Luke 10 (BOHCB)

1 Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. 2 Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. 3 Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai. 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya. 5 “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ 6 In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku. 7 Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida. 8 “Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku. 9 Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’ 10 Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce, 11 ‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’ 12 Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin. 13 “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. 14 A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku. 15 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki. 16 “Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.” 17 Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.” 18 Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. 19 Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.” 21 A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau. 22 “Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.” 23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani. 24 Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.” 25 Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?” 26 Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?” 27 Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ” 28 Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.” 29 Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?” 30 Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. 31 Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. 32 Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. 33 Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. 34 Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. 35 Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’ 36 “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?” 37 Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.”Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.” 38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!” 41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

In Other Versions

Luke 10 in the ANGEFD

Luke 10 in the ANTPNG2D

Luke 10 in the AS21

Luke 10 in the BAGH

Luke 10 in the BBPNG

Luke 10 in the BBT1E

Luke 10 in the BDS

Luke 10 in the BEV

Luke 10 in the BHAD

Luke 10 in the BIB

Luke 10 in the BLPT

Luke 10 in the BNT

Luke 10 in the BNTABOOT

Luke 10 in the BNTLV

Luke 10 in the BOATCB

Luke 10 in the BOATCB2

Luke 10 in the BOBCV

Luke 10 in the BOCNT

Luke 10 in the BOECS

Luke 10 in the BOGWICC

Luke 10 in the BOHCV

Luke 10 in the BOHLNT

Luke 10 in the BOHNTLTAL

Luke 10 in the BOICB

Luke 10 in the BOILNTAP

Luke 10 in the BOITCV

Luke 10 in the BOKCV

Luke 10 in the BOKCV2

Luke 10 in the BOKHWOG

Luke 10 in the BOKSSV

Luke 10 in the BOLCB

Luke 10 in the BOLCB2

Luke 10 in the BOMCV

Luke 10 in the BONAV

Luke 10 in the BONCB

Luke 10 in the BONLT

Luke 10 in the BONUT2

Luke 10 in the BOPLNT

Luke 10 in the BOSCB

Luke 10 in the BOSNC

Luke 10 in the BOTLNT

Luke 10 in the BOVCB

Luke 10 in the BOYCB

Luke 10 in the BPBB

Luke 10 in the BPH

Luke 10 in the BSB

Luke 10 in the CCB

Luke 10 in the CUV

Luke 10 in the CUVS

Luke 10 in the DBT

Luke 10 in the DGDNT

Luke 10 in the DHNT

Luke 10 in the DNT

Luke 10 in the ELBE

Luke 10 in the EMTV

Luke 10 in the ESV

Luke 10 in the FBV

Luke 10 in the FEB

Luke 10 in the GGMNT

Luke 10 in the GNT

Luke 10 in the HARY

Luke 10 in the HNT

Luke 10 in the IRVA

Luke 10 in the IRVB

Luke 10 in the IRVG

Luke 10 in the IRVH

Luke 10 in the IRVK

Luke 10 in the IRVM

Luke 10 in the IRVM2

Luke 10 in the IRVO

Luke 10 in the IRVP

Luke 10 in the IRVT

Luke 10 in the IRVT2

Luke 10 in the IRVU

Luke 10 in the ISVN

Luke 10 in the JSNT

Luke 10 in the KAPI

Luke 10 in the KBT1ETNIK

Luke 10 in the KBV

Luke 10 in the KJV

Luke 10 in the KNFD

Luke 10 in the LBA

Luke 10 in the LBLA

Luke 10 in the LNT

Luke 10 in the LSV

Luke 10 in the MAAL

Luke 10 in the MBV

Luke 10 in the MBV2

Luke 10 in the MHNT

Luke 10 in the MKNFD

Luke 10 in the MNG

Luke 10 in the MNT

Luke 10 in the MNT2

Luke 10 in the MRS1T

Luke 10 in the NAA

Luke 10 in the NASB

Luke 10 in the NBLA

Luke 10 in the NBS

Luke 10 in the NBVTP

Luke 10 in the NET2

Luke 10 in the NIV11

Luke 10 in the NNT

Luke 10 in the NNT2

Luke 10 in the NNT3

Luke 10 in the PDDPT

Luke 10 in the PFNT

Luke 10 in the RMNT

Luke 10 in the SBIAS

Luke 10 in the SBIBS

Luke 10 in the SBIBS2

Luke 10 in the SBICS

Luke 10 in the SBIDS

Luke 10 in the SBIGS

Luke 10 in the SBIHS

Luke 10 in the SBIIS

Luke 10 in the SBIIS2

Luke 10 in the SBIIS3

Luke 10 in the SBIKS

Luke 10 in the SBIKS2

Luke 10 in the SBIMS

Luke 10 in the SBIOS

Luke 10 in the SBIPS

Luke 10 in the SBISS

Luke 10 in the SBITS

Luke 10 in the SBITS2

Luke 10 in the SBITS3

Luke 10 in the SBITS4

Luke 10 in the SBIUS

Luke 10 in the SBIVS

Luke 10 in the SBT

Luke 10 in the SBT1E

Luke 10 in the SCHL

Luke 10 in the SNT

Luke 10 in the SUSU

Luke 10 in the SUSU2

Luke 10 in the SYNO

Luke 10 in the TBIAOTANT

Luke 10 in the TBT1E

Luke 10 in the TBT1E2

Luke 10 in the TFTIP

Luke 10 in the TFTU

Luke 10 in the TGNTATF3T

Luke 10 in the THAI

Luke 10 in the TNFD

Luke 10 in the TNT

Luke 10 in the TNTIK

Luke 10 in the TNTIL

Luke 10 in the TNTIN

Luke 10 in the TNTIP

Luke 10 in the TNTIZ

Luke 10 in the TOMA

Luke 10 in the TTENT

Luke 10 in the UBG

Luke 10 in the UGV

Luke 10 in the UGV2

Luke 10 in the UGV3

Luke 10 in the VBL

Luke 10 in the VDCC

Luke 10 in the YALU

Luke 10 in the YAPE

Luke 10 in the YBVTP

Luke 10 in the ZBP