBIDS

John 13 in the SBIGS

John 13 in the SBIHS

John 13 in the SBIIS

John 13 in the SBIIS2

John 13 in the SBIIS3

John 13 in the SBIKS

John 13 in the SBIKS2

John 13 in the SBIMS

John 13 in the SBIOS

John 13 in the SBIPS

John 13 in the SBISS

John 13 in the SBITS

John 13 in the SBITS2

John 13 in the SBITS3

John 13 in the SBITS4

John 13 in the SBIUS

John 13 in the SBIVS

John 13 in the SBT

John 13 in the SBT1E

John 13 in the SCHL

John 13 in the SNT

John 13 in the SUSU

John 13 in the SUSU2

John 13 in the SYNO

John 13 in the TBIAOTANT

John 13 in the TBT1E

John 13 in the TBT1E2

John 13 in the TFTIP

John 13 in the TFTU

John 13 in the TGNTATF3T

John 13 in the THAI

John 13 in the TNFD

John 13 in the TNT

John 13 in the TNTIK

John 13 in the TNTIL

John 13 in the TNTIN

John 13 in the TNTIP

John 13 in the TNTIZ

John 13 in the TOMA

John 13 in the TTENT

John 13 in the UBG

John 13 in the UGV

John 13 in the UGV2

John 13 in the UGV3

John 13 in the VBL

John 13 in the VDCC

John 13 in the YALU

John 13 in the YAPE

John 13 in the YBVTP

John 13 in the ZBP