John 18 (BOHCB)

1 Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki. 2 To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. 3 Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai. 4 Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?” 5 Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.”Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) 6 Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa. 7 Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?”Suka ce, “Yesu Banazare.” 8 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne shi. In kuma ni ne kuke nema, to, sai ku bar waɗannan su tafi.” 9 Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa, “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.” 10 Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.) 11 Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?” 12 Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma ma’aikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka daure shi 13 sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. 14 Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane. 15 Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin, 16 Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus. 17 Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?”Bitrus ya amsa ya ce, “A’a, ba na ciki.” 18 To, ana sanyi, bayi da ma’aikatan suna tsattsaye kewaye da wutar da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi. 19 Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa. 20 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. 21 Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.” 22 Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” 23 Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?” 24 Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist. 25 Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?”Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.” 26 Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?” 27 Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara. 28 Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. 29 Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?” 30 Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.” 31 Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.”Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.” 32 Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi. 33 Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?” 34 Yesu ya yi tambaya ya ce, “Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?” 35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?” 36 Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.” 37 Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.” 38 Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?”Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba. 39 Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?” 40 Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.

In Other Versions

John 18 in the ANGEFD

John 18 in the ANTPNG2D

John 18 in the AS21

John 18 in the BAGH

John 18 in the BBPNG

John 18 in the BBT1E

John 18 in the BDS

John 18 in the BEV

John 18 in the BHAD

John 18 in the BIB

John 18 in the BLPT

John 18 in the BNT

John 18 in the BNTABOOT

John 18 in the BNTLV

John 18 in the BOATCB

John 18 in the BOATCB2

John 18 in the BOBCV

John 18 in the BOCNT

John 18 in the BOECS

John 18 in the BOGWICC

John 18 in the BOHCV

John 18 in the BOHLNT

John 18 in the BOHNTLTAL

John 18 in the BOICB

John 18 in the BOILNTAP

John 18 in the BOITCV

John 18 in the BOKCV

John 18 in the BOKCV2

John 18 in the BOKHWOG

John 18 in the BOKSSV

John 18 in the BOLCB

John 18 in the BOLCB2

John 18 in the BOMCV

John 18 in the BONAV

John 18 in the BONCB

John 18 in the BONLT

John 18 in the BONUT2

John 18 in the BOPLNT

John 18 in the BOSCB

John 18 in the BOSNC

John 18 in the BOTLNT

John 18 in the BOVCB

John 18 in the BOYCB

John 18 in the BPBB

John 18 in the BPH

John 18 in the BSB

John 18 in the CCB

John 18 in the CUV

John 18 in the CUVS

John 18 in the DBT

John 18 in the DGDNT

John 18 in the DHNT

John 18 in the DNT

John 18 in the ELBE

John 18 in the EMTV

John 18 in the ESV

John 18 in the FBV

John 18 in the FEB

John 18 in the GGMNT

John 18 in the GNT

John 18 in the HARY

John 18 in the HNT

John 18 in the IRVA

John 18 in the IRVB

John 18 in the IRVG

John 18 in the IRVH

John 18 in the IRVK

John 18 in the IRVM

John 18 in the IRVM2

John 18 in the IRVO

John 18 in the IRVP

John 18 in the IRVT

John 18 in the IRVT2

John 18 in the IRVU

John 18 in the ISVN

John 18 in the JSNT

John 18 in the KAPI

John 18 in the KBT1ETNIK

John 18 in the KBV

John 18 in the KJV

John 18 in the KNFD

John 18 in the LBA

John 18 in the LBLA

John 18 in the LNT

John 18 in the LSV

John 18 in the MAAL

John 18 in the MBV

John 18 in the MBV2

John 18 in the MHNT

John 18 in the MKNFD

John 18 in the MNG

John 18 in the MNT

John 18 in the MNT2

John 18 in the MRS1T

John 18 in the NAA

John 18 in the NASB

John 18 in the NBLA

John 18 in the NBS

John 18 in the NBVTP

John 18 in the NET2

John 18 in the NIV11

John 18 in the NNT

John 18 in the NNT2

John 18 in the NNT3

John 18 in the PDDPT

John 18 in the PFNT

John 18 in the RMNT

John 18 in the SBIAS

John 18 in the SBIBS

John 18 in the SBIBS2

John 18 in the SBICS

John 18 in the SBIDS

John 18 in the SBIGS

John 18 in the SBIHS

John 18 in the SBIIS

John 18 in the SBIIS2

John 18 in the SBIIS3

John 18 in the SBIKS

John 18 in the SBIKS2

John 18 in the SBIMS

John 18 in the SBIOS

John 18 in the SBIPS

John 18 in the SBISS

John 18 in the SBITS

John 18 in the SBITS2

John 18 in the SBITS3

John 18 in the SBITS4

John 18 in the SBIUS

John 18 in the SBIVS

John 18 in the SBT

John 18 in the SBT1E

John 18 in the SCHL

John 18 in the SNT

John 18 in the SUSU

John 18 in the SUSU2

John 18 in the SYNO

John 18 in the TBIAOTANT

John 18 in the TBT1E

John 18 in the TBT1E2

John 18 in the TFTIP

John 18 in the TFTU

John 18 in the TGNTATF3T

John 18 in the THAI

John 18 in the TNFD

John 18 in the TNT

John 18 in the TNTIK

John 18 in the TNTIL

John 18 in the TNTIN

John 18 in the TNTIP

John 18 in the TNTIZ

John 18 in the TOMA

John 18 in the TTENT

John 18 in the UBG

John 18 in the UGV

John 18 in the UGV2

John 18 in the UGV3

John 18 in the VBL

John 18 in the VDCC

John 18 in the YALU

John 18 in the YAPE

John 18 in the YBVTP

John 18 in the ZBP