Matthew 15 (BOHCB)

1 Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce, 2 “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!” 3 Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? 4 Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ 5 Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ 6 ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku. 7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce, 8 “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni. 9 A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ” 10 Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane. 11 Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.” 12 Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?” 13 Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi. 14 Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne. In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.” 15 Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.” 16 Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne? 17 Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba? 18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20 Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.” 21 Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon. 22 Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.” 23 Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.” 24 Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.” 25 Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!” 26 Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.” 27 Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.” 28 Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take. 29 Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna. 30 Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su. 31 Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila. 32 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.” 33 Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?” 34 Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?”Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.” 35 Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. 36 Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. 37 Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai. 38 Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara. 39 Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.

In Other Versions

Matthew 15 in the ANGEFD

Matthew 15 in the ANTPNG2D

Matthew 15 in the AS21

Matthew 15 in the BAGH

Matthew 15 in the BBPNG

Matthew 15 in the BBT1E

Matthew 15 in the BDS

Matthew 15 in the BEV

Matthew 15 in the BHAD

Matthew 15 in the BIB

Matthew 15 in the BLPT

Matthew 15 in the BNT

Matthew 15 in the BNTABOOT

Matthew 15 in the BNTLV

Matthew 15 in the BOATCB

Matthew 15 in the BOATCB2

Matthew 15 in the BOBCV

Matthew 15 in the BOCNT

Matthew 15 in the BOECS

Matthew 15 in the BOGWICC

Matthew 15 in the BOHCV

Matthew 15 in the BOHLNT

Matthew 15 in the BOHNTLTAL

Matthew 15 in the BOICB

Matthew 15 in the BOILNTAP

Matthew 15 in the BOITCV

Matthew 15 in the BOKCV

Matthew 15 in the BOKCV2

Matthew 15 in the BOKHWOG

Matthew 15 in the BOKSSV

Matthew 15 in the BOLCB

Matthew 15 in the BOLCB2

Matthew 15 in the BOMCV

Matthew 15 in the BONAV

Matthew 15 in the BONCB

Matthew 15 in the BONLT

Matthew 15 in the BONUT2

Matthew 15 in the BOPLNT

Matthew 15 in the BOSCB

Matthew 15 in the BOSNC

Matthew 15 in the BOTLNT

Matthew 15 in the BOVCB

Matthew 15 in the BOYCB

Matthew 15 in the BPBB

Matthew 15 in the BPH

Matthew 15 in the BSB

Matthew 15 in the CCB

Matthew 15 in the CUV

Matthew 15 in the CUVS

Matthew 15 in the DBT

Matthew 15 in the DGDNT

Matthew 15 in the DHNT

Matthew 15 in the DNT

Matthew 15 in the ELBE

Matthew 15 in the EMTV

Matthew 15 in the ESV

Matthew 15 in the FBV

Matthew 15 in the FEB

Matthew 15 in the GGMNT

Matthew 15 in the GNT

Matthew 15 in the HARY

Matthew 15 in the HNT

Matthew 15 in the IRVA

Matthew 15 in the IRVB

Matthew 15 in the IRVG

Matthew 15 in the IRVH

Matthew 15 in the IRVK

Matthew 15 in the IRVM

Matthew 15 in the IRVM2

Matthew 15 in the IRVO

Matthew 15 in the IRVP

Matthew 15 in the IRVT

Matthew 15 in the IRVT2

Matthew 15 in the IRVU

Matthew 15 in the ISVN

Matthew 15 in the JSNT

Matthew 15 in the KAPI

Matthew 15 in the KBT1ETNIK

Matthew 15 in the KBV

Matthew 15 in the KJV

Matthew 15 in the KNFD

Matthew 15 in the LBA

Matthew 15 in the LBLA

Matthew 15 in the LNT

Matthew 15 in the LSV

Matthew 15 in the MAAL

Matthew 15 in the MBV

Matthew 15 in the MBV2

Matthew 15 in the MHNT

Matthew 15 in the MKNFD

Matthew 15 in the MNG

Matthew 15 in the MNT

Matthew 15 in the MNT2

Matthew 15 in the MRS1T

Matthew 15 in the NAA

Matthew 15 in the NASB

Matthew 15 in the NBLA

Matthew 15 in the NBS

Matthew 15 in the NBVTP

Matthew 15 in the NET2

Matthew 15 in the NIV11

Matthew 15 in the NNT

Matthew 15 in the NNT2

Matthew 15 in the NNT3

Matthew 15 in the PDDPT

Matthew 15 in the PFNT

Matthew 15 in the RMNT

Matthew 15 in the SBIAS

Matthew 15 in the SBIBS

Matthew 15 in the SBIBS2

Matthew 15 in the SBICS

Matthew 15 in the SBIDS

Matthew 15 in the SBIGS

Matthew 15 in the SBIHS

Matthew 15 in the SBIIS

Matthew 15 in the SBIIS2

Matthew 15 in the SBIIS3

Matthew 15 in the SBIKS

Matthew 15 in the SBIKS2

Matthew 15 in the SBIMS

Matthew 15 in the SBIOS

Matthew 15 in the SBIPS

Matthew 15 in the SBISS

Matthew 15 in the SBITS

Matthew 15 in the SBITS2

Matthew 15 in the SBITS3

Matthew 15 in the SBITS4

Matthew 15 in the SBIUS

Matthew 15 in the SBIVS

Matthew 15 in the SBT

Matthew 15 in the SBT1E

Matthew 15 in the SCHL

Matthew 15 in the SNT

Matthew 15 in the SUSU

Matthew 15 in the SUSU2

Matthew 15 in the SYNO

Matthew 15 in the TBIAOTANT

Matthew 15 in the TBT1E

Matthew 15 in the TBT1E2

Matthew 15 in the TFTIP

Matthew 15 in the TFTU

Matthew 15 in the TGNTATF3T

Matthew 15 in the THAI

Matthew 15 in the TNFD

Matthew 15 in the TNT

Matthew 15 in the TNTIK

Matthew 15 in the TNTIL

Matthew 15 in the TNTIN

Matthew 15 in the TNTIP

Matthew 15 in the TNTIZ

Matthew 15 in the TOMA

Matthew 15 in the TTENT

Matthew 15 in the UBG

Matthew 15 in the UGV

Matthew 15 in the UGV2

Matthew 15 in the UGV3

Matthew 15 in the VBL

Matthew 15 in the VDCC

Matthew 15 in the YALU

Matthew 15 in the YAPE

Matthew 15 in the YBVTP

Matthew 15 in the ZBP