Mark 11 (BOHCB)

1 Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa, 2 ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan. 3 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ” 4 Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan, 5 sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?” 6 Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su. 7 Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa. 8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. 9 Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa,“Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!” 10 “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!” 11 Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun. 12 Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. 13 Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. 14 Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka. 15 Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, 16 ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. 17 Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’” 18 Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa. 19 Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin. 20 Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. 21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!” 22 Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23 Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. 24 Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku. 25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.” 27 Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa. 28 Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?” 29 Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 30 Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!” 31 Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 32 In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.” 33 Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”

In Other Versions

Mark 11 in the ANGEFD

Mark 11 in the ANTPNG2D

Mark 11 in the AS21

Mark 11 in the BAGH

Mark 11 in the BBPNG

Mark 11 in the BBT1E

Mark 11 in the BDS

Mark 11 in the BEV

Mark 11 in the BHAD

Mark 11 in the BIB

Mark 11 in the BLPT

Mark 11 in the BNT

Mark 11 in the BNTABOOT

Mark 11 in the BNTLV

Mark 11 in the BOATCB

Mark 11 in the BOATCB2

Mark 11 in the BOBCV

Mark 11 in the BOCNT

Mark 11 in the BOECS

Mark 11 in the BOGWICC

Mark 11 in the BOHCV

Mark 11 in the BOHLNT

Mark 11 in the BOHNTLTAL

Mark 11 in the BOICB

Mark 11 in the BOILNTAP

Mark 11 in the BOITCV

Mark 11 in the BOKCV

Mark 11 in the BOKCV2

Mark 11 in the BOKHWOG

Mark 11 in the BOKSSV

Mark 11 in the BOLCB

Mark 11 in the BOLCB2

Mark 11 in the BOMCV

Mark 11 in the BONAV

Mark 11 in the BONCB

Mark 11 in the BONLT

Mark 11 in the BONUT2

Mark 11 in the BOPLNT

Mark 11 in the BOSCB

Mark 11 in the BOSNC

Mark 11 in the BOTLNT

Mark 11 in the BOVCB

Mark 11 in the BOYCB

Mark 11 in the BPBB

Mark 11 in the BPH

Mark 11 in the BSB

Mark 11 in the CCB

Mark 11 in the CUV

Mark 11 in the CUVS

Mark 11 in the DBT

Mark 11 in the DGDNT

Mark 11 in the DHNT

Mark 11 in the DNT

Mark 11 in the ELBE

Mark 11 in the EMTV

Mark 11 in the ESV

Mark 11 in the FBV

Mark 11 in the FEB

Mark 11 in the GGMNT

Mark 11 in the GNT

Mark 11 in the HARY

Mark 11 in the HNT

Mark 11 in the IRVA

Mark 11 in the IRVB

Mark 11 in the IRVG

Mark 11 in the IRVH

Mark 11 in the IRVK

Mark 11 in the IRVM

Mark 11 in the IRVM2

Mark 11 in the IRVO

Mark 11 in the IRVP

Mark 11 in the IRVT

Mark 11 in the IRVT2

Mark 11 in the IRVU

Mark 11 in the ISVN

Mark 11 in the JSNT

Mark 11 in the KAPI

Mark 11 in the KBT1ETNIK

Mark 11 in the KBV

Mark 11 in the KJV

Mark 11 in the KNFD

Mark 11 in the LBA

Mark 11 in the LBLA

Mark 11 in the LNT

Mark 11 in the LSV

Mark 11 in the MAAL

Mark 11 in the MBV

Mark 11 in the MBV2

Mark 11 in the MHNT

Mark 11 in the MKNFD

Mark 11 in the MNG

Mark 11 in the MNT

Mark 11 in the MNT2

Mark 11 in the MRS1T

Mark 11 in the NAA

Mark 11 in the NASB

Mark 11 in the NBLA

Mark 11 in the NBS

Mark 11 in the NBVTP

Mark 11 in the NET2

Mark 11 in the NIV11

Mark 11 in the NNT

Mark 11 in the NNT2

Mark 11 in the NNT3

Mark 11 in the PDDPT

Mark 11 in the PFNT

Mark 11 in the RMNT

Mark 11 in the SBIAS

Mark 11 in the SBIBS

Mark 11 in the SBIBS2

Mark 11 in the SBICS

Mark 11 in the SBIDS

Mark 11 in the SBIGS

Mark 11 in the SBIHS

Mark 11 in the SBIIS

Mark 11 in the SBIIS2

Mark 11 in the SBIIS3

Mark 11 in the SBIKS

Mark 11 in the SBIKS2

Mark 11 in the SBIMS

Mark 11 in the SBIOS

Mark 11 in the SBIPS

Mark 11 in the SBISS

Mark 11 in the SBITS

Mark 11 in the SBITS2

Mark 11 in the SBITS3

Mark 11 in the SBITS4

Mark 11 in the SBIUS

Mark 11 in the SBIVS

Mark 11 in the SBT

Mark 11 in the SBT1E

Mark 11 in the SCHL

Mark 11 in the SNT

Mark 11 in the SUSU

Mark 11 in the SUSU2

Mark 11 in the SYNO

Mark 11 in the TBIAOTANT

Mark 11 in the TBT1E

Mark 11 in the TBT1E2

Mark 11 in the TFTIP

Mark 11 in the TFTU

Mark 11 in the TGNTATF3T

Mark 11 in the THAI

Mark 11 in the TNFD

Mark 11 in the TNT

Mark 11 in the TNTIK

Mark 11 in the TNTIL

Mark 11 in the TNTIN

Mark 11 in the TNTIP

Mark 11 in the TNTIZ

Mark 11 in the TOMA

Mark 11 in the TTENT

Mark 11 in the UBG

Mark 11 in the UGV

Mark 11 in the UGV2

Mark 11 in the UGV3

Mark 11 in the VBL

Mark 11 in the VDCC

Mark 11 in the YALU

Mark 11 in the YAPE

Mark 11 in the YBVTP

Mark 11 in the ZBP