James 1 (BOHCB)
1 Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa. 7 Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji; 8 shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi. 9 Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka. 10 Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji. 11 Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa. 12 Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa. 13 Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; 14 amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. 15 Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa. 16 Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. 18 Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta. 19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so. 21 Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku. 22 Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. 23 Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi 24 bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa. 25 Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi. 26 In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne. 27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
In Other Versions
James 1 in the ANGEFD
James 1 in the ANTPNG2D
James 1 in the AS21
James 1 in the BAGH
James 1 in the BBPNG
James 1 in the BBT1E
James 1 in the BDS
James 1 in the BEV
James 1 in the BHAD
James 1 in the BIB
James 1 in the BLPT
James 1 in the BNT
James 1 in the BNTABOOT
James 1 in the BNTLV
James 1 in the BOATCB
James 1 in the BOATCB2
James 1 in the BOBCV
James 1 in the BOCNT
James 1 in the BOECS
James 1 in the BOGWICC
James 1 in the BOHCV
James 1 in the BOHLNT
James 1 in the BOHNTLTAL
James 1 in the BOICB
James 1 in the BOILNTAP
James 1 in the BOITCV
James 1 in the BOKCV
James 1 in the BOKCV2
James 1 in the BOKHWOG
James 1 in the BOKSSV
James 1 in the BOLCB
James 1 in the BOLCB2
James 1 in the BOMCV
James 1 in the BONAV
James 1 in the BONCB
James 1 in the BONLT
James 1 in the BONUT2
James 1 in the BOPLNT
James 1 in the BOSCB
James 1 in the BOSNC
James 1 in the BOTLNT
James 1 in the BOVCB
James 1 in the BOYCB
James 1 in the BPBB
James 1 in the BPH
James 1 in the BSB
James 1 in the CCB
James 1 in the CUV
James 1 in the CUVS
James 1 in the DBT
James 1 in the DGDNT
James 1 in the DHNT
James 1 in the DNT
James 1 in the ELBE
James 1 in the EMTV
James 1 in the ESV
James 1 in the FBV
James 1 in the FEB
James 1 in the GGMNT
James 1 in the GNT
James 1 in the HARY
James 1 in the HNT
James 1 in the IRVA
James 1 in the IRVB
James 1 in the IRVG
James 1 in the IRVH
James 1 in the IRVK
James 1 in the IRVM
James 1 in the IRVM2
James 1 in the IRVO
James 1 in the IRVP
James 1 in the IRVT
James 1 in the IRVT2
James 1 in the IRVU
James 1 in the ISVN
James 1 in the JSNT
James 1 in the KAPI
James 1 in the KBT1ETNIK
James 1 in the KBV
James 1 in the KJV
James 1 in the KNFD
James 1 in the LBA
James 1 in the LBLA
James 1 in the LNT
James 1 in the LSV
James 1 in the MAAL
James 1 in the MBV
James 1 in the MBV2
James 1 in the MHNT
James 1 in the MKNFD
James 1 in the MNG
James 1 in the MNT
James 1 in the MNT2
James 1 in the MRS1T
James 1 in the NAA
James 1 in the NASB
James 1 in the NBLA
James 1 in the NBS
James 1 in the NBVTP
James 1 in the NET2
James 1 in the NIV11
James 1 in the NNT
James 1 in the NNT2
James 1 in the NNT3
James 1 in the PDDPT
James 1 in the PFNT
James 1 in the RMNT
James 1 in the SBIAS
James 1 in the SBIBS
James 1 in the SBIBS2
James 1 in the SBICS
James 1 in the SBIDS
James 1 in the SBIGS
James 1 in the SBIHS
James 1 in the SBIIS
James 1 in the SBIIS2
James 1 in the SBIIS3
James 1 in the SBIKS
James 1 in the SBIKS2
James 1 in the SBIMS
James 1 in the SBIOS
James 1 in the SBIPS
James 1 in the SBISS
James 1 in the SBITS
James 1 in the SBITS2
James 1 in the SBITS3
James 1 in the SBITS4
James 1 in the SBIUS
James 1 in the SBIVS
James 1 in the SBT
James 1 in the SBT1E
James 1 in the SCHL
James 1 in the SNT
James 1 in the SUSU
James 1 in the SUSU2
James 1 in the SYNO
James 1 in the TBIAOTANT
James 1 in the TBT1E
James 1 in the TBT1E2
James 1 in the TFTIP
James 1 in the TFTU
James 1 in the TGNTATF3T
James 1 in the THAI
James 1 in the TNFD
James 1 in the TNT
James 1 in the TNTIK
James 1 in the TNTIL
James 1 in the TNTIN
James 1 in the TNTIP
James 1 in the TNTIZ
James 1 in the TOMA
James 1 in the TTENT
James 1 in the UBG
James 1 in the UGV
James 1 in the UGV2
James 1 in the UGV3
James 1 in the VBL
James 1 in the VDCC
James 1 in the YALU
James 1 in the YAPE
James 1 in the YBVTP
James 1 in the ZBP