Mark 2 (BOHCB)

1 Bayan ’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida. 2 Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara. 3 Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. 4 Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. 5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.” 6 To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, 7 “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” 8 Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? 9 Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? 10 Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, 11 “Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 12 Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!” 13 Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu. 14 Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi. 15 Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi. 16 Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 17 Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.” 18 To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?” 19 Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su. 20 Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi. 21 “Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni. 22 Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.” 23 Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi. 24 Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?” 25 Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata? 26 Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?” 27 Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba. 28 Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.”

In Other Versions

Mark 2 in the ANGEFD

Mark 2 in the ANTPNG2D

Mark 2 in the AS21

Mark 2 in the BAGH

Mark 2 in the BBPNG

Mark 2 in the BBT1E

Mark 2 in the BDS

Mark 2 in the BEV

Mark 2 in the BHAD

Mark 2 in the BIB

Mark 2 in the BLPT

Mark 2 in the BNT

Mark 2 in the BNTABOOT

Mark 2 in the BNTLV

Mark 2 in the BOATCB

Mark 2 in the BOATCB2

Mark 2 in the BOBCV

Mark 2 in the BOCNT

Mark 2 in the BOECS

Mark 2 in the BOGWICC

Mark 2 in the BOHCV

Mark 2 in the BOHLNT

Mark 2 in the BOHNTLTAL

Mark 2 in the BOICB

Mark 2 in the BOILNTAP

Mark 2 in the BOITCV

Mark 2 in the BOKCV

Mark 2 in the BOKCV2

Mark 2 in the BOKHWOG

Mark 2 in the BOKSSV

Mark 2 in the BOLCB

Mark 2 in the BOLCB2

Mark 2 in the BOMCV

Mark 2 in the BONAV

Mark 2 in the BONCB

Mark 2 in the BONLT

Mark 2 in the BONUT2

Mark 2 in the BOPLNT

Mark 2 in the BOSCB

Mark 2 in the BOSNC

Mark 2 in the BOTLNT

Mark 2 in the BOVCB

Mark 2 in the BOYCB

Mark 2 in the BPBB

Mark 2 in the BPH

Mark 2 in the BSB

Mark 2 in the CCB

Mark 2 in the CUV

Mark 2 in the CUVS

Mark 2 in the DBT

Mark 2 in the DGDNT

Mark 2 in the DHNT

Mark 2 in the DNT

Mark 2 in the ELBE

Mark 2 in the EMTV

Mark 2 in the ESV

Mark 2 in the FBV

Mark 2 in the FEB

Mark 2 in the GGMNT

Mark 2 in the GNT

Mark 2 in the HARY

Mark 2 in the HNT

Mark 2 in the IRVA

Mark 2 in the IRVB

Mark 2 in the IRVG

Mark 2 in the IRVH

Mark 2 in the IRVK

Mark 2 in the IRVM

Mark 2 in the IRVM2

Mark 2 in the IRVO

Mark 2 in the IRVP

Mark 2 in the IRVT

Mark 2 in the IRVT2

Mark 2 in the IRVU

Mark 2 in the ISVN

Mark 2 in the JSNT

Mark 2 in the KAPI

Mark 2 in the KBT1ETNIK

Mark 2 in the KBV

Mark 2 in the KJV

Mark 2 in the KNFD

Mark 2 in the LBA

Mark 2 in the LBLA

Mark 2 in the LNT

Mark 2 in the LSV

Mark 2 in the MAAL

Mark 2 in the MBV

Mark 2 in the MBV2

Mark 2 in the MHNT

Mark 2 in the MKNFD

Mark 2 in the MNG

Mark 2 in the MNT

Mark 2 in the MNT2

Mark 2 in the MRS1T

Mark 2 in the NAA

Mark 2 in the NASB

Mark 2 in the NBLA

Mark 2 in the NBS

Mark 2 in the NBVTP

Mark 2 in the NET2

Mark 2 in the NIV11

Mark 2 in the NNT

Mark 2 in the NNT2

Mark 2 in the NNT3

Mark 2 in the PDDPT

Mark 2 in the PFNT

Mark 2 in the RMNT

Mark 2 in the SBIAS

Mark 2 in the SBIBS

Mark 2 in the SBIBS2

Mark 2 in the SBICS

Mark 2 in the SBIDS

Mark 2 in the SBIGS

Mark 2 in the SBIHS

Mark 2 in the SBIIS

Mark 2 in the SBIIS2

Mark 2 in the SBIIS3

Mark 2 in the SBIKS

Mark 2 in the SBIKS2

Mark 2 in the SBIMS

Mark 2 in the SBIOS

Mark 2 in the SBIPS

Mark 2 in the SBISS

Mark 2 in the SBITS

Mark 2 in the SBITS2

Mark 2 in the SBITS3

Mark 2 in the SBITS4

Mark 2 in the SBIUS

Mark 2 in the SBIVS

Mark 2 in the SBT

Mark 2 in the SBT1E

Mark 2 in the SCHL

Mark 2 in the SNT

Mark 2 in the SUSU

Mark 2 in the SUSU2

Mark 2 in the SYNO

Mark 2 in the TBIAOTANT

Mark 2 in the TBT1E

Mark 2 in the TBT1E2

Mark 2 in the TFTIP

Mark 2 in the TFTU

Mark 2 in the TGNTATF3T

Mark 2 in the THAI

Mark 2 in the TNFD

Mark 2 in the TNT

Mark 2 in the TNTIK

Mark 2 in the TNTIL

Mark 2 in the TNTIN

Mark 2 in the TNTIP

Mark 2 in the TNTIZ

Mark 2 in the TOMA

Mark 2 in the TTENT

Mark 2 in the UBG

Mark 2 in the UGV

Mark 2 in the UGV2

Mark 2 in the UGV3

Mark 2 in the VBL

Mark 2 in the VDCC

Mark 2 in the YALU

Mark 2 in the YAPE

Mark 2 in the YBVTP

Mark 2 in the ZBP