Luke 18 (BOHCB)

1 Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa. 2 Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba. 3 A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka yi mini adalci tsakanina da maƙiyina.’ 4 “An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba, 5 amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada tă gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ” 6 Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce. 7 Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne? 8 Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?” 9 Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce, 10 “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. 11 Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. 12 Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’ 13 “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’ 14 “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.” 15 Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su. 16 Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 17 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” 18 Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?” 19 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 20 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ” 21 Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.” 22 Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.” 23 Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. 24 Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! 25 Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.” 26 Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?” 27 Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.” 28 Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!” 29 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, 30 da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.” 31 Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika. 32 Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau, 33 za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.” 34 Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu ma’anarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba. 35 Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36 Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37 Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.” 38 Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 39 Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 40 Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, 41 “Me kake so in yi maka?”Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.” 42 Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43 Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.

In Other Versions

Luke 18 in the ANGEFD

Luke 18 in the ANTPNG2D

Luke 18 in the AS21

Luke 18 in the BAGH

Luke 18 in the BBPNG

Luke 18 in the BBT1E

Luke 18 in the BDS

Luke 18 in the BEV

Luke 18 in the BHAD

Luke 18 in the BIB

Luke 18 in the BLPT

Luke 18 in the BNT

Luke 18 in the BNTABOOT

Luke 18 in the BNTLV

Luke 18 in the BOATCB

Luke 18 in the BOATCB2

Luke 18 in the BOBCV

Luke 18 in the BOCNT

Luke 18 in the BOECS

Luke 18 in the BOGWICC

Luke 18 in the BOHCV

Luke 18 in the BOHLNT

Luke 18 in the BOHNTLTAL

Luke 18 in the BOICB

Luke 18 in the BOILNTAP

Luke 18 in the BOITCV

Luke 18 in the BOKCV

Luke 18 in the BOKCV2

Luke 18 in the BOKHWOG

Luke 18 in the BOKSSV

Luke 18 in the BOLCB

Luke 18 in the BOLCB2

Luke 18 in the BOMCV

Luke 18 in the BONAV

Luke 18 in the BONCB

Luke 18 in the BONLT

Luke 18 in the BONUT2

Luke 18 in the BOPLNT

Luke 18 in the BOSCB

Luke 18 in the BOSNC

Luke 18 in the BOTLNT

Luke 18 in the BOVCB

Luke 18 in the BOYCB

Luke 18 in the BPBB

Luke 18 in the BPH

Luke 18 in the BSB

Luke 18 in the CCB

Luke 18 in the CUV

Luke 18 in the CUVS

Luke 18 in the DBT

Luke 18 in the DGDNT

Luke 18 in the DHNT

Luke 18 in the DNT

Luke 18 in the ELBE

Luke 18 in the EMTV

Luke 18 in the ESV

Luke 18 in the FBV

Luke 18 in the FEB

Luke 18 in the GGMNT

Luke 18 in the GNT

Luke 18 in the HARY

Luke 18 in the HNT

Luke 18 in the IRVA

Luke 18 in the IRVB

Luke 18 in the IRVG

Luke 18 in the IRVH

Luke 18 in the IRVK

Luke 18 in the IRVM

Luke 18 in the IRVM2

Luke 18 in the IRVO

Luke 18 in the IRVP

Luke 18 in the IRVT

Luke 18 in the IRVT2

Luke 18 in the IRVU

Luke 18 in the ISVN

Luke 18 in the JSNT

Luke 18 in the KAPI

Luke 18 in the KBT1ETNIK

Luke 18 in the KBV

Luke 18 in the KJV

Luke 18 in the KNFD

Luke 18 in the LBA

Luke 18 in the LBLA

Luke 18 in the LNT

Luke 18 in the LSV

Luke 18 in the MAAL

Luke 18 in the MBV

Luke 18 in the MBV2

Luke 18 in the MHNT

Luke 18 in the MKNFD

Luke 18 in the MNG

Luke 18 in the MNT

Luke 18 in the MNT2

Luke 18 in the MRS1T

Luke 18 in the NAA

Luke 18 in the NASB

Luke 18 in the NBLA

Luke 18 in the NBS

Luke 18 in the NBVTP

Luke 18 in the NET2

Luke 18 in the NIV11

Luke 18 in the NNT

Luke 18 in the NNT2

Luke 18 in the NNT3

Luke 18 in the PDDPT

Luke 18 in the PFNT

Luke 18 in the RMNT

Luke 18 in the SBIAS

Luke 18 in the SBIBS

Luke 18 in the SBIBS2

Luke 18 in the SBICS

Luke 18 in the SBIDS

Luke 18 in the SBIGS

Luke 18 in the SBIHS

Luke 18 in the SBIIS

Luke 18 in the SBIIS2

Luke 18 in the SBIIS3

Luke 18 in the SBIKS

Luke 18 in the SBIKS2

Luke 18 in the SBIMS

Luke 18 in the SBIOS

Luke 18 in the SBIPS

Luke 18 in the SBISS

Luke 18 in the SBITS

Luke 18 in the SBITS2

Luke 18 in the SBITS3

Luke 18 in the SBITS4

Luke 18 in the SBIUS

Luke 18 in the SBIVS

Luke 18 in the SBT

Luke 18 in the SBT1E

Luke 18 in the SCHL

Luke 18 in the SNT

Luke 18 in the SUSU

Luke 18 in the SUSU2

Luke 18 in the SYNO

Luke 18 in the TBIAOTANT

Luke 18 in the TBT1E

Luke 18 in the TBT1E2

Luke 18 in the TFTIP

Luke 18 in the TFTU

Luke 18 in the TGNTATF3T

Luke 18 in the THAI

Luke 18 in the TNFD

Luke 18 in the TNT

Luke 18 in the TNTIK

Luke 18 in the TNTIL

Luke 18 in the TNTIN

Luke 18 in the TNTIP

Luke 18 in the TNTIZ

Luke 18 in the TOMA

Luke 18 in the TTENT

Luke 18 in the UBG

Luke 18 in the UGV

Luke 18 in the UGV2

Luke 18 in the UGV3

Luke 18 in the VBL

Luke 18 in the VDCC

Luke 18 in the YALU

Luke 18 in the YAPE

Luke 18 in the YBVTP

Luke 18 in the ZBP