Colossians 2 (BOHCB)
1 Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba. 2 Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, 3 a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani. 4 Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki. 5 Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi. 6 To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa, 7 ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya. 8 Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba. 9 Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata, 10 an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma. 11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka. 12 Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu. 13 Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu. 14 Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye. 15 Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye. 16 Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci. 17 Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu. 18 Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka. 19 Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma. 20 Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa, 21 “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”? 22 Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane. 23 Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.
In Other Versions
Colossians 2 in the ANGEFD
Colossians 2 in the ANTPNG2D
Colossians 2 in the AS21
Colossians 2 in the BAGH
Colossians 2 in the BBPNG
Colossians 2 in the BBT1E
Colossians 2 in the BDS
Colossians 2 in the BEV
Colossians 2 in the BHAD
Colossians 2 in the BIB
Colossians 2 in the BLPT
Colossians 2 in the BNT
Colossians 2 in the BNTABOOT
Colossians 2 in the BNTLV
Colossians 2 in the BOATCB
Colossians 2 in the BOATCB2
Colossians 2 in the BOBCV
Colossians 2 in the BOCNT
Colossians 2 in the BOECS
Colossians 2 in the BOGWICC
Colossians 2 in the BOHCV
Colossians 2 in the BOHLNT
Colossians 2 in the BOHNTLTAL
Colossians 2 in the BOICB
Colossians 2 in the BOILNTAP
Colossians 2 in the BOITCV
Colossians 2 in the BOKCV
Colossians 2 in the BOKCV2
Colossians 2 in the BOKHWOG
Colossians 2 in the BOKSSV
Colossians 2 in the BOLCB
Colossians 2 in the BOLCB2
Colossians 2 in the BOMCV
Colossians 2 in the BONAV
Colossians 2 in the BONCB
Colossians 2 in the BONLT
Colossians 2 in the BONUT2
Colossians 2 in the BOPLNT
Colossians 2 in the BOSCB
Colossians 2 in the BOSNC
Colossians 2 in the BOTLNT
Colossians 2 in the BOVCB
Colossians 2 in the BOYCB
Colossians 2 in the BPBB
Colossians 2 in the BPH
Colossians 2 in the BSB
Colossians 2 in the CCB
Colossians 2 in the CUV
Colossians 2 in the CUVS
Colossians 2 in the DBT
Colossians 2 in the DGDNT
Colossians 2 in the DHNT
Colossians 2 in the DNT
Colossians 2 in the ELBE
Colossians 2 in the EMTV
Colossians 2 in the ESV
Colossians 2 in the FBV
Colossians 2 in the FEB
Colossians 2 in the GGMNT
Colossians 2 in the GNT
Colossians 2 in the HARY
Colossians 2 in the HNT
Colossians 2 in the IRVA
Colossians 2 in the IRVB
Colossians 2 in the IRVG
Colossians 2 in the IRVH
Colossians 2 in the IRVK
Colossians 2 in the IRVM
Colossians 2 in the IRVM2
Colossians 2 in the IRVO
Colossians 2 in the IRVP
Colossians 2 in the IRVT
Colossians 2 in the IRVT2
Colossians 2 in the IRVU
Colossians 2 in the ISVN
Colossians 2 in the JSNT
Colossians 2 in the KAPI
Colossians 2 in the KBT1ETNIK
Colossians 2 in the KBV
Colossians 2 in the KJV
Colossians 2 in the KNFD
Colossians 2 in the LBA
Colossians 2 in the LBLA
Colossians 2 in the LNT
Colossians 2 in the LSV
Colossians 2 in the MAAL
Colossians 2 in the MBV
Colossians 2 in the MBV2
Colossians 2 in the MHNT
Colossians 2 in the MKNFD
Colossians 2 in the MNG
Colossians 2 in the MNT
Colossians 2 in the MNT2
Colossians 2 in the MRS1T
Colossians 2 in the NAA
Colossians 2 in the NASB
Colossians 2 in the NBLA
Colossians 2 in the NBS
Colossians 2 in the NBVTP
Colossians 2 in the NET2
Colossians 2 in the NIV11
Colossians 2 in the NNT
Colossians 2 in the NNT2
Colossians 2 in the NNT3
Colossians 2 in the PDDPT
Colossians 2 in the PFNT
Colossians 2 in the RMNT
Colossians 2 in the SBIAS
Colossians 2 in the SBIBS
Colossians 2 in the SBIBS2
Colossians 2 in the SBICS
Colossians 2 in the SBIDS
Colossians 2 in the SBIGS
Colossians 2 in the SBIHS
Colossians 2 in the SBIIS
Colossians 2 in the SBIIS2
Colossians 2 in the SBIIS3
Colossians 2 in the SBIKS
Colossians 2 in the SBIKS2
Colossians 2 in the SBIMS
Colossians 2 in the SBIOS
Colossians 2 in the SBIPS
Colossians 2 in the SBISS
Colossians 2 in the SBITS
Colossians 2 in the SBITS2
Colossians 2 in the SBITS3
Colossians 2 in the SBITS4
Colossians 2 in the SBIUS
Colossians 2 in the SBIVS
Colossians 2 in the SBT
Colossians 2 in the SBT1E
Colossians 2 in the SCHL
Colossians 2 in the SNT
Colossians 2 in the SUSU
Colossians 2 in the SUSU2
Colossians 2 in the SYNO
Colossians 2 in the TBIAOTANT
Colossians 2 in the TBT1E
Colossians 2 in the TBT1E2
Colossians 2 in the TFTIP
Colossians 2 in the TFTU
Colossians 2 in the TGNTATF3T
Colossians 2 in the THAI
Colossians 2 in the TNFD
Colossians 2 in the TNT
Colossians 2 in the TNTIK
Colossians 2 in the TNTIL
Colossians 2 in the TNTIN
Colossians 2 in the TNTIP
Colossians 2 in the TNTIZ
Colossians 2 in the TOMA
Colossians 2 in the TTENT
Colossians 2 in the UBG
Colossians 2 in the UGV
Colossians 2 in the UGV2
Colossians 2 in the UGV3
Colossians 2 in the VBL
Colossians 2 in the VDCC
Colossians 2 in the YALU
Colossians 2 in the YAPE
Colossians 2 in the YBVTP
Colossians 2 in the ZBP