John 9 (BOHCB)

1 Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?” 3 Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. 5 Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.” 6 Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. 7 Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani. 8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?” 9 Waɗansu suka ce shi mana.Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.”Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.” 10 Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?” 11 Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.” 12 Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?”Ya ce, “Ban sani ba.” 13 Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa. 14 To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce. 15 Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.” 16 Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.”Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban. 17 A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.”Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.” 18 Yahudawa dai ba su yarda cewa dā shi makaho ne ya kuma sami ganin gari ba, sai da suka kira iyayen mutumin. 19 Suka tambaye su, “Wannan ɗanku ne? Shi ne wanda kuka ce an haife shi makaho? To, ta yaya yake gani yanzu?” 20 Iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san shi ɗanmu ne, mun kuma san cewa an haife shi makaho. 21 Sai dai yadda yake gani yanzu, ko kuma wa ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi. Ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” 22 Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore shi daga majami’a. 23 Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.” 24 Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.” 25 Sai ya amsa ya ce, “Ko shi mai zunubi ne ko babu, ni dai ban sani ba. Abu ɗaya fa na sani, dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani!” 26 Sai suka tambaye suka ce, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?” 27 Ya amsa ya ce, “Na riga na gaya muku ba ku kuwa saurara ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28 Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne! 29 Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.” 30 Sai mutumin ya ce, “Cabɗi, yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe idanuna. 31 Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa. 32 Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho. 33 Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.” 34 Sai suka amsa suka ce, “Kai da aka haifa cike da zunubi; za ka yi karambanin koyarwar da mu!” Sai suka kore shi. 35 Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?” 36 Sai mutumin ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.” 37 Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.” 38 Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada. 39 Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.” 40 Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?” 41 Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.

In Other Versions

John 9 in the ANGEFD

John 9 in the ANTPNG2D

John 9 in the AS21

John 9 in the BAGH

John 9 in the BBPNG

John 9 in the BBT1E

John 9 in the BDS

John 9 in the BEV

John 9 in the BHAD

John 9 in the BIB

John 9 in the BLPT

John 9 in the BNT

John 9 in the BNTABOOT

John 9 in the BNTLV

John 9 in the BOATCB

John 9 in the BOATCB2

John 9 in the BOBCV

John 9 in the BOCNT

John 9 in the BOECS

John 9 in the BOGWICC

John 9 in the BOHCV

John 9 in the BOHLNT

John 9 in the BOHNTLTAL

John 9 in the BOICB

John 9 in the BOILNTAP

John 9 in the BOITCV

John 9 in the BOKCV

John 9 in the BOKCV2

John 9 in the BOKHWOG

John 9 in the BOKSSV

John 9 in the BOLCB

John 9 in the BOLCB2

John 9 in the BOMCV

John 9 in the BONAV

John 9 in the BONCB

John 9 in the BONLT

John 9 in the BONUT2

John 9 in the BOPLNT

John 9 in the BOSCB

John 9 in the BOSNC

John 9 in the BOTLNT

John 9 in the BOVCB

John 9 in the BOYCB

John 9 in the BPBB

John 9 in the BPH

John 9 in the BSB

John 9 in the CCB

John 9 in the CUV

John 9 in the CUVS

John 9 in the DBT

John 9 in the DGDNT

John 9 in the DHNT

John 9 in the DNT

John 9 in the ELBE

John 9 in the EMTV

John 9 in the ESV

John 9 in the FBV

John 9 in the FEB

John 9 in the GGMNT

John 9 in the GNT

John 9 in the HARY

John 9 in the HNT

John 9 in the IRVA

John 9 in the IRVB

John 9 in the IRVG

John 9 in the IRVH

John 9 in the IRVK

John 9 in the IRVM

John 9 in the IRVM2

John 9 in the IRVO

John 9 in the IRVP

John 9 in the IRVT

John 9 in the IRVT2

John 9 in the IRVU

John 9 in the ISVN

John 9 in the JSNT

John 9 in the KAPI

John 9 in the KBT1ETNIK

John 9 in the KBV

John 9 in the KJV

John 9 in the KNFD

John 9 in the LBA

John 9 in the LBLA

John 9 in the LNT

John 9 in the LSV

John 9 in the MAAL

John 9 in the MBV

John 9 in the MBV2

John 9 in the MHNT

John 9 in the MKNFD

John 9 in the MNG

John 9 in the MNT

John 9 in the MNT2

John 9 in the MRS1T

John 9 in the NAA

John 9 in the NASB

John 9 in the NBLA

John 9 in the NBS

John 9 in the NBVTP

John 9 in the NET2

John 9 in the NIV11

John 9 in the NNT

John 9 in the NNT2

John 9 in the NNT3

John 9 in the PDDPT

John 9 in the PFNT

John 9 in the RMNT

John 9 in the SBIAS

John 9 in the SBIBS

John 9 in the SBIBS2

John 9 in the SBICS

John 9 in the SBIDS

John 9 in the SBIGS

John 9 in the SBIHS

John 9 in the SBIIS

John 9 in the SBIIS2

John 9 in the SBIIS3

John 9 in the SBIKS

John 9 in the SBIKS2

John 9 in the SBIMS

John 9 in the SBIOS

John 9 in the SBIPS

John 9 in the SBISS

John 9 in the SBITS

John 9 in the SBITS2

John 9 in the SBITS3

John 9 in the SBITS4

John 9 in the SBIUS

John 9 in the SBIVS

John 9 in the SBT

John 9 in the SBT1E

John 9 in the SCHL

John 9 in the SNT

John 9 in the SUSU

John 9 in the SUSU2

John 9 in the SYNO

John 9 in the TBIAOTANT

John 9 in the TBT1E

John 9 in the TBT1E2

John 9 in the TFTIP

John 9 in the TFTU

John 9 in the TGNTATF3T

John 9 in the THAI

John 9 in the TNFD

John 9 in the TNT

John 9 in the TNTIK

John 9 in the TNTIL

John 9 in the TNTIN

John 9 in the TNTIP

John 9 in the TNTIZ

John 9 in the TOMA

John 9 in the TTENT

John 9 in the UBG

John 9 in the UGV

John 9 in the UGV2

John 9 in the UGV3

John 9 in the VBL

John 9 in the VDCC

John 9 in the YALU

John 9 in the YAPE

John 9 in the YBVTP

John 9 in the ZBP