Matthew 11 (BOHCB)
1 Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili. 2 Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa 3 su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 4 Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani. 5 Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi. 6 Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.” 7 Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 8 In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke. 9 To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi. 10 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’ 11 Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12 Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam. 13 Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna. 14 In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15 Duk mai kunnen ji, yă ji. 16 “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, 17 “ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’ 18 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19 Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.” 20 Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. 21 “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. 22 Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku. 23 Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau. 24 Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.” 25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26 I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi. 27 “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
In Other Versions
Matthew 11 in the ANGEFD
Matthew 11 in the ANTPNG2D
Matthew 11 in the AS21
Matthew 11 in the BAGH
Matthew 11 in the BBPNG
Matthew 11 in the BBT1E
Matthew 11 in the BDS
Matthew 11 in the BEV
Matthew 11 in the BHAD
Matthew 11 in the BIB
Matthew 11 in the BLPT
Matthew 11 in the BNT
Matthew 11 in the BNTABOOT
Matthew 11 in the BNTLV
Matthew 11 in the BOATCB
Matthew 11 in the BOATCB2
Matthew 11 in the BOBCV
Matthew 11 in the BOCNT
Matthew 11 in the BOECS
Matthew 11 in the BOGWICC
Matthew 11 in the BOHCV
Matthew 11 in the BOHLNT
Matthew 11 in the BOHNTLTAL
Matthew 11 in the BOICB
Matthew 11 in the BOILNTAP
Matthew 11 in the BOITCV
Matthew 11 in the BOKCV
Matthew 11 in the BOKCV2
Matthew 11 in the BOKHWOG
Matthew 11 in the BOKSSV
Matthew 11 in the BOLCB
Matthew 11 in the BOLCB2
Matthew 11 in the BOMCV
Matthew 11 in the BONAV
Matthew 11 in the BONCB
Matthew 11 in the BONLT
Matthew 11 in the BONUT2
Matthew 11 in the BOPLNT
Matthew 11 in the BOSCB
Matthew 11 in the BOSNC
Matthew 11 in the BOTLNT
Matthew 11 in the BOVCB
Matthew 11 in the BOYCB
Matthew 11 in the BPBB
Matthew 11 in the BPH
Matthew 11 in the BSB
Matthew 11 in the CCB
Matthew 11 in the CUV
Matthew 11 in the CUVS
Matthew 11 in the DBT
Matthew 11 in the DGDNT
Matthew 11 in the DHNT
Matthew 11 in the DNT
Matthew 11 in the ELBE
Matthew 11 in the EMTV
Matthew 11 in the ESV
Matthew 11 in the FBV
Matthew 11 in the FEB
Matthew 11 in the GGMNT
Matthew 11 in the GNT
Matthew 11 in the HARY
Matthew 11 in the HNT
Matthew 11 in the IRVA
Matthew 11 in the IRVB
Matthew 11 in the IRVG
Matthew 11 in the IRVH
Matthew 11 in the IRVK
Matthew 11 in the IRVM
Matthew 11 in the IRVM2
Matthew 11 in the IRVO
Matthew 11 in the IRVP
Matthew 11 in the IRVT
Matthew 11 in the IRVT2
Matthew 11 in the IRVU
Matthew 11 in the ISVN
Matthew 11 in the JSNT
Matthew 11 in the KAPI
Matthew 11 in the KBT1ETNIK
Matthew 11 in the KBV
Matthew 11 in the KJV
Matthew 11 in the KNFD
Matthew 11 in the LBA
Matthew 11 in the LBLA
Matthew 11 in the LNT
Matthew 11 in the LSV
Matthew 11 in the MAAL
Matthew 11 in the MBV
Matthew 11 in the MBV2
Matthew 11 in the MHNT
Matthew 11 in the MKNFD
Matthew 11 in the MNG
Matthew 11 in the MNT
Matthew 11 in the MNT2
Matthew 11 in the MRS1T
Matthew 11 in the NAA
Matthew 11 in the NASB
Matthew 11 in the NBLA
Matthew 11 in the NBS
Matthew 11 in the NBVTP
Matthew 11 in the NET2
Matthew 11 in the NIV11
Matthew 11 in the NNT
Matthew 11 in the NNT2
Matthew 11 in the NNT3
Matthew 11 in the PDDPT
Matthew 11 in the PFNT
Matthew 11 in the RMNT
Matthew 11 in the SBIAS
Matthew 11 in the SBIBS
Matthew 11 in the SBIBS2
Matthew 11 in the SBICS
Matthew 11 in the SBIDS
Matthew 11 in the SBIGS
Matthew 11 in the SBIHS
Matthew 11 in the SBIIS
Matthew 11 in the SBIIS2
Matthew 11 in the SBIIS3
Matthew 11 in the SBIKS
Matthew 11 in the SBIKS2
Matthew 11 in the SBIMS
Matthew 11 in the SBIOS
Matthew 11 in the SBIPS
Matthew 11 in the SBISS
Matthew 11 in the SBITS
Matthew 11 in the SBITS2
Matthew 11 in the SBITS3
Matthew 11 in the SBITS4
Matthew 11 in the SBIUS
Matthew 11 in the SBIVS
Matthew 11 in the SBT
Matthew 11 in the SBT1E
Matthew 11 in the SCHL
Matthew 11 in the SNT
Matthew 11 in the SUSU
Matthew 11 in the SUSU2
Matthew 11 in the SYNO
Matthew 11 in the TBIAOTANT
Matthew 11 in the TBT1E
Matthew 11 in the TBT1E2
Matthew 11 in the TFTIP
Matthew 11 in the TFTU
Matthew 11 in the TGNTATF3T
Matthew 11 in the THAI
Matthew 11 in the TNFD
Matthew 11 in the TNT
Matthew 11 in the TNTIK
Matthew 11 in the TNTIL
Matthew 11 in the TNTIN
Matthew 11 in the TNTIP
Matthew 11 in the TNTIZ
Matthew 11 in the TOMA
Matthew 11 in the TTENT
Matthew 11 in the UBG
Matthew 11 in the UGV
Matthew 11 in the UGV2
Matthew 11 in the UGV3
Matthew 11 in the VBL
Matthew 11 in the VDCC
Matthew 11 in the YALU
Matthew 11 in the YAPE
Matthew 11 in the YBVTP
Matthew 11 in the ZBP