Luke 24 (BOHCB)

1 Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya. 2 Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin. 3 Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba. 4 Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya. 5 A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu? 6 Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa, 7 ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ” 8 Sai suka tuna da maganarsa. 9 Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa. 10 Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su. 11 Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne. 12 Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru. 13 A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima. 14 Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru. 15 Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su. 16 Amma ba a ba su ikon gane shi ba. 17 Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?”Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu. 18 Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?” 19 Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?”Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane. 20 Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi. 21 Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru. 22 Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan, 23 amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai. 24 Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.” 25 Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa! 26 Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa. 27 Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.” 28 Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba. 29 Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu. 30 Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su. 31 Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu. 32 Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.” 33 Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya, 34 suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman” 35 Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin. 36 Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!” 37 Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani. 38 Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku? 39 Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.” 40 Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa. 41 Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?” 42 Suka ba shi ɗan gasasshen kifi, 43 ya karɓa ya ci a gabansu. 44 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.” 45 Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. 46 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. 47 Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49 Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.” 50 Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka. 51 Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama. 52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. 53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

In Other Versions

Luke 24 in the ANGEFD

Luke 24 in the ANTPNG2D

Luke 24 in the AS21

Luke 24 in the BAGH

Luke 24 in the BBPNG

Luke 24 in the BBT1E

Luke 24 in the BDS

Luke 24 in the BEV

Luke 24 in the BHAD

Luke 24 in the BIB

Luke 24 in the BLPT

Luke 24 in the BNT

Luke 24 in the BNTABOOT

Luke 24 in the BNTLV

Luke 24 in the BOATCB

Luke 24 in the BOATCB2

Luke 24 in the BOBCV

Luke 24 in the BOCNT

Luke 24 in the BOECS

Luke 24 in the BOGWICC

Luke 24 in the BOHCV

Luke 24 in the BOHLNT

Luke 24 in the BOHNTLTAL

Luke 24 in the BOICB

Luke 24 in the BOILNTAP

Luke 24 in the BOITCV

Luke 24 in the BOKCV

Luke 24 in the BOKCV2

Luke 24 in the BOKHWOG

Luke 24 in the BOKSSV

Luke 24 in the BOLCB

Luke 24 in the BOLCB2

Luke 24 in the BOMCV

Luke 24 in the BONAV

Luke 24 in the BONCB

Luke 24 in the BONLT

Luke 24 in the BONUT2

Luke 24 in the BOPLNT

Luke 24 in the BOSCB

Luke 24 in the BOSNC

Luke 24 in the BOTLNT

Luke 24 in the BOVCB

Luke 24 in the BOYCB

Luke 24 in the BPBB

Luke 24 in the BPH

Luke 24 in the BSB

Luke 24 in the CCB

Luke 24 in the CUV

Luke 24 in the CUVS

Luke 24 in the DBT

Luke 24 in the DGDNT

Luke 24 in the DHNT

Luke 24 in the DNT

Luke 24 in the ELBE

Luke 24 in the EMTV

Luke 24 in the ESV

Luke 24 in the FBV

Luke 24 in the FEB

Luke 24 in the GGMNT

Luke 24 in the GNT

Luke 24 in the HARY

Luke 24 in the HNT

Luke 24 in the IRVA

Luke 24 in the IRVB

Luke 24 in the IRVG

Luke 24 in the IRVH

Luke 24 in the IRVK

Luke 24 in the IRVM

Luke 24 in the IRVM2

Luke 24 in the IRVO

Luke 24 in the IRVP

Luke 24 in the IRVT

Luke 24 in the IRVT2

Luke 24 in the IRVU

Luke 24 in the ISVN

Luke 24 in the JSNT

Luke 24 in the KAPI

Luke 24 in the KBT1ETNIK

Luke 24 in the KBV

Luke 24 in the KJV

Luke 24 in the KNFD

Luke 24 in the LBA

Luke 24 in the LBLA

Luke 24 in the LNT

Luke 24 in the LSV

Luke 24 in the MAAL

Luke 24 in the MBV

Luke 24 in the MBV2

Luke 24 in the MHNT

Luke 24 in the MKNFD

Luke 24 in the MNG

Luke 24 in the MNT

Luke 24 in the MNT2

Luke 24 in the MRS1T

Luke 24 in the NAA

Luke 24 in the NASB

Luke 24 in the NBLA

Luke 24 in the NBS

Luke 24 in the NBVTP

Luke 24 in the NET2

Luke 24 in the NIV11

Luke 24 in the NNT

Luke 24 in the NNT2

Luke 24 in the NNT3

Luke 24 in the PDDPT

Luke 24 in the PFNT

Luke 24 in the RMNT

Luke 24 in the SBIAS

Luke 24 in the SBIBS

Luke 24 in the SBIBS2

Luke 24 in the SBICS

Luke 24 in the SBIDS

Luke 24 in the SBIGS

Luke 24 in the SBIHS

Luke 24 in the SBIIS

Luke 24 in the SBIIS2

Luke 24 in the SBIIS3

Luke 24 in the SBIKS

Luke 24 in the SBIKS2

Luke 24 in the SBIMS

Luke 24 in the SBIOS

Luke 24 in the SBIPS

Luke 24 in the SBISS

Luke 24 in the SBITS

Luke 24 in the SBITS2

Luke 24 in the SBITS3

Luke 24 in the SBITS4

Luke 24 in the SBIUS

Luke 24 in the SBIVS

Luke 24 in the SBT

Luke 24 in the SBT1E

Luke 24 in the SCHL

Luke 24 in the SNT

Luke 24 in the SUSU

Luke 24 in the SUSU2

Luke 24 in the SYNO

Luke 24 in the TBIAOTANT

Luke 24 in the TBT1E

Luke 24 in the TBT1E2

Luke 24 in the TFTIP

Luke 24 in the TFTU

Luke 24 in the TGNTATF3T

Luke 24 in the THAI

Luke 24 in the TNFD

Luke 24 in the TNT

Luke 24 in the TNTIK

Luke 24 in the TNTIL

Luke 24 in the TNTIN

Luke 24 in the TNTIP

Luke 24 in the TNTIZ

Luke 24 in the TOMA

Luke 24 in the TTENT

Luke 24 in the UBG

Luke 24 in the UGV

Luke 24 in the UGV2

Luke 24 in the UGV3

Luke 24 in the VBL

Luke 24 in the VDCC

Luke 24 in the YALU

Luke 24 in the YAPE

Luke 24 in the YBVTP

Luke 24 in the ZBP