Mark 7 (BOHCB)

1 Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. 2 Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba. 3 (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. 4 Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.) 5 Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?” 6 Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni. 7 A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’ 8 Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.” 9 Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! 10 Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’ 11 Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12 sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13 Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.” 14 Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15 Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.” 17 Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 18 Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. 19 Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.) 20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.” 24 Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. 25 Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. 26 Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta. 27 Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.” 28 Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.” 29 Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.” 30 Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita. 31 Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis. 32 A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin. 33 Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34 Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”). 35 Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai. 36 Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. 37 Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”

In Other Versions

Mark 7 in the ANGEFD

Mark 7 in the ANTPNG2D

Mark 7 in the AS21

Mark 7 in the BAGH

Mark 7 in the BBPNG

Mark 7 in the BBT1E

Mark 7 in the BDS

Mark 7 in the BEV

Mark 7 in the BHAD

Mark 7 in the BIB

Mark 7 in the BLPT

Mark 7 in the BNT

Mark 7 in the BNTABOOT

Mark 7 in the BNTLV

Mark 7 in the BOATCB

Mark 7 in the BOATCB2

Mark 7 in the BOBCV

Mark 7 in the BOCNT

Mark 7 in the BOECS

Mark 7 in the BOGWICC

Mark 7 in the BOHCV

Mark 7 in the BOHLNT

Mark 7 in the BOHNTLTAL

Mark 7 in the BOICB

Mark 7 in the BOILNTAP

Mark 7 in the BOITCV

Mark 7 in the BOKCV

Mark 7 in the BOKCV2

Mark 7 in the BOKHWOG

Mark 7 in the BOKSSV

Mark 7 in the BOLCB

Mark 7 in the BOLCB2

Mark 7 in the BOMCV

Mark 7 in the BONAV

Mark 7 in the BONCB

Mark 7 in the BONLT

Mark 7 in the BONUT2

Mark 7 in the BOPLNT

Mark 7 in the BOSCB

Mark 7 in the BOSNC

Mark 7 in the BOTLNT

Mark 7 in the BOVCB

Mark 7 in the BOYCB

Mark 7 in the BPBB

Mark 7 in the BPH

Mark 7 in the BSB

Mark 7 in the CCB

Mark 7 in the CUV

Mark 7 in the CUVS

Mark 7 in the DBT

Mark 7 in the DGDNT

Mark 7 in the DHNT

Mark 7 in the DNT

Mark 7 in the ELBE

Mark 7 in the EMTV

Mark 7 in the ESV

Mark 7 in the FBV

Mark 7 in the FEB

Mark 7 in the GGMNT

Mark 7 in the GNT

Mark 7 in the HARY

Mark 7 in the HNT

Mark 7 in the IRVA

Mark 7 in the IRVB

Mark 7 in the IRVG

Mark 7 in the IRVH

Mark 7 in the IRVK

Mark 7 in the IRVM

Mark 7 in the IRVM2

Mark 7 in the IRVO

Mark 7 in the IRVP

Mark 7 in the IRVT

Mark 7 in the IRVT2

Mark 7 in the IRVU

Mark 7 in the ISVN

Mark 7 in the JSNT

Mark 7 in the KAPI

Mark 7 in the KBT1ETNIK

Mark 7 in the KBV

Mark 7 in the KJV

Mark 7 in the KNFD

Mark 7 in the LBA

Mark 7 in the LBLA

Mark 7 in the LNT

Mark 7 in the LSV

Mark 7 in the MAAL

Mark 7 in the MBV

Mark 7 in the MBV2

Mark 7 in the MHNT

Mark 7 in the MKNFD

Mark 7 in the MNG

Mark 7 in the MNT

Mark 7 in the MNT2

Mark 7 in the MRS1T

Mark 7 in the NAA

Mark 7 in the NASB

Mark 7 in the NBLA

Mark 7 in the NBS

Mark 7 in the NBVTP

Mark 7 in the NET2

Mark 7 in the NIV11

Mark 7 in the NNT

Mark 7 in the NNT2

Mark 7 in the NNT3

Mark 7 in the PDDPT

Mark 7 in the PFNT

Mark 7 in the RMNT

Mark 7 in the SBIAS

Mark 7 in the SBIBS

Mark 7 in the SBIBS2

Mark 7 in the SBICS

Mark 7 in the SBIDS

Mark 7 in the SBIGS

Mark 7 in the SBIHS

Mark 7 in the SBIIS

Mark 7 in the SBIIS2

Mark 7 in the SBIIS3

Mark 7 in the SBIKS

Mark 7 in the SBIKS2

Mark 7 in the SBIMS

Mark 7 in the SBIOS

Mark 7 in the SBIPS

Mark 7 in the SBISS

Mark 7 in the SBITS

Mark 7 in the SBITS2

Mark 7 in the SBITS3

Mark 7 in the SBITS4

Mark 7 in the SBIUS

Mark 7 in the SBIVS

Mark 7 in the SBT

Mark 7 in the SBT1E

Mark 7 in the SCHL

Mark 7 in the SNT

Mark 7 in the SUSU

Mark 7 in the SUSU2

Mark 7 in the SYNO

Mark 7 in the TBIAOTANT

Mark 7 in the TBT1E

Mark 7 in the TBT1E2

Mark 7 in the TFTIP

Mark 7 in the TFTU

Mark 7 in the TGNTATF3T

Mark 7 in the THAI

Mark 7 in the TNFD

Mark 7 in the TNT

Mark 7 in the TNTIK

Mark 7 in the TNTIL

Mark 7 in the TNTIN

Mark 7 in the TNTIP

Mark 7 in the TNTIZ

Mark 7 in the TOMA

Mark 7 in the TTENT

Mark 7 in the UBG

Mark 7 in the UGV

Mark 7 in the UGV2

Mark 7 in the UGV3

Mark 7 in the VBL

Mark 7 in the VDCC

Mark 7 in the YALU

Mark 7 in the YAPE

Mark 7 in the YBVTP

Mark 7 in the ZBP