Mark 14 (BOHCB)
1 To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe. 2 Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.” 3 Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa. 4 Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? 5 Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.” 6 Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni. 7 Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. 8 Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata. 9 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.” 10 Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su. 11 Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi. 12 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?” 13 Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi. 14 Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’ 15 Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.” 16 Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa. 17 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. 18 Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.” 19 Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?” 20 Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano. 21 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.” 22 Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.” 23 Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki. 24 Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. 25 Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ” 26 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun. 27 Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’ 28 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.” 29 Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.” 30 Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.” 31 Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka. 32 Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.” 33 Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. 34 Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.” 35 Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a. 36 Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.” 37 Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya? 38 Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.” 39 Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi. 40 Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa. 41 Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi. 42 Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!” 43 Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron. 44 Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.” 45 Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. 46 Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi. 47 Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist. 48 Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? 49 Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.” 50 Sai kowa ya yashe shi ya gudu. 51 Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi, 52 sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara. 53 Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru. 54 Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta. 55 Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba. 56 Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba. 57 Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce, 58 “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ” 59 Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba. 60 Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?” 61 Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba.Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?” 62 Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.” 63 Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? 64 Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?”Duka suka yanke masa hukuncin kisa. 65 Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka. 66 Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can. 67 Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau.Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.” 68 Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure. 69 Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” 70 Sai ya sāke yin musu.Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.” 71 Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.” 72 Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.