John 14 (BOHCB)
1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.” 5 Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?” 6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. 7 Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.” 8 Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.” 9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? 10 Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. 11 Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu. 12 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba. 13 Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. 14 Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi. 15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. 16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, 17 Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. 18 Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku. 19 Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu. 20 A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku. 21 Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.” 22 Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?” 23 Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni. 25 “Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku. 26 Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro. 28 “Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29 Na faɗa muku tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata. 30 Ba zan ƙara yi muku magana ba, gama mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Ba shi da iko a kaina, 31 amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni. “Ku zo, mu bar nan.
In Other Versions
John 14 in the ANGEFD
John 14 in the ANTPNG2D
John 14 in the AS21
John 14 in the BAGH
John 14 in the BBPNG
John 14 in the BBT1E
John 14 in the BDS
John 14 in the BEV
John 14 in the BHAD
John 14 in the BIB
John 14 in the BLPT
John 14 in the BNT
John 14 in the BNTABOOT
John 14 in the BNTLV
John 14 in the BOATCB
John 14 in the BOATCB2
John 14 in the BOBCV
John 14 in the BOCNT
John 14 in the BOECS
John 14 in the BOGWICC
John 14 in the BOHCV
John 14 in the BOHLNT
John 14 in the BOHNTLTAL
John 14 in the BOICB
John 14 in the BOILNTAP
John 14 in the BOITCV
John 14 in the BOKCV
John 14 in the BOKCV2
John 14 in the BOKHWOG
John 14 in the BOKSSV
John 14 in the BOLCB
John 14 in the BOLCB2
John 14 in the BOMCV
John 14 in the BONAV
John 14 in the BONCB
John 14 in the BONLT
John 14 in the BONUT2
John 14 in the BOPLNT
John 14 in the BOSCB
John 14 in the BOSNC
John 14 in the BOTLNT
John 14 in the BOVCB
John 14 in the BOYCB
John 14 in the BPBB
John 14 in the BPH
John 14 in the BSB
John 14 in the CCB
John 14 in the CUV
John 14 in the CUVS
John 14 in the DBT
John 14 in the DGDNT
John 14 in the DHNT
John 14 in the DNT
John 14 in the ELBE
John 14 in the EMTV
John 14 in the ESV
John 14 in the FBV
John 14 in the FEB
John 14 in the GGMNT
John 14 in the GNT
John 14 in the HARY
John 14 in the HNT
John 14 in the IRVA
John 14 in the IRVB
John 14 in the IRVG
John 14 in the IRVH
John 14 in the IRVK
John 14 in the IRVM
John 14 in the IRVM2
John 14 in the IRVO
John 14 in the IRVP
John 14 in the IRVT
John 14 in the IRVT2
John 14 in the IRVU
John 14 in the ISVN
John 14 in the JSNT
John 14 in the KAPI
John 14 in the KBT1ETNIK
John 14 in the KBV
John 14 in the KJV
John 14 in the KNFD
John 14 in the LBA
John 14 in the LBLA
John 14 in the LNT
John 14 in the LSV
John 14 in the MAAL
John 14 in the MBV
John 14 in the MBV2
John 14 in the MHNT
John 14 in the MKNFD
John 14 in the MNG
John 14 in the MNT
John 14 in the MNT2
John 14 in the MRS1T
John 14 in the NAA
John 14 in the NASB
John 14 in the NBLA
John 14 in the NBS
John 14 in the NBVTP
John 14 in the NET2
John 14 in the NIV11
John 14 in the NNT
John 14 in the NNT2
John 14 in the NNT3
John 14 in the PDDPT
John 14 in the PFNT
John 14 in the RMNT
John 14 in the SBIAS
John 14 in the SBIBS
John 14 in the SBIBS2
John 14 in the SBICS
John 14 in the SBIDS
John 14 in the SBIGS
John 14 in the SBIHS
John 14 in the SBIIS
John 14 in the SBIIS2
John 14 in the SBIIS3
John 14 in the SBIKS
John 14 in the SBIKS2
John 14 in the SBIMS
John 14 in the SBIOS
John 14 in the SBIPS
John 14 in the SBISS
John 14 in the SBITS
John 14 in the SBITS2
John 14 in the SBITS3
John 14 in the SBITS4
John 14 in the SBIUS
John 14 in the SBIVS
John 14 in the SBT
John 14 in the SBT1E
John 14 in the SCHL
John 14 in the SNT
John 14 in the SUSU
John 14 in the SUSU2
John 14 in the SYNO
John 14 in the TBIAOTANT
John 14 in the TBT1E
John 14 in the TBT1E2
John 14 in the TFTIP
John 14 in the TFTU
John 14 in the TGNTATF3T
John 14 in the THAI
John 14 in the TNFD
John 14 in the TNT
John 14 in the TNTIK
John 14 in the TNTIL
John 14 in the TNTIN
John 14 in the TNTIP
John 14 in the TNTIZ
John 14 in the TOMA
John 14 in the TTENT
John 14 in the UBG
John 14 in the UGV
John 14 in the UGV2
John 14 in the UGV3
John 14 in the VBL
John 14 in the VDCC
John 14 in the YALU
John 14 in the YAPE
John 14 in the YBVTP
John 14 in the ZBP