Philippians 3 (BOHCB)

1 A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne. 2 Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki. 3 Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba, 4 ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka.In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi, 5 an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne; 6 wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne. 7 Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. 8 Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi 9 a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya. 10 Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa, 11 yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu. 12 Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi. 13 ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, 14 ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu. 15 Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma. 16 Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka. 17 Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙa’idar da muka ba ku. 18 Gama kamar yadda na sha gaya muku yanzu kuma ina sāke gaya muku har ma da hawaye, waɗansu da yawa suna rayuwa kamar abokan gāban gicciyen Kiristi. 19 Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya. 20 Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, 21 shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

In Other Versions

Philippians 3 in the ANGEFD

Philippians 3 in the ANTPNG2D

Philippians 3 in the AS21

Philippians 3 in the BAGH

Philippians 3 in the BBPNG

Philippians 3 in the BBT1E

Philippians 3 in the BDS

Philippians 3 in the BEV

Philippians 3 in the BHAD

Philippians 3 in the BIB

Philippians 3 in the BLPT

Philippians 3 in the BNT

Philippians 3 in the BNTABOOT

Philippians 3 in the BNTLV

Philippians 3 in the BOATCB

Philippians 3 in the BOATCB2

Philippians 3 in the BOBCV

Philippians 3 in the BOCNT

Philippians 3 in the BOECS

Philippians 3 in the BOGWICC

Philippians 3 in the BOHCV

Philippians 3 in the BOHLNT

Philippians 3 in the BOHNTLTAL

Philippians 3 in the BOICB

Philippians 3 in the BOILNTAP

Philippians 3 in the BOITCV

Philippians 3 in the BOKCV

Philippians 3 in the BOKCV2

Philippians 3 in the BOKHWOG

Philippians 3 in the BOKSSV

Philippians 3 in the BOLCB

Philippians 3 in the BOLCB2

Philippians 3 in the BOMCV

Philippians 3 in the BONAV

Philippians 3 in the BONCB

Philippians 3 in the BONLT

Philippians 3 in the BONUT2

Philippians 3 in the BOPLNT

Philippians 3 in the BOSCB

Philippians 3 in the BOSNC

Philippians 3 in the BOTLNT

Philippians 3 in the BOVCB

Philippians 3 in the BOYCB

Philippians 3 in the BPBB

Philippians 3 in the BPH

Philippians 3 in the BSB

Philippians 3 in the CCB

Philippians 3 in the CUV

Philippians 3 in the CUVS

Philippians 3 in the DBT

Philippians 3 in the DGDNT

Philippians 3 in the DHNT

Philippians 3 in the DNT

Philippians 3 in the ELBE

Philippians 3 in the EMTV

Philippians 3 in the ESV

Philippians 3 in the FBV

Philippians 3 in the FEB

Philippians 3 in the GGMNT

Philippians 3 in the GNT

Philippians 3 in the HARY

Philippians 3 in the HNT

Philippians 3 in the IRVA

Philippians 3 in the IRVB

Philippians 3 in the IRVG

Philippians 3 in the IRVH

Philippians 3 in the IRVK

Philippians 3 in the IRVM

Philippians 3 in the IRVM2

Philippians 3 in the IRVO

Philippians 3 in the IRVP

Philippians 3 in the IRVT

Philippians 3 in the IRVT2

Philippians 3 in the IRVU

Philippians 3 in the ISVN

Philippians 3 in the JSNT

Philippians 3 in the KAPI

Philippians 3 in the KBT1ETNIK

Philippians 3 in the KBV

Philippians 3 in the KJV

Philippians 3 in the KNFD

Philippians 3 in the LBA

Philippians 3 in the LBLA

Philippians 3 in the LNT

Philippians 3 in the LSV

Philippians 3 in the MAAL

Philippians 3 in the MBV

Philippians 3 in the MBV2

Philippians 3 in the MHNT

Philippians 3 in the MKNFD

Philippians 3 in the MNG

Philippians 3 in the MNT

Philippians 3 in the MNT2

Philippians 3 in the MRS1T

Philippians 3 in the NAA

Philippians 3 in the NASB

Philippians 3 in the NBLA

Philippians 3 in the NBS

Philippians 3 in the NBVTP

Philippians 3 in the NET2

Philippians 3 in the NIV11

Philippians 3 in the NNT

Philippians 3 in the NNT2

Philippians 3 in the NNT3

Philippians 3 in the PDDPT

Philippians 3 in the PFNT

Philippians 3 in the RMNT

Philippians 3 in the SBIAS

Philippians 3 in the SBIBS

Philippians 3 in the SBIBS2

Philippians 3 in the SBICS

Philippians 3 in the SBIDS

Philippians 3 in the SBIGS

Philippians 3 in the SBIHS

Philippians 3 in the SBIIS

Philippians 3 in the SBIIS2

Philippians 3 in the SBIIS3

Philippians 3 in the SBIKS

Philippians 3 in the SBIKS2

Philippians 3 in the SBIMS

Philippians 3 in the SBIOS

Philippians 3 in the SBIPS

Philippians 3 in the SBISS

Philippians 3 in the SBITS

Philippians 3 in the SBITS2

Philippians 3 in the SBITS3

Philippians 3 in the SBITS4

Philippians 3 in the SBIUS

Philippians 3 in the SBIVS

Philippians 3 in the SBT

Philippians 3 in the SBT1E

Philippians 3 in the SCHL

Philippians 3 in the SNT

Philippians 3 in the SUSU

Philippians 3 in the SUSU2

Philippians 3 in the SYNO

Philippians 3 in the TBIAOTANT

Philippians 3 in the TBT1E

Philippians 3 in the TBT1E2

Philippians 3 in the TFTIP

Philippians 3 in the TFTU

Philippians 3 in the TGNTATF3T

Philippians 3 in the THAI

Philippians 3 in the TNFD

Philippians 3 in the TNT

Philippians 3 in the TNTIK

Philippians 3 in the TNTIL

Philippians 3 in the TNTIN

Philippians 3 in the TNTIP

Philippians 3 in the TNTIZ

Philippians 3 in the TOMA

Philippians 3 in the TTENT

Philippians 3 in the UBG

Philippians 3 in the UGV

Philippians 3 in the UGV2

Philippians 3 in the UGV3

Philippians 3 in the VBL

Philippians 3 in the VDCC

Philippians 3 in the YALU

Philippians 3 in the YAPE

Philippians 3 in the YBVTP

Philippians 3 in the ZBP