Matthew 2 (BOHCB)
1 Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima 2 suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.” 3 Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. 4 Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. 5 Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta. 6 “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda,ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba,gama daga cikinki mai mulki zai zo,wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’” 7 Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. 8 Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.” 9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. 12 Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam. 13 Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.” 14 Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar, 15 inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.” 16 Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan. 17 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, 18 “An ji murya a Rama,tana kuka da makoki mai tsanani,Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta,an kāsa ta’azantar da ita,don ba su.” 19 Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar, 20 ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.” 21 Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila. 22 Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili, 23 ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.”
In Other Versions
Matthew 2 in the ANGEFD
Matthew 2 in the ANTPNG2D
Matthew 2 in the AS21
Matthew 2 in the BAGH
Matthew 2 in the BBPNG
Matthew 2 in the BBT1E
Matthew 2 in the BDS
Matthew 2 in the BEV
Matthew 2 in the BHAD
Matthew 2 in the BIB
Matthew 2 in the BLPT
Matthew 2 in the BNT
Matthew 2 in the BNTABOOT
Matthew 2 in the BNTLV
Matthew 2 in the BOATCB
Matthew 2 in the BOATCB2
Matthew 2 in the BOBCV
Matthew 2 in the BOCNT
Matthew 2 in the BOECS
Matthew 2 in the BOGWICC
Matthew 2 in the BOHCV
Matthew 2 in the BOHLNT
Matthew 2 in the BOHNTLTAL
Matthew 2 in the BOICB
Matthew 2 in the BOILNTAP
Matthew 2 in the BOITCV
Matthew 2 in the BOKCV
Matthew 2 in the BOKCV2
Matthew 2 in the BOKHWOG
Matthew 2 in the BOKSSV
Matthew 2 in the BOLCB
Matthew 2 in the BOLCB2
Matthew 2 in the BOMCV
Matthew 2 in the BONAV
Matthew 2 in the BONCB
Matthew 2 in the BONLT
Matthew 2 in the BONUT2
Matthew 2 in the BOPLNT
Matthew 2 in the BOSCB
Matthew 2 in the BOSNC
Matthew 2 in the BOTLNT
Matthew 2 in the BOVCB
Matthew 2 in the BOYCB
Matthew 2 in the BPBB
Matthew 2 in the BPH
Matthew 2 in the BSB
Matthew 2 in the CCB
Matthew 2 in the CUV
Matthew 2 in the CUVS
Matthew 2 in the DBT
Matthew 2 in the DGDNT
Matthew 2 in the DHNT
Matthew 2 in the DNT
Matthew 2 in the ELBE
Matthew 2 in the EMTV
Matthew 2 in the ESV
Matthew 2 in the FBV
Matthew 2 in the FEB
Matthew 2 in the GGMNT
Matthew 2 in the GNT
Matthew 2 in the HARY
Matthew 2 in the HNT
Matthew 2 in the IRVA
Matthew 2 in the IRVB
Matthew 2 in the IRVG
Matthew 2 in the IRVH
Matthew 2 in the IRVK
Matthew 2 in the IRVM
Matthew 2 in the IRVM2
Matthew 2 in the IRVO
Matthew 2 in the IRVP
Matthew 2 in the IRVT
Matthew 2 in the IRVT2
Matthew 2 in the IRVU
Matthew 2 in the ISVN
Matthew 2 in the JSNT
Matthew 2 in the KAPI
Matthew 2 in the KBT1ETNIK
Matthew 2 in the KBV
Matthew 2 in the KJV
Matthew 2 in the KNFD
Matthew 2 in the LBA
Matthew 2 in the LBLA
Matthew 2 in the LNT
Matthew 2 in the LSV
Matthew 2 in the MAAL
Matthew 2 in the MBV
Matthew 2 in the MBV2
Matthew 2 in the MHNT
Matthew 2 in the MKNFD
Matthew 2 in the MNG
Matthew 2 in the MNT
Matthew 2 in the MNT2
Matthew 2 in the MRS1T
Matthew 2 in the NAA
Matthew 2 in the NASB
Matthew 2 in the NBLA
Matthew 2 in the NBS
Matthew 2 in the NBVTP
Matthew 2 in the NET2
Matthew 2 in the NIV11
Matthew 2 in the NNT
Matthew 2 in the NNT2
Matthew 2 in the NNT3
Matthew 2 in the PDDPT
Matthew 2 in the PFNT
Matthew 2 in the RMNT
Matthew 2 in the SBIAS
Matthew 2 in the SBIBS
Matthew 2 in the SBIBS2
Matthew 2 in the SBICS
Matthew 2 in the SBIDS
Matthew 2 in the SBIGS
Matthew 2 in the SBIHS
Matthew 2 in the SBIIS
Matthew 2 in the SBIIS2
Matthew 2 in the SBIIS3
Matthew 2 in the SBIKS
Matthew 2 in the SBIKS2
Matthew 2 in the SBIMS
Matthew 2 in the SBIOS
Matthew 2 in the SBIPS
Matthew 2 in the SBISS
Matthew 2 in the SBITS
Matthew 2 in the SBITS2
Matthew 2 in the SBITS3
Matthew 2 in the SBITS4
Matthew 2 in the SBIUS
Matthew 2 in the SBIVS
Matthew 2 in the SBT
Matthew 2 in the SBT1E
Matthew 2 in the SCHL
Matthew 2 in the SNT
Matthew 2 in the SUSU
Matthew 2 in the SUSU2
Matthew 2 in the SYNO
Matthew 2 in the TBIAOTANT
Matthew 2 in the TBT1E
Matthew 2 in the TBT1E2
Matthew 2 in the TFTIP
Matthew 2 in the TFTU
Matthew 2 in the TGNTATF3T
Matthew 2 in the THAI
Matthew 2 in the TNFD
Matthew 2 in the TNT
Matthew 2 in the TNTIK
Matthew 2 in the TNTIL
Matthew 2 in the TNTIN
Matthew 2 in the TNTIP
Matthew 2 in the TNTIZ
Matthew 2 in the TOMA
Matthew 2 in the TTENT
Matthew 2 in the UBG
Matthew 2 in the UGV
Matthew 2 in the UGV2
Matthew 2 in the UGV3
Matthew 2 in the VBL
Matthew 2 in the VDCC
Matthew 2 in the YALU
Matthew 2 in the YAPE
Matthew 2 in the YBVTP
Matthew 2 in the ZBP