Luke 8 (BOHCB)

1 Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi, 2 da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta. 3 Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari. 4 Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce, 5 “Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su. 6 Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin. 7 Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su. 8 Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.”Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.” 9 Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 10 Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’ 11 “Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah. 12 Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto. 13 Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya. 14 Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya. 15 Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.” 16 “Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske. 17 Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba. 18 Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.” 19 Sai uwar Yesu da ’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron. 20 Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.” 21 Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da ’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.” 22 Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. 23 Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari. 24 Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!”Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. 25 Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?”A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?” 26 Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili. 27 Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. 28 Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!” 29 Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa. 30 Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?”Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. 31 Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. 32 A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. 33 Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse. 34 Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. 35 Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. 36 Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun. 37 Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi. 38 Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce, 39 “Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin. 40 Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa. 41 Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa, 42 domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe. 43 A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya. 45 Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?”Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.” 46 Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.” 47 Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. 48 Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.” 49 Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.” 50 Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.” 51 Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. 52 Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.” 53 Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. 54 Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.” 55 Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. 56 Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.

In Other Versions

Luke 8 in the ANGEFD

Luke 8 in the ANTPNG2D

Luke 8 in the AS21

Luke 8 in the BAGH

Luke 8 in the BBPNG

Luke 8 in the BBT1E

Luke 8 in the BDS

Luke 8 in the BEV

Luke 8 in the BHAD

Luke 8 in the BIB

Luke 8 in the BLPT

Luke 8 in the BNT

Luke 8 in the BNTABOOT

Luke 8 in the BNTLV

Luke 8 in the BOATCB

Luke 8 in the BOATCB2

Luke 8 in the BOBCV

Luke 8 in the BOCNT

Luke 8 in the BOECS

Luke 8 in the BOGWICC

Luke 8 in the BOHCV

Luke 8 in the BOHLNT

Luke 8 in the BOHNTLTAL

Luke 8 in the BOICB

Luke 8 in the BOILNTAP

Luke 8 in the BOITCV

Luke 8 in the BOKCV

Luke 8 in the BOKCV2

Luke 8 in the BOKHWOG

Luke 8 in the BOKSSV

Luke 8 in the BOLCB

Luke 8 in the BOLCB2

Luke 8 in the BOMCV

Luke 8 in the BONAV

Luke 8 in the BONCB

Luke 8 in the BONLT

Luke 8 in the BONUT2

Luke 8 in the BOPLNT

Luke 8 in the BOSCB

Luke 8 in the BOSNC

Luke 8 in the BOTLNT

Luke 8 in the BOVCB

Luke 8 in the BOYCB

Luke 8 in the BPBB

Luke 8 in the BPH

Luke 8 in the BSB

Luke 8 in the CCB

Luke 8 in the CUV

Luke 8 in the CUVS

Luke 8 in the DBT

Luke 8 in the DGDNT

Luke 8 in the DHNT

Luke 8 in the DNT

Luke 8 in the ELBE

Luke 8 in the EMTV

Luke 8 in the ESV

Luke 8 in the FBV

Luke 8 in the FEB

Luke 8 in the GGMNT

Luke 8 in the GNT

Luke 8 in the HARY

Luke 8 in the HNT

Luke 8 in the IRVA

Luke 8 in the IRVB

Luke 8 in the IRVG

Luke 8 in the IRVH

Luke 8 in the IRVK

Luke 8 in the IRVM

Luke 8 in the IRVM2

Luke 8 in the IRVO

Luke 8 in the IRVP

Luke 8 in the IRVT

Luke 8 in the IRVT2

Luke 8 in the IRVU

Luke 8 in the ISVN

Luke 8 in the JSNT

Luke 8 in the KAPI

Luke 8 in the KBT1ETNIK

Luke 8 in the KBV

Luke 8 in the KJV

Luke 8 in the KNFD

Luke 8 in the LBA

Luke 8 in the LBLA

Luke 8 in the LNT

Luke 8 in the LSV

Luke 8 in the MAAL

Luke 8 in the MBV

Luke 8 in the MBV2

Luke 8 in the MHNT

Luke 8 in the MKNFD

Luke 8 in the MNG

Luke 8 in the MNT

Luke 8 in the MNT2

Luke 8 in the MRS1T

Luke 8 in the NAA

Luke 8 in the NASB

Luke 8 in the NBLA

Luke 8 in the NBS

Luke 8 in the NBVTP

Luke 8 in the NET2

Luke 8 in the NIV11

Luke 8 in the NNT

Luke 8 in the NNT2

Luke 8 in the NNT3

Luke 8 in the PDDPT

Luke 8 in the PFNT

Luke 8 in the RMNT

Luke 8 in the SBIAS

Luke 8 in the SBIBS

Luke 8 in the SBIBS2

Luke 8 in the SBICS

Luke 8 in the SBIDS

Luke 8 in the SBIGS

Luke 8 in the SBIHS

Luke 8 in the SBIIS

Luke 8 in the SBIIS2

Luke 8 in the SBIIS3

Luke 8 in the SBIKS

Luke 8 in the SBIKS2

Luke 8 in the SBIMS

Luke 8 in the SBIOS

Luke 8 in the SBIPS

Luke 8 in the SBISS

Luke 8 in the SBITS

Luke 8 in the SBITS2

Luke 8 in the SBITS3

Luke 8 in the SBITS4

Luke 8 in the SBIUS

Luke 8 in the SBIVS

Luke 8 in the SBT

Luke 8 in the SBT1E

Luke 8 in the SCHL

Luke 8 in the SNT

Luke 8 in the SUSU

Luke 8 in the SUSU2

Luke 8 in the SYNO

Luke 8 in the TBIAOTANT

Luke 8 in the TBT1E

Luke 8 in the TBT1E2

Luke 8 in the TFTIP

Luke 8 in the TFTU

Luke 8 in the TGNTATF3T

Luke 8 in the THAI

Luke 8 in the TNFD

Luke 8 in the TNT

Luke 8 in the TNTIK

Luke 8 in the TNTIL

Luke 8 in the TNTIN

Luke 8 in the TNTIP

Luke 8 in the TNTIZ

Luke 8 in the TOMA

Luke 8 in the TTENT

Luke 8 in the UBG

Luke 8 in the UGV

Luke 8 in the UGV2

Luke 8 in the UGV3

Luke 8 in the VBL

Luke 8 in the VDCC

Luke 8 in the YALU

Luke 8 in the YAPE

Luke 8 in the YBVTP

Luke 8 in the ZBP