Luke 3 (BOHCB)

1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.  2 A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada. 3 Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 4 Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya.“Muryar mai kira a hamada,‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,ku miƙe hanyoyi dominsa. 5 Za a cike kowane kwari,a farfashe kowane dutse da kowane tudu.Za a miƙe hanyoyin da suka karkace,a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul. 6 Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ” 7 Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8 Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim. 9 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.” 10 Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?” 11 Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.” 12 Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?” 13 Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.” 14 Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?”Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.” 15 Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa. 16 Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma. 17 Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” 18 Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara. 19 Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi, 20 Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku. 21 Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, 22 Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.” 23 To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli, 24 ɗan Mattat,ɗan Lawi, ɗan Melki,ɗan Yannai, ɗan Yusuf, 25 ɗan Mattatiyas, ɗan Amos,ɗan Nahum, ɗan Esli,ɗan Naggai, 26 ɗan Ma’at,ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin,ɗan Yosek, ɗan Yoda, 27 ɗan Yowanan, ɗan Resa,ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel,ɗan Neri, 28 ɗan Melki,ɗan Addi, ɗan Kosam,ɗan Elmadam, ɗan Er, 29 ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer,ɗan Yorim, ɗan Mattat,ɗan Lawi, 30 ɗan Simeyon,ɗan Yahuda, ɗan Yusuf,ɗan Yonam, ɗan Eliyakim, 31 ɗan Meleya, ɗan Menna,ɗan Mattata, ɗan Natan,ɗan Dawuda, 32 ɗan Yesse,ɗan Obed, ɗan Bowaz,ɗan Salmon, ɗan Nashon, 33 ɗan Amminadab, ɗan Ram,ɗan Hezron, ɗan Ferez,ɗan Yahuda, 34 ɗan Yaƙub,ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim,ɗan Tera, ɗan Nahor, 35 ɗan Serug, ɗan Reyu,ɗan Feleg, ɗan Eber,ɗan Sala, 36 ɗan Kainan,ɗan Arfakshad, ɗan Shem,ɗan Nuhu, ɗan Lamek, 37 ɗan Metusela, ɗan Enok,ɗan Yared, ɗan Mahalalel,ɗan Kainan, 38 ɗan Enosh,ɗan Shitu, ɗan Adamu,ɗan Allah.

In Other Versions

Luke 3 in the ANGEFD

Luke 3 in the ANTPNG2D

Luke 3 in the AS21

Luke 3 in the BAGH

Luke 3 in the BBPNG

Luke 3 in the BBT1E

Luke 3 in the BDS

Luke 3 in the BEV

Luke 3 in the BHAD

Luke 3 in the BIB

Luke 3 in the BLPT

Luke 3 in the BNT

Luke 3 in the BNTABOOT

Luke 3 in the BNTLV

Luke 3 in the BOATCB

Luke 3 in the BOATCB2

Luke 3 in the BOBCV

Luke 3 in the BOCNT

Luke 3 in the BOECS

Luke 3 in the BOGWICC

Luke 3 in the BOHCV

Luke 3 in the BOHLNT

Luke 3 in the BOHNTLTAL

Luke 3 in the BOICB

Luke 3 in the BOILNTAP

Luke 3 in the BOITCV

Luke 3 in the BOKCV

Luke 3 in the BOKCV2

Luke 3 in the BOKHWOG

Luke 3 in the BOKSSV

Luke 3 in the BOLCB

Luke 3 in the BOLCB2

Luke 3 in the BOMCV

Luke 3 in the BONAV

Luke 3 in the BONCB

Luke 3 in the BONLT

Luke 3 in the BONUT2

Luke 3 in the BOPLNT

Luke 3 in the BOSCB

Luke 3 in the BOSNC

Luke 3 in the BOTLNT

Luke 3 in the BOVCB

Luke 3 in the BOYCB

Luke 3 in the BPBB

Luke 3 in the BPH

Luke 3 in the BSB

Luke 3 in the CCB

Luke 3 in the CUV

Luke 3 in the CUVS

Luke 3 in the DBT

Luke 3 in the DGDNT

Luke 3 in the DHNT

Luke 3 in the DNT

Luke 3 in the ELBE

Luke 3 in the EMTV

Luke 3 in the ESV

Luke 3 in the FBV

Luke 3 in the FEB

Luke 3 in the GGMNT

Luke 3 in the GNT

Luke 3 in the HARY

Luke 3 in the HNT

Luke 3 in the IRVA

Luke 3 in the IRVB

Luke 3 in the IRVG

Luke 3 in the IRVH

Luke 3 in the IRVK

Luke 3 in the IRVM

Luke 3 in the IRVM2

Luke 3 in the IRVO

Luke 3 in the IRVP

Luke 3 in the IRVT

Luke 3 in the IRVT2

Luke 3 in the IRVU

Luke 3 in the ISVN

Luke 3 in the JSNT

Luke 3 in the KAPI

Luke 3 in the KBT1ETNIK

Luke 3 in the KBV

Luke 3 in the KJV

Luke 3 in the KNFD

Luke 3 in the LBA

Luke 3 in the LBLA

Luke 3 in the LNT

Luke 3 in the LSV

Luke 3 in the MAAL

Luke 3 in the MBV

Luke 3 in the MBV2

Luke 3 in the MHNT

Luke 3 in the MKNFD

Luke 3 in the MNG

Luke 3 in the MNT

Luke 3 in the MNT2

Luke 3 in the MRS1T

Luke 3 in the NAA

Luke 3 in the NASB

Luke 3 in the NBLA

Luke 3 in the NBS

Luke 3 in the NBVTP

Luke 3 in the NET2

Luke 3 in the NIV11

Luke 3 in the NNT

Luke 3 in the NNT2

Luke 3 in the NNT3

Luke 3 in the PDDPT

Luke 3 in the PFNT

Luke 3 in the RMNT

Luke 3 in the SBIAS

Luke 3 in the SBIBS

Luke 3 in the SBIBS2

Luke 3 in the SBICS

Luke 3 in the SBIDS

Luke 3 in the SBIGS

Luke 3 in the SBIHS

Luke 3 in the SBIIS

Luke 3 in the SBIIS2

Luke 3 in the SBIIS3

Luke 3 in the SBIKS

Luke 3 in the SBIKS2

Luke 3 in the SBIMS

Luke 3 in the SBIOS

Luke 3 in the SBIPS

Luke 3 in the SBISS

Luke 3 in the SBITS

Luke 3 in the SBITS2

Luke 3 in the SBITS3

Luke 3 in the SBITS4

Luke 3 in the SBIUS

Luke 3 in the SBIVS

Luke 3 in the SBT

Luke 3 in the SBT1E

Luke 3 in the SCHL

Luke 3 in the SNT

Luke 3 in the SUSU

Luke 3 in the SUSU2

Luke 3 in the SYNO

Luke 3 in the TBIAOTANT

Luke 3 in the TBT1E

Luke 3 in the TBT1E2

Luke 3 in the TFTIP

Luke 3 in the TFTU

Luke 3 in the TGNTATF3T

Luke 3 in the THAI

Luke 3 in the TNFD

Luke 3 in the TNT

Luke 3 in the TNTIK

Luke 3 in the TNTIL

Luke 3 in the TNTIN

Luke 3 in the TNTIP

Luke 3 in the TNTIZ

Luke 3 in the TOMA

Luke 3 in the TTENT

Luke 3 in the UBG

Luke 3 in the UGV

Luke 3 in the UGV2

Luke 3 in the UGV3

Luke 3 in the VBL

Luke 3 in the VDCC

Luke 3 in the YALU

Luke 3 in the YAPE

Luke 3 in the YBVTP

Luke 3 in the ZBP