Mark 13 (BOHCB)

1 Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!” 2 Yesu ya amsa ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.” 3 Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, 4 “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?” 5 Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku. 6 Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 7 Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. 8 Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda. 9 “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10 Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. 11 Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne. 12 “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto. 14 “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’ tsaye inda bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu. 15 Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu. 16 Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa. 17 Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! 18 Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi. 19 Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba. 20 “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin. 21 A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. 22 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 23 Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri. 24 “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; 25 taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’ 26 “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma. 27 Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama. 28 “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. 29 Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 30 Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru. 31 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba. 32 “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. 33 Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. 34 Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro. 35 “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36 In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci. 37 Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”

In Other Versions

Mark 13 in the ANGEFD

Mark 13 in the ANTPNG2D

Mark 13 in the AS21

Mark 13 in the BAGH

Mark 13 in the BBPNG

Mark 13 in the BBT1E

Mark 13 in the BDS

Mark 13 in the BEV

Mark 13 in the BHAD

Mark 13 in the BIB

Mark 13 in the BLPT

Mark 13 in the BNT

Mark 13 in the BNTABOOT

Mark 13 in the BNTLV

Mark 13 in the BOATCB

Mark 13 in the BOATCB2

Mark 13 in the BOBCV

Mark 13 in the BOCNT

Mark 13 in the BOECS

Mark 13 in the BOGWICC

Mark 13 in the BOHCV

Mark 13 in the BOHLNT

Mark 13 in the BOHNTLTAL

Mark 13 in the BOICB

Mark 13 in the BOILNTAP

Mark 13 in the BOITCV

Mark 13 in the BOKCV

Mark 13 in the BOKCV2

Mark 13 in the BOKHWOG

Mark 13 in the BOKSSV

Mark 13 in the BOLCB

Mark 13 in the BOLCB2

Mark 13 in the BOMCV

Mark 13 in the BONAV

Mark 13 in the BONCB

Mark 13 in the BONLT

Mark 13 in the BONUT2

Mark 13 in the BOPLNT

Mark 13 in the BOSCB

Mark 13 in the BOSNC

Mark 13 in the BOTLNT

Mark 13 in the BOVCB

Mark 13 in the BOYCB

Mark 13 in the BPBB

Mark 13 in the BPH

Mark 13 in the BSB

Mark 13 in the CCB

Mark 13 in the CUV

Mark 13 in the CUVS

Mark 13 in the DBT

Mark 13 in the DGDNT

Mark 13 in the DHNT

Mark 13 in the DNT

Mark 13 in the ELBE

Mark 13 in the EMTV

Mark 13 in the ESV

Mark 13 in the FBV

Mark 13 in the FEB

Mark 13 in the GGMNT

Mark 13 in the GNT

Mark 13 in the HARY

Mark 13 in the HNT

Mark 13 in the IRVA

Mark 13 in the IRVB

Mark 13 in the IRVG

Mark 13 in the IRVH

Mark 13 in the IRVK

Mark 13 in the IRVM

Mark 13 in the IRVM2

Mark 13 in the IRVO

Mark 13 in the IRVP

Mark 13 in the IRVT

Mark 13 in the IRVT2

Mark 13 in the IRVU

Mark 13 in the ISVN

Mark 13 in the JSNT

Mark 13 in the KAPI

Mark 13 in the KBT1ETNIK

Mark 13 in the KBV

Mark 13 in the KJV

Mark 13 in the KNFD

Mark 13 in the LBA

Mark 13 in the LBLA

Mark 13 in the LNT

Mark 13 in the LSV

Mark 13 in the MAAL

Mark 13 in the MBV

Mark 13 in the MBV2

Mark 13 in the MHNT

Mark 13 in the MKNFD

Mark 13 in the MNG

Mark 13 in the MNT

Mark 13 in the MNT2

Mark 13 in the MRS1T

Mark 13 in the NAA

Mark 13 in the NASB

Mark 13 in the NBLA

Mark 13 in the NBS

Mark 13 in the NBVTP

Mark 13 in the NET2

Mark 13 in the NIV11

Mark 13 in the NNT

Mark 13 in the NNT2

Mark 13 in the NNT3

Mark 13 in the PDDPT

Mark 13 in the PFNT

Mark 13 in the RMNT

Mark 13 in the SBIAS

Mark 13 in the SBIBS

Mark 13 in the SBIBS2

Mark 13 in the SBICS

Mark 13 in the SBIDS

Mark 13 in the SBIGS

Mark 13 in the SBIHS

Mark 13 in the SBIIS

Mark 13 in the SBIIS2

Mark 13 in the SBIIS3

Mark 13 in the SBIKS

Mark 13 in the SBIKS2

Mark 13 in the SBIMS

Mark 13 in the SBIOS

Mark 13 in the SBIPS

Mark 13 in the SBISS

Mark 13 in the SBITS

Mark 13 in the SBITS2

Mark 13 in the SBITS3

Mark 13 in the SBITS4

Mark 13 in the SBIUS

Mark 13 in the SBIVS

Mark 13 in the SBT

Mark 13 in the SBT1E

Mark 13 in the SCHL

Mark 13 in the SNT

Mark 13 in the SUSU

Mark 13 in the SUSU2

Mark 13 in the SYNO

Mark 13 in the TBIAOTANT

Mark 13 in the TBT1E

Mark 13 in the TBT1E2

Mark 13 in the TFTIP

Mark 13 in the TFTU

Mark 13 in the TGNTATF3T

Mark 13 in the THAI

Mark 13 in the TNFD

Mark 13 in the TNT

Mark 13 in the TNTIK

Mark 13 in the TNTIL

Mark 13 in the TNTIN

Mark 13 in the TNTIP

Mark 13 in the TNTIZ

Mark 13 in the TOMA

Mark 13 in the TTENT

Mark 13 in the UBG

Mark 13 in the UGV

Mark 13 in the UGV2

Mark 13 in the UGV3

Mark 13 in the VBL

Mark 13 in the VDCC

Mark 13 in the YALU

Mark 13 in the YAPE

Mark 13 in the YBVTP

Mark 13 in the ZBP