1 Peter 2 (BOHCB)

1 Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2 Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3 yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji. 4 Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi 5 ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. 6 Gama a cikin Nassi an ce,“Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona,zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,wanda kuma ya dogara gare shiba zai taɓa kunyata ba.” 7 A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba,“Dutsen da magina suka ƙiya zama dutsen kusurwar gini, 8 kuma,“Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓekuma fā ne da yake sa su fāɗi.”Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. 10 Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai. 11 Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. 12 Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu. 13 Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, 14 ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. 15 Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. 16 Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. 17 Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki. 18 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. 19 Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. 20 Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. 21 Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi. 22 “Bai taɓa yin laifi ba sam,ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.” 23 Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. 24 Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. 25 Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.

In Other Versions

1 Peter 2 in the ANGEFD

1 Peter 2 in the ANTPNG2D

1 Peter 2 in the AS21

1 Peter 2 in the BAGH

1 Peter 2 in the BBPNG

1 Peter 2 in the BBT1E

1 Peter 2 in the BDS

1 Peter 2 in the BEV

1 Peter 2 in the BHAD

1 Peter 2 in the BIB

1 Peter 2 in the BLPT

1 Peter 2 in the BNT

1 Peter 2 in the BNTABOOT

1 Peter 2 in the BNTLV

1 Peter 2 in the BOATCB

1 Peter 2 in the BOATCB2

1 Peter 2 in the BOBCV

1 Peter 2 in the BOCNT

1 Peter 2 in the BOECS

1 Peter 2 in the BOGWICC

1 Peter 2 in the BOHCV

1 Peter 2 in the BOHLNT

1 Peter 2 in the BOHNTLTAL

1 Peter 2 in the BOICB

1 Peter 2 in the BOILNTAP

1 Peter 2 in the BOITCV

1 Peter 2 in the BOKCV

1 Peter 2 in the BOKCV2

1 Peter 2 in the BOKHWOG

1 Peter 2 in the BOKSSV

1 Peter 2 in the BOLCB

1 Peter 2 in the BOLCB2

1 Peter 2 in the BOMCV

1 Peter 2 in the BONAV

1 Peter 2 in the BONCB

1 Peter 2 in the BONLT

1 Peter 2 in the BONUT2

1 Peter 2 in the BOPLNT

1 Peter 2 in the BOSCB

1 Peter 2 in the BOSNC

1 Peter 2 in the BOTLNT

1 Peter 2 in the BOVCB

1 Peter 2 in the BOYCB

1 Peter 2 in the BPBB

1 Peter 2 in the BPH

1 Peter 2 in the BSB

1 Peter 2 in the CCB

1 Peter 2 in the CUV

1 Peter 2 in the CUVS

1 Peter 2 in the DBT

1 Peter 2 in the DGDNT

1 Peter 2 in the DHNT

1 Peter 2 in the DNT

1 Peter 2 in the ELBE

1 Peter 2 in the EMTV

1 Peter 2 in the ESV

1 Peter 2 in the FBV

1 Peter 2 in the FEB

1 Peter 2 in the GGMNT

1 Peter 2 in the GNT

1 Peter 2 in the HARY

1 Peter 2 in the HNT

1 Peter 2 in the IRVA

1 Peter 2 in the IRVB

1 Peter 2 in the IRVG

1 Peter 2 in the IRVH

1 Peter 2 in the IRVK

1 Peter 2 in the IRVM

1 Peter 2 in the IRVM2

1 Peter 2 in the IRVO

1 Peter 2 in the IRVP

1 Peter 2 in the IRVT

1 Peter 2 in the IRVT2

1 Peter 2 in the IRVU

1 Peter 2 in the ISVN

1 Peter 2 in the JSNT

1 Peter 2 in the KAPI

1 Peter 2 in the KBT1ETNIK

1 Peter 2 in the KBV

1 Peter 2 in the KJV

1 Peter 2 in the KNFD

1 Peter 2 in the LBA

1 Peter 2 in the LBLA

1 Peter 2 in the LNT

1 Peter 2 in the LSV

1 Peter 2 in the MAAL

1 Peter 2 in the MBV

1 Peter 2 in the MBV2

1 Peter 2 in the MHNT

1 Peter 2 in the MKNFD

1 Peter 2 in the MNG

1 Peter 2 in the MNT

1 Peter 2 in the MNT2

1 Peter 2 in the MRS1T

1 Peter 2 in the NAA

1 Peter 2 in the NASB

1 Peter 2 in the NBLA

1 Peter 2 in the NBS

1 Peter 2 in the NBVTP

1 Peter 2 in the NET2

1 Peter 2 in the NIV11

1 Peter 2 in the NNT

1 Peter 2 in the NNT2

1 Peter 2 in the NNT3

1 Peter 2 in the PDDPT

1 Peter 2 in the PFNT

1 Peter 2 in the RMNT

1 Peter 2 in the SBIAS

1 Peter 2 in the SBIBS

1 Peter 2 in the SBIBS2

1 Peter 2 in the SBICS

1 Peter 2 in the SBIDS

1 Peter 2 in the SBIGS

1 Peter 2 in the SBIHS

1 Peter 2 in the SBIIS

1 Peter 2 in the SBIIS2

1 Peter 2 in the SBIIS3

1 Peter 2 in the SBIKS

1 Peter 2 in the SBIKS2

1 Peter 2 in the SBIMS

1 Peter 2 in the SBIOS

1 Peter 2 in the SBIPS

1 Peter 2 in the SBISS

1 Peter 2 in the SBITS

1 Peter 2 in the SBITS2

1 Peter 2 in the SBITS3

1 Peter 2 in the SBITS4

1 Peter 2 in the SBIUS

1 Peter 2 in the SBIVS

1 Peter 2 in the SBT

1 Peter 2 in the SBT1E

1 Peter 2 in the SCHL

1 Peter 2 in the SNT

1 Peter 2 in the SUSU

1 Peter 2 in the SUSU2

1 Peter 2 in the SYNO

1 Peter 2 in the TBIAOTANT

1 Peter 2 in the TBT1E

1 Peter 2 in the TBT1E2

1 Peter 2 in the TFTIP

1 Peter 2 in the TFTU

1 Peter 2 in the TGNTATF3T

1 Peter 2 in the THAI

1 Peter 2 in the TNFD

1 Peter 2 in the TNT

1 Peter 2 in the TNTIK

1 Peter 2 in the TNTIL

1 Peter 2 in the TNTIN

1 Peter 2 in the TNTIP

1 Peter 2 in the TNTIZ

1 Peter 2 in the TOMA

1 Peter 2 in the TTENT

1 Peter 2 in the UBG

1 Peter 2 in the UGV

1 Peter 2 in the UGV2

1 Peter 2 in the UGV3

1 Peter 2 in the VBL

1 Peter 2 in the VDCC

1 Peter 2 in the YALU

1 Peter 2 in the YAPE

1 Peter 2 in the YBVTP

1 Peter 2 in the ZBP