1 Timothy 5 (BOHCB)
1 Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, 2 tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki. 3 Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. 4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. 5 Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. 6 Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai. 7 Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. 8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni. 9 Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta, 10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau. 11 Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. 12 Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. 13 Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. 14 Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. 15 Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan. 16 In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi. 17 Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. 18 Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.” 19 Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. 20 Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro. 21 Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci. 22 Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki. 23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka. 24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya. 25 Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.
In Other Versions
1 Timothy 5 in the ANGEFD
1 Timothy 5 in the ANTPNG2D
1 Timothy 5 in the AS21
1 Timothy 5 in the BAGH
1 Timothy 5 in the BBPNG
1 Timothy 5 in the BBT1E
1 Timothy 5 in the BDS
1 Timothy 5 in the BEV
1 Timothy 5 in the BHAD
1 Timothy 5 in the BIB
1 Timothy 5 in the BLPT
1 Timothy 5 in the BNT
1 Timothy 5 in the BNTABOOT
1 Timothy 5 in the BNTLV
1 Timothy 5 in the BOATCB
1 Timothy 5 in the BOATCB2
1 Timothy 5 in the BOBCV
1 Timothy 5 in the BOCNT
1 Timothy 5 in the BOECS
1 Timothy 5 in the BOGWICC
1 Timothy 5 in the BOHCV
1 Timothy 5 in the BOHLNT
1 Timothy 5 in the BOHNTLTAL
1 Timothy 5 in the BOICB
1 Timothy 5 in the BOILNTAP
1 Timothy 5 in the BOITCV
1 Timothy 5 in the BOKCV
1 Timothy 5 in the BOKCV2
1 Timothy 5 in the BOKHWOG
1 Timothy 5 in the BOKSSV
1 Timothy 5 in the BOLCB
1 Timothy 5 in the BOLCB2
1 Timothy 5 in the BOMCV
1 Timothy 5 in the BONAV
1 Timothy 5 in the BONCB
1 Timothy 5 in the BONLT
1 Timothy 5 in the BONUT2
1 Timothy 5 in the BOPLNT
1 Timothy 5 in the BOSCB
1 Timothy 5 in the BOSNC
1 Timothy 5 in the BOTLNT
1 Timothy 5 in the BOVCB
1 Timothy 5 in the BOYCB
1 Timothy 5 in the BPBB
1 Timothy 5 in the BPH
1 Timothy 5 in the BSB
1 Timothy 5 in the CCB
1 Timothy 5 in the CUV
1 Timothy 5 in the CUVS
1 Timothy 5 in the DBT
1 Timothy 5 in the DGDNT
1 Timothy 5 in the DHNT
1 Timothy 5 in the DNT
1 Timothy 5 in the ELBE
1 Timothy 5 in the EMTV
1 Timothy 5 in the ESV
1 Timothy 5 in the FBV
1 Timothy 5 in the FEB
1 Timothy 5 in the GGMNT
1 Timothy 5 in the GNT
1 Timothy 5 in the HARY
1 Timothy 5 in the HNT
1 Timothy 5 in the IRVA
1 Timothy 5 in the IRVB
1 Timothy 5 in the IRVG
1 Timothy 5 in the IRVH
1 Timothy 5 in the IRVK
1 Timothy 5 in the IRVM
1 Timothy 5 in the IRVM2
1 Timothy 5 in the IRVO
1 Timothy 5 in the IRVP
1 Timothy 5 in the IRVT
1 Timothy 5 in the IRVT2
1 Timothy 5 in the IRVU
1 Timothy 5 in the ISVN
1 Timothy 5 in the JSNT
1 Timothy 5 in the KAPI
1 Timothy 5 in the KBT1ETNIK
1 Timothy 5 in the KBV
1 Timothy 5 in the KJV
1 Timothy 5 in the KNFD
1 Timothy 5 in the LBA
1 Timothy 5 in the LBLA
1 Timothy 5 in the LNT
1 Timothy 5 in the LSV
1 Timothy 5 in the MAAL
1 Timothy 5 in the MBV
1 Timothy 5 in the MBV2
1 Timothy 5 in the MHNT
1 Timothy 5 in the MKNFD
1 Timothy 5 in the MNG
1 Timothy 5 in the MNT
1 Timothy 5 in the MNT2
1 Timothy 5 in the MRS1T
1 Timothy 5 in the NAA
1 Timothy 5 in the NASB
1 Timothy 5 in the NBLA
1 Timothy 5 in the NBS
1 Timothy 5 in the NBVTP
1 Timothy 5 in the NET2
1 Timothy 5 in the NIV11
1 Timothy 5 in the NNT
1 Timothy 5 in the NNT2
1 Timothy 5 in the NNT3
1 Timothy 5 in the PDDPT
1 Timothy 5 in the PFNT
1 Timothy 5 in the RMNT
1 Timothy 5 in the SBIAS
1 Timothy 5 in the SBIBS
1 Timothy 5 in the SBIBS2
1 Timothy 5 in the SBICS
1 Timothy 5 in the SBIDS
1 Timothy 5 in the SBIGS
1 Timothy 5 in the SBIHS
1 Timothy 5 in the SBIIS
1 Timothy 5 in the SBIIS2
1 Timothy 5 in the SBIIS3
1 Timothy 5 in the SBIKS
1 Timothy 5 in the SBIKS2
1 Timothy 5 in the SBIMS
1 Timothy 5 in the SBIOS
1 Timothy 5 in the SBIPS
1 Timothy 5 in the SBISS
1 Timothy 5 in the SBITS
1 Timothy 5 in the SBITS2
1 Timothy 5 in the SBITS3
1 Timothy 5 in the SBITS4
1 Timothy 5 in the SBIUS
1 Timothy 5 in the SBIVS
1 Timothy 5 in the SBT
1 Timothy 5 in the SBT1E
1 Timothy 5 in the SCHL
1 Timothy 5 in the SNT
1 Timothy 5 in the SUSU
1 Timothy 5 in the SUSU2
1 Timothy 5 in the SYNO
1 Timothy 5 in the TBIAOTANT
1 Timothy 5 in the TBT1E
1 Timothy 5 in the TBT1E2
1 Timothy 5 in the TFTIP
1 Timothy 5 in the TFTU
1 Timothy 5 in the TGNTATF3T
1 Timothy 5 in the THAI
1 Timothy 5 in the TNFD
1 Timothy 5 in the TNT
1 Timothy 5 in the TNTIK
1 Timothy 5 in the TNTIL
1 Timothy 5 in the TNTIN
1 Timothy 5 in the TNTIP
1 Timothy 5 in the TNTIZ
1 Timothy 5 in the TOMA
1 Timothy 5 in the TTENT
1 Timothy 5 in the UBG
1 Timothy 5 in the UGV
1 Timothy 5 in the UGV2
1 Timothy 5 in the UGV3
1 Timothy 5 in the VBL
1 Timothy 5 in the VDCC
1 Timothy 5 in the YALU
1 Timothy 5 in the YAPE
1 Timothy 5 in the YBVTP
1 Timothy 5 in the ZBP