Luke 17 (BOHCB)

1 Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. 2 Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi. 3 Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa. 4 In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.” 5 Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!” 6 Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya. 7 “In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’? 8 Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’? 9 Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne? 10 Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ” 11 Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. 12 Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13 suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!” 14 Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce. 15 Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16 Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne. 17 Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18 Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?” 19 Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” 20 Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba. 21 Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.” 22 Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. 23 Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu. 24 Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa. 25 Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi. 26 “Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum. 27 Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka. 28 “Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. 29 Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka. 30 “Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana. 31 A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu. 32 Ku tuna fa da matar Lot! 33 Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi. 34 Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. 35 Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.” 37 Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?”Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”

In Other Versions

Luke 17 in the ANGEFD

Luke 17 in the ANTPNG2D

Luke 17 in the AS21

Luke 17 in the BAGH

Luke 17 in the BBPNG

Luke 17 in the BBT1E

Luke 17 in the BDS

Luke 17 in the BEV

Luke 17 in the BHAD

Luke 17 in the BIB

Luke 17 in the BLPT

Luke 17 in the BNT

Luke 17 in the BNTABOOT

Luke 17 in the BNTLV

Luke 17 in the BOATCB

Luke 17 in the BOATCB2

Luke 17 in the BOBCV

Luke 17 in the BOCNT

Luke 17 in the BOECS

Luke 17 in the BOGWICC

Luke 17 in the BOHCV

Luke 17 in the BOHLNT

Luke 17 in the BOHNTLTAL

Luke 17 in the BOICB

Luke 17 in the BOILNTAP

Luke 17 in the BOITCV

Luke 17 in the BOKCV

Luke 17 in the BOKCV2

Luke 17 in the BOKHWOG

Luke 17 in the BOKSSV

Luke 17 in the BOLCB

Luke 17 in the BOLCB2

Luke 17 in the BOMCV

Luke 17 in the BONAV

Luke 17 in the BONCB

Luke 17 in the BONLT

Luke 17 in the BONUT2

Luke 17 in the BOPLNT

Luke 17 in the BOSCB

Luke 17 in the BOSNC

Luke 17 in the BOTLNT

Luke 17 in the BOVCB

Luke 17 in the BOYCB

Luke 17 in the BPBB

Luke 17 in the BPH

Luke 17 in the BSB

Luke 17 in the CCB

Luke 17 in the CUV

Luke 17 in the CUVS

Luke 17 in the DBT

Luke 17 in the DGDNT

Luke 17 in the DHNT

Luke 17 in the DNT

Luke 17 in the ELBE

Luke 17 in the EMTV

Luke 17 in the ESV

Luke 17 in the FBV

Luke 17 in the FEB

Luke 17 in the GGMNT

Luke 17 in the GNT

Luke 17 in the HARY

Luke 17 in the HNT

Luke 17 in the IRVA

Luke 17 in the IRVB

Luke 17 in the IRVG

Luke 17 in the IRVH

Luke 17 in the IRVK

Luke 17 in the IRVM

Luke 17 in the IRVM2

Luke 17 in the IRVO

Luke 17 in the IRVP

Luke 17 in the IRVT

Luke 17 in the IRVT2

Luke 17 in the IRVU

Luke 17 in the ISVN

Luke 17 in the JSNT

Luke 17 in the KAPI

Luke 17 in the KBT1ETNIK

Luke 17 in the KBV

Luke 17 in the KJV

Luke 17 in the KNFD

Luke 17 in the LBA

Luke 17 in the LBLA

Luke 17 in the LNT

Luke 17 in the LSV

Luke 17 in the MAAL

Luke 17 in the MBV

Luke 17 in the MBV2

Luke 17 in the MHNT

Luke 17 in the MKNFD

Luke 17 in the MNG

Luke 17 in the MNT

Luke 17 in the MNT2

Luke 17 in the MRS1T

Luke 17 in the NAA

Luke 17 in the NASB

Luke 17 in the NBLA

Luke 17 in the NBS

Luke 17 in the NBVTP

Luke 17 in the NET2

Luke 17 in the NIV11

Luke 17 in the NNT

Luke 17 in the NNT2

Luke 17 in the NNT3

Luke 17 in the PDDPT

Luke 17 in the PFNT

Luke 17 in the RMNT

Luke 17 in the SBIAS

Luke 17 in the SBIBS

Luke 17 in the SBIBS2

Luke 17 in the SBICS

Luke 17 in the SBIDS

Luke 17 in the SBIGS

Luke 17 in the SBIHS

Luke 17 in the SBIIS

Luke 17 in the SBIIS2

Luke 17 in the SBIIS3

Luke 17 in the SBIKS

Luke 17 in the SBIKS2

Luke 17 in the SBIMS

Luke 17 in the SBIOS

Luke 17 in the SBIPS

Luke 17 in the SBISS

Luke 17 in the SBITS

Luke 17 in the SBITS2

Luke 17 in the SBITS3

Luke 17 in the SBITS4

Luke 17 in the SBIUS

Luke 17 in the SBIVS

Luke 17 in the SBT

Luke 17 in the SBT1E

Luke 17 in the SCHL

Luke 17 in the SNT

Luke 17 in the SUSU

Luke 17 in the SUSU2

Luke 17 in the SYNO

Luke 17 in the TBIAOTANT

Luke 17 in the TBT1E

Luke 17 in the TBT1E2

Luke 17 in the TFTIP

Luke 17 in the TFTU

Luke 17 in the TGNTATF3T

Luke 17 in the THAI

Luke 17 in the TNFD

Luke 17 in the TNT

Luke 17 in the TNTIK

Luke 17 in the TNTIL

Luke 17 in the TNTIN

Luke 17 in the TNTIP

Luke 17 in the TNTIZ

Luke 17 in the TOMA

Luke 17 in the TTENT

Luke 17 in the UBG

Luke 17 in the UGV

Luke 17 in the UGV2

Luke 17 in the UGV3

Luke 17 in the VBL

Luke 17 in the VDCC

Luke 17 in the YALU

Luke 17 in the YAPE

Luke 17 in the YBVTP

Luke 17 in the ZBP