Matthew 7 (BOHCB)
1 “Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. 2 Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku. 3 “Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido? 4 Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido? 5 Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka. 6 “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo. 7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8 Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa. 9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba! 12 Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa. 13 “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. 14 Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne. 15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16 Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17 Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 18 Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 19 Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20 Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.” 21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’ 24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.” 28 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, 29 domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.
In Other Versions
Matthew 7 in the ANGEFD
Matthew 7 in the ANTPNG2D
Matthew 7 in the AS21
Matthew 7 in the BAGH
Matthew 7 in the BBPNG
Matthew 7 in the BBT1E
Matthew 7 in the BDS
Matthew 7 in the BEV
Matthew 7 in the BHAD
Matthew 7 in the BIB
Matthew 7 in the BLPT
Matthew 7 in the BNT
Matthew 7 in the BNTABOOT
Matthew 7 in the BNTLV
Matthew 7 in the BOATCB
Matthew 7 in the BOATCB2
Matthew 7 in the BOBCV
Matthew 7 in the BOCNT
Matthew 7 in the BOECS
Matthew 7 in the BOGWICC
Matthew 7 in the BOHCV
Matthew 7 in the BOHLNT
Matthew 7 in the BOHNTLTAL
Matthew 7 in the BOICB
Matthew 7 in the BOILNTAP
Matthew 7 in the BOITCV
Matthew 7 in the BOKCV
Matthew 7 in the BOKCV2
Matthew 7 in the BOKHWOG
Matthew 7 in the BOKSSV
Matthew 7 in the BOLCB
Matthew 7 in the BOLCB2
Matthew 7 in the BOMCV
Matthew 7 in the BONAV
Matthew 7 in the BONCB
Matthew 7 in the BONLT
Matthew 7 in the BONUT2
Matthew 7 in the BOPLNT
Matthew 7 in the BOSCB
Matthew 7 in the BOSNC
Matthew 7 in the BOTLNT
Matthew 7 in the BOVCB
Matthew 7 in the BOYCB
Matthew 7 in the BPBB
Matthew 7 in the BPH
Matthew 7 in the BSB
Matthew 7 in the CCB
Matthew 7 in the CUV
Matthew 7 in the CUVS
Matthew 7 in the DBT
Matthew 7 in the DGDNT
Matthew 7 in the DHNT
Matthew 7 in the DNT
Matthew 7 in the ELBE
Matthew 7 in the EMTV
Matthew 7 in the ESV
Matthew 7 in the FBV
Matthew 7 in the FEB
Matthew 7 in the GGMNT
Matthew 7 in the GNT
Matthew 7 in the HARY
Matthew 7 in the HNT
Matthew 7 in the IRVA
Matthew 7 in the IRVB
Matthew 7 in the IRVG
Matthew 7 in the IRVH
Matthew 7 in the IRVK
Matthew 7 in the IRVM
Matthew 7 in the IRVM2
Matthew 7 in the IRVO
Matthew 7 in the IRVP
Matthew 7 in the IRVT
Matthew 7 in the IRVT2
Matthew 7 in the IRVU
Matthew 7 in the ISVN
Matthew 7 in the JSNT
Matthew 7 in the KAPI
Matthew 7 in the KBT1ETNIK
Matthew 7 in the KBV
Matthew 7 in the KJV
Matthew 7 in the KNFD
Matthew 7 in the LBA
Matthew 7 in the LBLA
Matthew 7 in the LNT
Matthew 7 in the LSV
Matthew 7 in the MAAL
Matthew 7 in the MBV
Matthew 7 in the MBV2
Matthew 7 in the MHNT
Matthew 7 in the MKNFD
Matthew 7 in the MNG
Matthew 7 in the MNT
Matthew 7 in the MNT2
Matthew 7 in the MRS1T
Matthew 7 in the NAA
Matthew 7 in the NASB
Matthew 7 in the NBLA
Matthew 7 in the NBS
Matthew 7 in the NBVTP
Matthew 7 in the NET2
Matthew 7 in the NIV11
Matthew 7 in the NNT
Matthew 7 in the NNT2
Matthew 7 in the NNT3
Matthew 7 in the PDDPT
Matthew 7 in the PFNT
Matthew 7 in the RMNT
Matthew 7 in the SBIAS
Matthew 7 in the SBIBS
Matthew 7 in the SBIBS2
Matthew 7 in the SBICS
Matthew 7 in the SBIDS
Matthew 7 in the SBIGS
Matthew 7 in the SBIHS
Matthew 7 in the SBIIS
Matthew 7 in the SBIIS2
Matthew 7 in the SBIIS3
Matthew 7 in the SBIKS
Matthew 7 in the SBIKS2
Matthew 7 in the SBIMS
Matthew 7 in the SBIOS
Matthew 7 in the SBIPS
Matthew 7 in the SBISS
Matthew 7 in the SBITS
Matthew 7 in the SBITS2
Matthew 7 in the SBITS3
Matthew 7 in the SBITS4
Matthew 7 in the SBIUS
Matthew 7 in the SBIVS
Matthew 7 in the SBT
Matthew 7 in the SBT1E
Matthew 7 in the SCHL
Matthew 7 in the SNT
Matthew 7 in the SUSU
Matthew 7 in the SUSU2
Matthew 7 in the SYNO
Matthew 7 in the TBIAOTANT
Matthew 7 in the TBT1E
Matthew 7 in the TBT1E2
Matthew 7 in the TFTIP
Matthew 7 in the TFTU
Matthew 7 in the TGNTATF3T
Matthew 7 in the THAI
Matthew 7 in the TNFD
Matthew 7 in the TNT
Matthew 7 in the TNTIK
Matthew 7 in the TNTIL
Matthew 7 in the TNTIN
Matthew 7 in the TNTIP
Matthew 7 in the TNTIZ
Matthew 7 in the TOMA
Matthew 7 in the TTENT
Matthew 7 in the UBG
Matthew 7 in the UGV
Matthew 7 in the UGV2
Matthew 7 in the UGV3
Matthew 7 in the VBL
Matthew 7 in the VDCC
Matthew 7 in the YALU
Matthew 7 in the YAPE
Matthew 7 in the YBVTP
Matthew 7 in the ZBP