Matthew 23 (BOHCB)

1 Sa’an nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa, 2 “Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa. 3 Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi. 4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka. 5 “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsu fantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa; 6 suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u; 7 suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’ 8 “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne. 9 Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama. 10 Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi. 11 Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku. 12 Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi. 13 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kun rufe ƙofar mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba. 15 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, sa’ad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu. 16 “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’ 17 Wawaye makafi! Wanne ya fi girma, zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18 Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’ 19 Makafi kawai! Wanne ya fi girma, bayarwar, ko kuwa bagaden da yake tsarkake bayarwar? 20 Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagade, ya rantse ne da bagaden tare da abin da yake bisansa. 21 Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa. 22 Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa. 23 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba. 24 Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi. 25 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai. 26 Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta. 27 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta. 28 Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta. 29 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado. 30 Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’ 31 Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne. 32 To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara! 33 “Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta? 34 Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari. 35 Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku. 36 Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani. 37 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi. 38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe. 39 Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”

In Other Versions

Matthew 23 in the ANGEFD

Matthew 23 in the ANTPNG2D

Matthew 23 in the AS21

Matthew 23 in the BAGH

Matthew 23 in the BBPNG

Matthew 23 in the BBT1E

Matthew 23 in the BDS

Matthew 23 in the BEV

Matthew 23 in the BHAD

Matthew 23 in the BIB

Matthew 23 in the BLPT

Matthew 23 in the BNT

Matthew 23 in the BNTABOOT

Matthew 23 in the BNTLV

Matthew 23 in the BOATCB

Matthew 23 in the BOATCB2

Matthew 23 in the BOBCV

Matthew 23 in the BOCNT

Matthew 23 in the BOECS

Matthew 23 in the BOGWICC

Matthew 23 in the BOHCV

Matthew 23 in the BOHLNT

Matthew 23 in the BOHNTLTAL

Matthew 23 in the BOICB

Matthew 23 in the BOILNTAP

Matthew 23 in the BOITCV

Matthew 23 in the BOKCV

Matthew 23 in the BOKCV2

Matthew 23 in the BOKHWOG

Matthew 23 in the BOKSSV

Matthew 23 in the BOLCB

Matthew 23 in the BOLCB2

Matthew 23 in the BOMCV

Matthew 23 in the BONAV

Matthew 23 in the BONCB

Matthew 23 in the BONLT

Matthew 23 in the BONUT2

Matthew 23 in the BOPLNT

Matthew 23 in the BOSCB

Matthew 23 in the BOSNC

Matthew 23 in the BOTLNT

Matthew 23 in the BOVCB

Matthew 23 in the BOYCB

Matthew 23 in the BPBB

Matthew 23 in the BPH

Matthew 23 in the BSB

Matthew 23 in the CCB

Matthew 23 in the CUV

Matthew 23 in the CUVS

Matthew 23 in the DBT

Matthew 23 in the DGDNT

Matthew 23 in the DHNT

Matthew 23 in the DNT

Matthew 23 in the ELBE

Matthew 23 in the EMTV

Matthew 23 in the ESV

Matthew 23 in the FBV

Matthew 23 in the FEB

Matthew 23 in the GGMNT

Matthew 23 in the GNT

Matthew 23 in the HARY

Matthew 23 in the HNT

Matthew 23 in the IRVA

Matthew 23 in the IRVB

Matthew 23 in the IRVG

Matthew 23 in the IRVH

Matthew 23 in the IRVK

Matthew 23 in the IRVM

Matthew 23 in the IRVM2

Matthew 23 in the IRVO

Matthew 23 in the IRVP

Matthew 23 in the IRVT

Matthew 23 in the IRVT2

Matthew 23 in the IRVU

Matthew 23 in the ISVN

Matthew 23 in the JSNT

Matthew 23 in the KAPI

Matthew 23 in the KBT1ETNIK

Matthew 23 in the KBV

Matthew 23 in the KJV

Matthew 23 in the KNFD

Matthew 23 in the LBA

Matthew 23 in the LBLA

Matthew 23 in the LNT

Matthew 23 in the LSV

Matthew 23 in the MAAL

Matthew 23 in the MBV

Matthew 23 in the MBV2

Matthew 23 in the MHNT

Matthew 23 in the MKNFD

Matthew 23 in the MNG

Matthew 23 in the MNT

Matthew 23 in the MNT2

Matthew 23 in the MRS1T

Matthew 23 in the NAA

Matthew 23 in the NASB

Matthew 23 in the NBLA

Matthew 23 in the NBS

Matthew 23 in the NBVTP

Matthew 23 in the NET2

Matthew 23 in the NIV11

Matthew 23 in the NNT

Matthew 23 in the NNT2

Matthew 23 in the NNT3

Matthew 23 in the PDDPT

Matthew 23 in the PFNT

Matthew 23 in the RMNT

Matthew 23 in the SBIAS

Matthew 23 in the SBIBS

Matthew 23 in the SBIBS2

Matthew 23 in the SBICS

Matthew 23 in the SBIDS

Matthew 23 in the SBIGS

Matthew 23 in the SBIHS

Matthew 23 in the SBIIS

Matthew 23 in the SBIIS2

Matthew 23 in the SBIIS3

Matthew 23 in the SBIKS

Matthew 23 in the SBIKS2

Matthew 23 in the SBIMS

Matthew 23 in the SBIOS

Matthew 23 in the SBIPS

Matthew 23 in the SBISS

Matthew 23 in the SBITS

Matthew 23 in the SBITS2

Matthew 23 in the SBITS3

Matthew 23 in the SBITS4

Matthew 23 in the SBIUS

Matthew 23 in the SBIVS

Matthew 23 in the SBT

Matthew 23 in the SBT1E

Matthew 23 in the SCHL

Matthew 23 in the SNT

Matthew 23 in the SUSU

Matthew 23 in the SUSU2

Matthew 23 in the SYNO

Matthew 23 in the TBIAOTANT

Matthew 23 in the TBT1E

Matthew 23 in the TBT1E2

Matthew 23 in the TFTIP

Matthew 23 in the TFTU

Matthew 23 in the TGNTATF3T

Matthew 23 in the THAI

Matthew 23 in the TNFD

Matthew 23 in the TNT

Matthew 23 in the TNTIK

Matthew 23 in the TNTIL

Matthew 23 in the TNTIN

Matthew 23 in the TNTIP

Matthew 23 in the TNTIZ

Matthew 23 in the TOMA

Matthew 23 in the TTENT

Matthew 23 in the UBG

Matthew 23 in the UGV

Matthew 23 in the UGV2

Matthew 23 in the UGV3

Matthew 23 in the VBL

Matthew 23 in the VDCC

Matthew 23 in the YALU

Matthew 23 in the YAPE

Matthew 23 in the YBVTP

Matthew 23 in the ZBP