Revelation 22 (BOHCB)
1 Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon, 2 yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne. 3 Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. 4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. 5 Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin. 6 Mala’ikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki mala’ikansa, don yă nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.” 7 “Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.” 8 Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. 9 Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!” 10 Sa’an nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa. 11 Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.” 12 “Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi. 13 Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe. 14 “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi. 15 Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta. 16 “Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.” 17 Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta. 18 Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan. 19 Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan. 20 Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.”Amin. Zo, Ubangiji Yesu! 21 Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.
In Other Versions
Revelation 22 in the ANGEFD
Revelation 22 in the ANTPNG2D
Revelation 22 in the AS21
Revelation 22 in the BAGH
Revelation 22 in the BBPNG
Revelation 22 in the BBT1E
Revelation 22 in the BDS
Revelation 22 in the BEV
Revelation 22 in the BHAD
Revelation 22 in the BIB
Revelation 22 in the BLPT
Revelation 22 in the BNT
Revelation 22 in the BNTABOOT
Revelation 22 in the BNTLV
Revelation 22 in the BOATCB
Revelation 22 in the BOATCB2
Revelation 22 in the BOBCV
Revelation 22 in the BOCNT
Revelation 22 in the BOECS
Revelation 22 in the BOGWICC
Revelation 22 in the BOHCV
Revelation 22 in the BOHLNT
Revelation 22 in the BOHNTLTAL
Revelation 22 in the BOICB
Revelation 22 in the BOILNTAP
Revelation 22 in the BOITCV
Revelation 22 in the BOKCV
Revelation 22 in the BOKCV2
Revelation 22 in the BOKHWOG
Revelation 22 in the BOKSSV
Revelation 22 in the BOLCB
Revelation 22 in the BOLCB2
Revelation 22 in the BOMCV
Revelation 22 in the BONAV
Revelation 22 in the BONCB
Revelation 22 in the BONLT
Revelation 22 in the BONUT2
Revelation 22 in the BOPLNT
Revelation 22 in the BOSCB
Revelation 22 in the BOSNC
Revelation 22 in the BOTLNT
Revelation 22 in the BOVCB
Revelation 22 in the BOYCB
Revelation 22 in the BPBB
Revelation 22 in the BPH
Revelation 22 in the BSB
Revelation 22 in the CCB
Revelation 22 in the CUV
Revelation 22 in the CUVS
Revelation 22 in the DBT
Revelation 22 in the DGDNT
Revelation 22 in the DHNT
Revelation 22 in the DNT
Revelation 22 in the ELBE
Revelation 22 in the EMTV
Revelation 22 in the ESV
Revelation 22 in the FBV
Revelation 22 in the FEB
Revelation 22 in the GGMNT
Revelation 22 in the GNT
Revelation 22 in the HARY
Revelation 22 in the HNT
Revelation 22 in the IRVA
Revelation 22 in the IRVB
Revelation 22 in the IRVG
Revelation 22 in the IRVH
Revelation 22 in the IRVK
Revelation 22 in the IRVM
Revelation 22 in the IRVM2
Revelation 22 in the IRVO
Revelation 22 in the IRVP
Revelation 22 in the IRVT
Revelation 22 in the IRVT2
Revelation 22 in the IRVU
Revelation 22 in the ISVN
Revelation 22 in the JSNT
Revelation 22 in the KAPI
Revelation 22 in the KBT1ETNIK
Revelation 22 in the KBV
Revelation 22 in the KJV
Revelation 22 in the KNFD
Revelation 22 in the LBA
Revelation 22 in the LBLA
Revelation 22 in the LNT
Revelation 22 in the LSV
Revelation 22 in the MAAL
Revelation 22 in the MBV
Revelation 22 in the MBV2
Revelation 22 in the MHNT
Revelation 22 in the MKNFD
Revelation 22 in the MNG
Revelation 22 in the MNT
Revelation 22 in the MNT2
Revelation 22 in the MRS1T
Revelation 22 in the NAA
Revelation 22 in the NASB
Revelation 22 in the NBLA
Revelation 22 in the NBS
Revelation 22 in the NBVTP
Revelation 22 in the NET2
Revelation 22 in the NIV11
Revelation 22 in the NNT
Revelation 22 in the NNT2
Revelation 22 in the NNT3
Revelation 22 in the PDDPT
Revelation 22 in the PFNT
Revelation 22 in the RMNT
Revelation 22 in the SBIAS
Revelation 22 in the SBIBS
Revelation 22 in the SBIBS2
Revelation 22 in the SBICS
Revelation 22 in the SBIDS
Revelation 22 in the SBIGS
Revelation 22 in the SBIHS
Revelation 22 in the SBIIS
Revelation 22 in the SBIIS2
Revelation 22 in the SBIIS3
Revelation 22 in the SBIKS
Revelation 22 in the SBIKS2
Revelation 22 in the SBIMS
Revelation 22 in the SBIOS
Revelation 22 in the SBIPS
Revelation 22 in the SBISS
Revelation 22 in the SBITS
Revelation 22 in the SBITS2
Revelation 22 in the SBITS3
Revelation 22 in the SBITS4
Revelation 22 in the SBIUS
Revelation 22 in the SBIVS
Revelation 22 in the SBT
Revelation 22 in the SBT1E
Revelation 22 in the SCHL
Revelation 22 in the SNT
Revelation 22 in the SUSU
Revelation 22 in the SUSU2
Revelation 22 in the SYNO
Revelation 22 in the TBIAOTANT
Revelation 22 in the TBT1E
Revelation 22 in the TBT1E2
Revelation 22 in the TFTIP
Revelation 22 in the TFTU
Revelation 22 in the TGNTATF3T
Revelation 22 in the THAI
Revelation 22 in the TNFD
Revelation 22 in the TNT
Revelation 22 in the TNTIK
Revelation 22 in the TNTIL
Revelation 22 in the TNTIN
Revelation 22 in the TNTIP
Revelation 22 in the TNTIZ
Revelation 22 in the TOMA
Revelation 22 in the TTENT
Revelation 22 in the UBG
Revelation 22 in the UGV
Revelation 22 in the UGV2
Revelation 22 in the UGV3
Revelation 22 in the VBL
Revelation 22 in the VDCC
Revelation 22 in the YALU
Revelation 22 in the YAPE
Revelation 22 in the YBVTP
Revelation 22 in the ZBP