Philippians 1 (BOHCB)
1 Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, Zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima. 2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare ku. 3 Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4 A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu. 7 Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni. 8 Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu. 9 Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10 don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi, 11 cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa. 12 To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara. 13 Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi. 14 Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro. 15 Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi. 16 Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara. 17 Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi. 18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki.I, zan kuwa ci gaba da farin ciki, 19 gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata. 20 Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa. 21 Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. 22 In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! 23 Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba; 24 amma ya fi muku muhimmanci in rayu cikin jiki. 25 Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki, 26 domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina. 27 Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara 28 ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. 29 Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa, 30 da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha.
In Other Versions
Philippians 1 in the ANGEFD
Philippians 1 in the ANTPNG2D
Philippians 1 in the AS21
Philippians 1 in the BAGH
Philippians 1 in the BBPNG
Philippians 1 in the BBT1E
Philippians 1 in the BDS
Philippians 1 in the BEV
Philippians 1 in the BHAD
Philippians 1 in the BIB
Philippians 1 in the BLPT
Philippians 1 in the BNT
Philippians 1 in the BNTABOOT
Philippians 1 in the BNTLV
Philippians 1 in the BOATCB
Philippians 1 in the BOATCB2
Philippians 1 in the BOBCV
Philippians 1 in the BOCNT
Philippians 1 in the BOECS
Philippians 1 in the BOGWICC
Philippians 1 in the BOHCV
Philippians 1 in the BOHLNT
Philippians 1 in the BOHNTLTAL
Philippians 1 in the BOICB
Philippians 1 in the BOILNTAP
Philippians 1 in the BOITCV
Philippians 1 in the BOKCV
Philippians 1 in the BOKCV2
Philippians 1 in the BOKHWOG
Philippians 1 in the BOKSSV
Philippians 1 in the BOLCB
Philippians 1 in the BOLCB2
Philippians 1 in the BOMCV
Philippians 1 in the BONAV
Philippians 1 in the BONCB
Philippians 1 in the BONLT
Philippians 1 in the BONUT2
Philippians 1 in the BOPLNT
Philippians 1 in the BOSCB
Philippians 1 in the BOSNC
Philippians 1 in the BOTLNT
Philippians 1 in the BOVCB
Philippians 1 in the BOYCB
Philippians 1 in the BPBB
Philippians 1 in the BPH
Philippians 1 in the BSB
Philippians 1 in the CCB
Philippians 1 in the CUV
Philippians 1 in the CUVS
Philippians 1 in the DBT
Philippians 1 in the DGDNT
Philippians 1 in the DHNT
Philippians 1 in the DNT
Philippians 1 in the ELBE
Philippians 1 in the EMTV
Philippians 1 in the ESV
Philippians 1 in the FBV
Philippians 1 in the FEB
Philippians 1 in the GGMNT
Philippians 1 in the GNT
Philippians 1 in the HARY
Philippians 1 in the HNT
Philippians 1 in the IRVA
Philippians 1 in the IRVB
Philippians 1 in the IRVG
Philippians 1 in the IRVH
Philippians 1 in the IRVK
Philippians 1 in the IRVM
Philippians 1 in the IRVM2
Philippians 1 in the IRVO
Philippians 1 in the IRVP
Philippians 1 in the IRVT
Philippians 1 in the IRVT2
Philippians 1 in the IRVU
Philippians 1 in the ISVN
Philippians 1 in the JSNT
Philippians 1 in the KAPI
Philippians 1 in the KBT1ETNIK
Philippians 1 in the KBV
Philippians 1 in the KJV
Philippians 1 in the KNFD
Philippians 1 in the LBA
Philippians 1 in the LBLA
Philippians 1 in the LNT
Philippians 1 in the LSV
Philippians 1 in the MAAL
Philippians 1 in the MBV
Philippians 1 in the MBV2
Philippians 1 in the MHNT
Philippians 1 in the MKNFD
Philippians 1 in the MNG
Philippians 1 in the MNT
Philippians 1 in the MNT2
Philippians 1 in the MRS1T
Philippians 1 in the NAA
Philippians 1 in the NASB
Philippians 1 in the NBLA
Philippians 1 in the NBS
Philippians 1 in the NBVTP
Philippians 1 in the NET2
Philippians 1 in the NIV11
Philippians 1 in the NNT
Philippians 1 in the NNT2
Philippians 1 in the NNT3
Philippians 1 in the PDDPT
Philippians 1 in the PFNT
Philippians 1 in the RMNT
Philippians 1 in the SBIAS
Philippians 1 in the SBIBS
Philippians 1 in the SBIBS2
Philippians 1 in the SBICS
Philippians 1 in the SBIDS
Philippians 1 in the SBIGS
Philippians 1 in the SBIHS
Philippians 1 in the SBIIS
Philippians 1 in the SBIIS2
Philippians 1 in the SBIIS3
Philippians 1 in the SBIKS
Philippians 1 in the SBIKS2
Philippians 1 in the SBIMS
Philippians 1 in the SBIOS
Philippians 1 in the SBIPS
Philippians 1 in the SBISS
Philippians 1 in the SBITS
Philippians 1 in the SBITS2
Philippians 1 in the SBITS3
Philippians 1 in the SBITS4
Philippians 1 in the SBIUS
Philippians 1 in the SBIVS
Philippians 1 in the SBT
Philippians 1 in the SBT1E
Philippians 1 in the SCHL
Philippians 1 in the SNT
Philippians 1 in the SUSU
Philippians 1 in the SUSU2
Philippians 1 in the SYNO
Philippians 1 in the TBIAOTANT
Philippians 1 in the TBT1E
Philippians 1 in the TBT1E2
Philippians 1 in the TFTIP
Philippians 1 in the TFTU
Philippians 1 in the TGNTATF3T
Philippians 1 in the THAI
Philippians 1 in the TNFD
Philippians 1 in the TNT
Philippians 1 in the TNTIK
Philippians 1 in the TNTIL
Philippians 1 in the TNTIN
Philippians 1 in the TNTIP
Philippians 1 in the TNTIZ
Philippians 1 in the TOMA
Philippians 1 in the TTENT
Philippians 1 in the UBG
Philippians 1 in the UGV
Philippians 1 in the UGV2
Philippians 1 in the UGV3
Philippians 1 in the VBL
Philippians 1 in the VDCC
Philippians 1 in the YALU
Philippians 1 in the YAPE
Philippians 1 in the YBVTP
Philippians 1 in the ZBP