Acts 16 (BOHCB)

1 Bulus ya kai Derbe sa’an nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa mutuniyar Yahuda ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa mutumin Hellenawa ne. 2 ’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa. 3 Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa mutumin Hellenawa ne. 4 Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye. 5 Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana. 6 Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya. 7 Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba. 8 Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas. 9 Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” 10 Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara. 11 Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, kashegari kuma muka nufi Neyafolis. 12 Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa. 13 A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana. 14 Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus. 15 Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu. 16 Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi. 17 Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” 18 Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita. 19 Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma. 20 Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari, 21 ta wurin koyar da al’adun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.” 22 Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. 23 Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. 24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu. 25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle. 27 Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, sa’ad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ’yan kurkukun sun gudu. 28 Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!” 29 Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila. 30 Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?” 31 Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.” 32 Sa’an nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa. 33 A wannan sa’a na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa. 34 Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa. 35 Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika ma’aikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa, “Ka saki mutanen nan.” 36 Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.” 37 Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu ’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.” 38 Sai ma’aikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro. 39 Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin. 40 Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da ’yan’uwa suka kuma ƙarfafa su. Sa’an nan suka tafi.

In Other Versions

Acts 16 in the ANGEFD

Acts 16 in the ANTPNG2D

Acts 16 in the AS21

Acts 16 in the BAGH

Acts 16 in the BBPNG

Acts 16 in the BBT1E

Acts 16 in the BDS

Acts 16 in the BEV

Acts 16 in the BHAD

Acts 16 in the BIB

Acts 16 in the BLPT

Acts 16 in the BNT

Acts 16 in the BNTABOOT

Acts 16 in the BNTLV

Acts 16 in the BOATCB

Acts 16 in the BOATCB2

Acts 16 in the BOBCV

Acts 16 in the BOCNT

Acts 16 in the BOECS

Acts 16 in the BOGWICC

Acts 16 in the BOHCV

Acts 16 in the BOHLNT

Acts 16 in the BOHNTLTAL

Acts 16 in the BOICB

Acts 16 in the BOILNTAP

Acts 16 in the BOITCV

Acts 16 in the BOKCV

Acts 16 in the BOKCV2

Acts 16 in the BOKHWOG

Acts 16 in the BOKSSV

Acts 16 in the BOLCB

Acts 16 in the BOLCB2

Acts 16 in the BOMCV

Acts 16 in the BONAV

Acts 16 in the BONCB

Acts 16 in the BONLT

Acts 16 in the BONUT2

Acts 16 in the BOPLNT

Acts 16 in the BOSCB

Acts 16 in the BOSNC

Acts 16 in the BOTLNT

Acts 16 in the BOVCB

Acts 16 in the BOYCB

Acts 16 in the BPBB

Acts 16 in the BPH

Acts 16 in the BSB

Acts 16 in the CCB

Acts 16 in the CUV

Acts 16 in the CUVS

Acts 16 in the DBT

Acts 16 in the DGDNT

Acts 16 in the DHNT

Acts 16 in the DNT

Acts 16 in the ELBE

Acts 16 in the EMTV

Acts 16 in the ESV

Acts 16 in the FBV

Acts 16 in the FEB

Acts 16 in the GGMNT

Acts 16 in the GNT

Acts 16 in the HARY

Acts 16 in the HNT

Acts 16 in the IRVA

Acts 16 in the IRVB

Acts 16 in the IRVG

Acts 16 in the IRVH

Acts 16 in the IRVK

Acts 16 in the IRVM

Acts 16 in the IRVM2

Acts 16 in the IRVO

Acts 16 in the IRVP

Acts 16 in the IRVT

Acts 16 in the IRVT2

Acts 16 in the IRVU

Acts 16 in the ISVN

Acts 16 in the JSNT

Acts 16 in the KAPI

Acts 16 in the KBT1ETNIK

Acts 16 in the KBV

Acts 16 in the KJV

Acts 16 in the KNFD

Acts 16 in the LBA

Acts 16 in the LBLA

Acts 16 in the LNT

Acts 16 in the LSV

Acts 16 in the MAAL

Acts 16 in the MBV

Acts 16 in the MBV2

Acts 16 in the MHNT

Acts 16 in the MKNFD

Acts 16 in the MNG

Acts 16 in the MNT

Acts 16 in the MNT2

Acts 16 in the MRS1T

Acts 16 in the NAA

Acts 16 in the NASB

Acts 16 in the NBLA

Acts 16 in the NBS

Acts 16 in the NBVTP

Acts 16 in the NET2

Acts 16 in the NIV11

Acts 16 in the NNT

Acts 16 in the NNT2

Acts 16 in the NNT3

Acts 16 in the PDDPT

Acts 16 in the PFNT

Acts 16 in the RMNT

Acts 16 in the SBIAS

Acts 16 in the SBIBS

Acts 16 in the SBIBS2

Acts 16 in the SBICS

Acts 16 in the SBIDS

Acts 16 in the SBIGS

Acts 16 in the SBIHS

Acts 16 in the SBIIS

Acts 16 in the SBIIS2

Acts 16 in the SBIIS3

Acts 16 in the SBIKS

Acts 16 in the SBIKS2

Acts 16 in the SBIMS

Acts 16 in the SBIOS

Acts 16 in the SBIPS

Acts 16 in the SBISS

Acts 16 in the SBITS

Acts 16 in the SBITS2

Acts 16 in the SBITS3

Acts 16 in the SBITS4

Acts 16 in the SBIUS

Acts 16 in the SBIVS

Acts 16 in the SBT

Acts 16 in the SBT1E

Acts 16 in the SCHL

Acts 16 in the SNT

Acts 16 in the SUSU

Acts 16 in the SUSU2

Acts 16 in the SYNO

Acts 16 in the TBIAOTANT

Acts 16 in the TBT1E

Acts 16 in the TBT1E2

Acts 16 in the TFTIP

Acts 16 in the TFTU

Acts 16 in the TGNTATF3T

Acts 16 in the THAI

Acts 16 in the TNFD

Acts 16 in the TNT

Acts 16 in the TNTIK

Acts 16 in the TNTIL

Acts 16 in the TNTIN

Acts 16 in the TNTIP

Acts 16 in the TNTIZ

Acts 16 in the TOMA

Acts 16 in the TTENT

Acts 16 in the UBG

Acts 16 in the UGV

Acts 16 in the UGV2

Acts 16 in the UGV3

Acts 16 in the VBL

Acts 16 in the VDCC

Acts 16 in the YALU

Acts 16 in the YAPE

Acts 16 in the YBVTP

Acts 16 in the ZBP