1 Timothy 6 (BOHCB)

1 Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu. 2 Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su ’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su.Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su. 3 In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba, 4 yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace 5 da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi. 6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri. 11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali. 12 Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. 13 Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida, 14 ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi, 15 wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, 16 wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin. 17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce. 20 Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, 21 wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku.

In Other Versions

1 Timothy 6 in the ANGEFD

1 Timothy 6 in the ANTPNG2D

1 Timothy 6 in the AS21

1 Timothy 6 in the BAGH

1 Timothy 6 in the BBPNG

1 Timothy 6 in the BBT1E

1 Timothy 6 in the BDS

1 Timothy 6 in the BEV

1 Timothy 6 in the BHAD

1 Timothy 6 in the BIB

1 Timothy 6 in the BLPT

1 Timothy 6 in the BNT

1 Timothy 6 in the BNTABOOT

1 Timothy 6 in the BNTLV

1 Timothy 6 in the BOATCB

1 Timothy 6 in the BOATCB2

1 Timothy 6 in the BOBCV

1 Timothy 6 in the BOCNT

1 Timothy 6 in the BOECS

1 Timothy 6 in the BOGWICC

1 Timothy 6 in the BOHCV

1 Timothy 6 in the BOHLNT

1 Timothy 6 in the BOHNTLTAL

1 Timothy 6 in the BOICB

1 Timothy 6 in the BOILNTAP

1 Timothy 6 in the BOITCV

1 Timothy 6 in the BOKCV

1 Timothy 6 in the BOKCV2

1 Timothy 6 in the BOKHWOG

1 Timothy 6 in the BOKSSV

1 Timothy 6 in the BOLCB

1 Timothy 6 in the BOLCB2

1 Timothy 6 in the BOMCV

1 Timothy 6 in the BONAV

1 Timothy 6 in the BONCB

1 Timothy 6 in the BONLT

1 Timothy 6 in the BONUT2

1 Timothy 6 in the BOPLNT

1 Timothy 6 in the BOSCB

1 Timothy 6 in the BOSNC

1 Timothy 6 in the BOTLNT

1 Timothy 6 in the BOVCB

1 Timothy 6 in the BOYCB

1 Timothy 6 in the BPBB

1 Timothy 6 in the BPH

1 Timothy 6 in the BSB

1 Timothy 6 in the CCB

1 Timothy 6 in the CUV

1 Timothy 6 in the CUVS

1 Timothy 6 in the DBT

1 Timothy 6 in the DGDNT

1 Timothy 6 in the DHNT

1 Timothy 6 in the DNT

1 Timothy 6 in the ELBE

1 Timothy 6 in the EMTV

1 Timothy 6 in the ESV

1 Timothy 6 in the FBV

1 Timothy 6 in the FEB

1 Timothy 6 in the GGMNT

1 Timothy 6 in the GNT

1 Timothy 6 in the HARY

1 Timothy 6 in the HNT

1 Timothy 6 in the IRVA

1 Timothy 6 in the IRVB

1 Timothy 6 in the IRVG

1 Timothy 6 in the IRVH

1 Timothy 6 in the IRVK

1 Timothy 6 in the IRVM

1 Timothy 6 in the IRVM2

1 Timothy 6 in the IRVO

1 Timothy 6 in the IRVP

1 Timothy 6 in the IRVT

1 Timothy 6 in the IRVT2

1 Timothy 6 in the IRVU

1 Timothy 6 in the ISVN

1 Timothy 6 in the JSNT

1 Timothy 6 in the KAPI

1 Timothy 6 in the KBT1ETNIK

1 Timothy 6 in the KBV

1 Timothy 6 in the KJV

1 Timothy 6 in the KNFD

1 Timothy 6 in the LBA

1 Timothy 6 in the LBLA

1 Timothy 6 in the LNT

1 Timothy 6 in the LSV

1 Timothy 6 in the MAAL

1 Timothy 6 in the MBV

1 Timothy 6 in the MBV2

1 Timothy 6 in the MHNT

1 Timothy 6 in the MKNFD

1 Timothy 6 in the MNG

1 Timothy 6 in the MNT

1 Timothy 6 in the MNT2

1 Timothy 6 in the MRS1T

1 Timothy 6 in the NAA

1 Timothy 6 in the NASB

1 Timothy 6 in the NBLA

1 Timothy 6 in the NBS

1 Timothy 6 in the NBVTP

1 Timothy 6 in the NET2

1 Timothy 6 in the NIV11

1 Timothy 6 in the NNT

1 Timothy 6 in the NNT2

1 Timothy 6 in the NNT3

1 Timothy 6 in the PDDPT

1 Timothy 6 in the PFNT

1 Timothy 6 in the RMNT

1 Timothy 6 in the SBIAS

1 Timothy 6 in the SBIBS

1 Timothy 6 in the SBIBS2

1 Timothy 6 in the SBICS

1 Timothy 6 in the SBIDS

1 Timothy 6 in the SBIGS

1 Timothy 6 in the SBIHS

1 Timothy 6 in the SBIIS

1 Timothy 6 in the SBIIS2

1 Timothy 6 in the SBIIS3

1 Timothy 6 in the SBIKS

1 Timothy 6 in the SBIKS2

1 Timothy 6 in the SBIMS

1 Timothy 6 in the SBIOS

1 Timothy 6 in the SBIPS

1 Timothy 6 in the SBISS

1 Timothy 6 in the SBITS

1 Timothy 6 in the SBITS2

1 Timothy 6 in the SBITS3

1 Timothy 6 in the SBITS4

1 Timothy 6 in the SBIUS

1 Timothy 6 in the SBIVS

1 Timothy 6 in the SBT

1 Timothy 6 in the SBT1E

1 Timothy 6 in the SCHL

1 Timothy 6 in the SNT

1 Timothy 6 in the SUSU

1 Timothy 6 in the SUSU2

1 Timothy 6 in the SYNO

1 Timothy 6 in the TBIAOTANT

1 Timothy 6 in the TBT1E

1 Timothy 6 in the TBT1E2

1 Timothy 6 in the TFTIP

1 Timothy 6 in the TFTU

1 Timothy 6 in the TGNTATF3T

1 Timothy 6 in the THAI

1 Timothy 6 in the TNFD

1 Timothy 6 in the TNT

1 Timothy 6 in the TNTIK

1 Timothy 6 in the TNTIL

1 Timothy 6 in the TNTIN

1 Timothy 6 in the TNTIP

1 Timothy 6 in the TNTIZ

1 Timothy 6 in the TOMA

1 Timothy 6 in the TTENT

1 Timothy 6 in the UBG

1 Timothy 6 in the UGV

1 Timothy 6 in the UGV2

1 Timothy 6 in the UGV3

1 Timothy 6 in the VBL

1 Timothy 6 in the VDCC

1 Timothy 6 in the YALU

1 Timothy 6 in the YAPE

1 Timothy 6 in the YBVTP

1 Timothy 6 in the ZBP