John 3 (BOHCB)
1 Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. 2 Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.” 3 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.” 4 Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!” 5 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. 6 Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. 7 Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ 8 Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.” 9 Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?” 10 Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba? 11 Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu. 12 Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama? 13 Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum. 14 Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15 don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.” 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah. 22 Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma. 23 To, Yohanna ma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, saboda akwai ruwa da yawa a can, mutane kuwa suka yi ta zuwa don a yi musu baftisma. 24 (Wannan kuwa kafin a sa Yohanna a kurkuku.) 25 Sai gardama ta tashi tsakanin waɗansu almajiran Yohanna da wani mutumin Yahuda a kan zancen al’adar tsarkakewa. 26 Sai suka zo wurin Yohanna suka ce masa, “Rabbi, wancan mutumin da yake tare da kai a ƙetaren Urdun, wannan da ka ba da shaida a kansa sosai nan, yana baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.” 27 Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama. 28 Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’ 29 Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu. 30 Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa. 31 “Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa. 32 Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa. 33 Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne. 34 Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka. 35 Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa. 36 Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”