Acts 12 (BOHCB)

1 Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. 2 Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. 3 Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. 4 Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa. 5 Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa. 6 A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. 7 Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa. 8 Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” 9 Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. 10 Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi. 11 Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.” 12 Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a. 13 Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne. 14 Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!” 15 Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.” 16 Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki. 17 Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri. 18 Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus. 19 Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su.Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ’yan kwanaki a can. 20 Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu. 21 A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi. 22 Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.” 23 Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu. 24 Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu. 25 Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.

In Other Versions

Acts 12 in the ANGEFD

Acts 12 in the ANTPNG2D

Acts 12 in the AS21

Acts 12 in the BAGH

Acts 12 in the BBPNG

Acts 12 in the BBT1E

Acts 12 in the BDS

Acts 12 in the BEV

Acts 12 in the BHAD

Acts 12 in the BIB

Acts 12 in the BLPT

Acts 12 in the BNT

Acts 12 in the BNTABOOT

Acts 12 in the BNTLV

Acts 12 in the BOATCB

Acts 12 in the BOATCB2

Acts 12 in the BOBCV

Acts 12 in the BOCNT

Acts 12 in the BOECS

Acts 12 in the BOGWICC

Acts 12 in the BOHCV

Acts 12 in the BOHLNT

Acts 12 in the BOHNTLTAL

Acts 12 in the BOICB

Acts 12 in the BOILNTAP

Acts 12 in the BOITCV

Acts 12 in the BOKCV

Acts 12 in the BOKCV2

Acts 12 in the BOKHWOG

Acts 12 in the BOKSSV

Acts 12 in the BOLCB

Acts 12 in the BOLCB2

Acts 12 in the BOMCV

Acts 12 in the BONAV

Acts 12 in the BONCB

Acts 12 in the BONLT

Acts 12 in the BONUT2

Acts 12 in the BOPLNT

Acts 12 in the BOSCB

Acts 12 in the BOSNC

Acts 12 in the BOTLNT

Acts 12 in the BOVCB

Acts 12 in the BOYCB

Acts 12 in the BPBB

Acts 12 in the BPH

Acts 12 in the BSB

Acts 12 in the CCB

Acts 12 in the CUV

Acts 12 in the CUVS

Acts 12 in the DBT

Acts 12 in the DGDNT

Acts 12 in the DHNT

Acts 12 in the DNT

Acts 12 in the ELBE

Acts 12 in the EMTV

Acts 12 in the ESV

Acts 12 in the FBV

Acts 12 in the FEB

Acts 12 in the GGMNT

Acts 12 in the GNT

Acts 12 in the HARY

Acts 12 in the HNT

Acts 12 in the IRVA

Acts 12 in the IRVB

Acts 12 in the IRVG

Acts 12 in the IRVH

Acts 12 in the IRVK

Acts 12 in the IRVM

Acts 12 in the IRVM2

Acts 12 in the IRVO

Acts 12 in the IRVP

Acts 12 in the IRVT

Acts 12 in the IRVT2

Acts 12 in the IRVU

Acts 12 in the ISVN

Acts 12 in the JSNT

Acts 12 in the KAPI

Acts 12 in the KBT1ETNIK

Acts 12 in the KBV

Acts 12 in the KJV

Acts 12 in the KNFD

Acts 12 in the LBA

Acts 12 in the LBLA

Acts 12 in the LNT

Acts 12 in the LSV

Acts 12 in the MAAL

Acts 12 in the MBV

Acts 12 in the MBV2

Acts 12 in the MHNT

Acts 12 in the MKNFD

Acts 12 in the MNG

Acts 12 in the MNT

Acts 12 in the MNT2

Acts 12 in the MRS1T

Acts 12 in the NAA

Acts 12 in the NASB

Acts 12 in the NBLA

Acts 12 in the NBS

Acts 12 in the NBVTP

Acts 12 in the NET2

Acts 12 in the NIV11

Acts 12 in the NNT

Acts 12 in the NNT2

Acts 12 in the NNT3

Acts 12 in the PDDPT

Acts 12 in the PFNT

Acts 12 in the RMNT

Acts 12 in the SBIAS

Acts 12 in the SBIBS

Acts 12 in the SBIBS2

Acts 12 in the SBICS

Acts 12 in the SBIDS

Acts 12 in the SBIGS

Acts 12 in the SBIHS

Acts 12 in the SBIIS

Acts 12 in the SBIIS2

Acts 12 in the SBIIS3

Acts 12 in the SBIKS

Acts 12 in the SBIKS2

Acts 12 in the SBIMS

Acts 12 in the SBIOS

Acts 12 in the SBIPS

Acts 12 in the SBISS

Acts 12 in the SBITS

Acts 12 in the SBITS2

Acts 12 in the SBITS3

Acts 12 in the SBITS4

Acts 12 in the SBIUS

Acts 12 in the SBIVS

Acts 12 in the SBT

Acts 12 in the SBT1E

Acts 12 in the SCHL

Acts 12 in the SNT

Acts 12 in the SUSU

Acts 12 in the SUSU2

Acts 12 in the SYNO

Acts 12 in the TBIAOTANT

Acts 12 in the TBT1E

Acts 12 in the TBT1E2

Acts 12 in the TFTIP

Acts 12 in the TFTU

Acts 12 in the TGNTATF3T

Acts 12 in the THAI

Acts 12 in the TNFD

Acts 12 in the TNT

Acts 12 in the TNTIK

Acts 12 in the TNTIL

Acts 12 in the TNTIN

Acts 12 in the TNTIP

Acts 12 in the TNTIZ

Acts 12 in the TOMA

Acts 12 in the TTENT

Acts 12 in the UBG

Acts 12 in the UGV

Acts 12 in the UGV2

Acts 12 in the UGV3

Acts 12 in the VBL

Acts 12 in the VDCC

Acts 12 in the YALU

Acts 12 in the YAPE

Acts 12 in the YBVTP

Acts 12 in the ZBP