Luke 12 (BOHCB)

1 Ana nan sa’ad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci. 2 Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 3 Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna. 4 “Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7 Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma. 8 “Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. 9 Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah. 10 Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11 “Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, 12 gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.” 13 Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.” 14 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” 15 Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.” 16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’ 18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’ 20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’ 21 “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.” 22 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. 23 Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa! 25 Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa? 26 Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran? 27 “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. 28 In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29 Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30 Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. 31 Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa. 32 “Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin. 33 Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. 34 Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take. 35 “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, 36 kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. 37 Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci. 38 Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. 39 Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. 40 Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.” 41 Bitrus ya yi tambaya ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?” 42 Ubangiji ya amsa ya ce, “To, wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci? 43 Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka. 44 Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa. 45 Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. 46 Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a sa’ar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya. 47 “Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka. 48 Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi. 49 “Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta ƙunu! 50 Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta! 51 Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne. 52 Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun. 53 Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.” 54 Ya ce wa taron, “Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi. 55 Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi. 56 Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba? 57 “Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba? 58 Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku. 59 Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”

In Other Versions

Luke 12 in the ANGEFD

Luke 12 in the ANTPNG2D

Luke 12 in the AS21

Luke 12 in the BAGH

Luke 12 in the BBPNG

Luke 12 in the BBT1E

Luke 12 in the BDS

Luke 12 in the BEV

Luke 12 in the BHAD

Luke 12 in the BIB

Luke 12 in the BLPT

Luke 12 in the BNT

Luke 12 in the BNTABOOT

Luke 12 in the BNTLV

Luke 12 in the BOATCB

Luke 12 in the BOATCB2

Luke 12 in the BOBCV

Luke 12 in the BOCNT

Luke 12 in the BOECS

Luke 12 in the BOGWICC

Luke 12 in the BOHCV

Luke 12 in the BOHLNT

Luke 12 in the BOHNTLTAL

Luke 12 in the BOICB

Luke 12 in the BOILNTAP

Luke 12 in the BOITCV

Luke 12 in the BOKCV

Luke 12 in the BOKCV2

Luke 12 in the BOKHWOG

Luke 12 in the BOKSSV

Luke 12 in the BOLCB

Luke 12 in the BOLCB2

Luke 12 in the BOMCV

Luke 12 in the BONAV

Luke 12 in the BONCB

Luke 12 in the BONLT

Luke 12 in the BONUT2

Luke 12 in the BOPLNT

Luke 12 in the BOSCB

Luke 12 in the BOSNC

Luke 12 in the BOTLNT

Luke 12 in the BOVCB

Luke 12 in the BOYCB

Luke 12 in the BPBB

Luke 12 in the BPH

Luke 12 in the BSB

Luke 12 in the CCB

Luke 12 in the CUV

Luke 12 in the CUVS

Luke 12 in the DBT

Luke 12 in the DGDNT

Luke 12 in the DHNT

Luke 12 in the DNT

Luke 12 in the ELBE

Luke 12 in the EMTV

Luke 12 in the ESV

Luke 12 in the FBV

Luke 12 in the FEB

Luke 12 in the GGMNT

Luke 12 in the GNT

Luke 12 in the HARY

Luke 12 in the HNT

Luke 12 in the IRVA

Luke 12 in the IRVB

Luke 12 in the IRVG

Luke 12 in the IRVH

Luke 12 in the IRVK

Luke 12 in the IRVM

Luke 12 in the IRVM2

Luke 12 in the IRVO

Luke 12 in the IRVP

Luke 12 in the IRVT

Luke 12 in the IRVT2

Luke 12 in the IRVU

Luke 12 in the ISVN

Luke 12 in the JSNT

Luke 12 in the KAPI

Luke 12 in the KBT1ETNIK

Luke 12 in the KBV

Luke 12 in the KJV

Luke 12 in the KNFD

Luke 12 in the LBA

Luke 12 in the LBLA

Luke 12 in the LNT

Luke 12 in the LSV

Luke 12 in the MAAL

Luke 12 in the MBV

Luke 12 in the MBV2

Luke 12 in the MHNT

Luke 12 in the MKNFD

Luke 12 in the MNG

Luke 12 in the MNT

Luke 12 in the MNT2

Luke 12 in the MRS1T

Luke 12 in the NAA

Luke 12 in the NASB

Luke 12 in the NBLA

Luke 12 in the NBS

Luke 12 in the NBVTP

Luke 12 in the NET2

Luke 12 in the NIV11

Luke 12 in the NNT

Luke 12 in the NNT2

Luke 12 in the NNT3

Luke 12 in the PDDPT

Luke 12 in the PFNT

Luke 12 in the RMNT

Luke 12 in the SBIAS

Luke 12 in the SBIBS

Luke 12 in the SBIBS2

Luke 12 in the SBICS

Luke 12 in the SBIDS

Luke 12 in the SBIGS

Luke 12 in the SBIHS

Luke 12 in the SBIIS

Luke 12 in the SBIIS2

Luke 12 in the SBIIS3

Luke 12 in the SBIKS

Luke 12 in the SBIKS2

Luke 12 in the SBIMS

Luke 12 in the SBIOS

Luke 12 in the SBIPS

Luke 12 in the SBISS

Luke 12 in the SBITS

Luke 12 in the SBITS2

Luke 12 in the SBITS3

Luke 12 in the SBITS4

Luke 12 in the SBIUS

Luke 12 in the SBIVS

Luke 12 in the SBT

Luke 12 in the SBT1E

Luke 12 in the SCHL

Luke 12 in the SNT

Luke 12 in the SUSU

Luke 12 in the SUSU2

Luke 12 in the SYNO

Luke 12 in the TBIAOTANT

Luke 12 in the TBT1E

Luke 12 in the TBT1E2

Luke 12 in the TFTIP

Luke 12 in the TFTU

Luke 12 in the TGNTATF3T

Luke 12 in the THAI

Luke 12 in the TNFD

Luke 12 in the TNT

Luke 12 in the TNTIK

Luke 12 in the TNTIL

Luke 12 in the TNTIN

Luke 12 in the TNTIP

Luke 12 in the TNTIZ

Luke 12 in the TOMA

Luke 12 in the TTENT

Luke 12 in the UBG

Luke 12 in the UGV

Luke 12 in the UGV2

Luke 12 in the UGV3

Luke 12 in the VBL

Luke 12 in the VDCC

Luke 12 in the YALU

Luke 12 in the YAPE

Luke 12 in the YBVTP

Luke 12 in the ZBP