Revelation 6 (BOHCB)
1 Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” 2 Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara. 3 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” 4 Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi. 5 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. 6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!” 7 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” 8 Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya. 9 Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. 10 Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” 11 Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su. 12 Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, 13 taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. 14 Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa. 15 Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. 16 Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! 17 Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”
In Other Versions
Revelation 6 in the ANGEFD
Revelation 6 in the ANTPNG2D
Revelation 6 in the AS21
Revelation 6 in the BAGH
Revelation 6 in the BBPNG
Revelation 6 in the BBT1E
Revelation 6 in the BDS
Revelation 6 in the BEV
Revelation 6 in the BHAD
Revelation 6 in the BIB
Revelation 6 in the BLPT
Revelation 6 in the BNT
Revelation 6 in the BNTABOOT
Revelation 6 in the BNTLV
Revelation 6 in the BOATCB
Revelation 6 in the BOATCB2
Revelation 6 in the BOBCV
Revelation 6 in the BOCNT
Revelation 6 in the BOECS
Revelation 6 in the BOGWICC
Revelation 6 in the BOHCV
Revelation 6 in the BOHLNT
Revelation 6 in the BOHNTLTAL
Revelation 6 in the BOICB
Revelation 6 in the BOILNTAP
Revelation 6 in the BOITCV
Revelation 6 in the BOKCV
Revelation 6 in the BOKCV2
Revelation 6 in the BOKHWOG
Revelation 6 in the BOKSSV
Revelation 6 in the BOLCB
Revelation 6 in the BOLCB2
Revelation 6 in the BOMCV
Revelation 6 in the BONAV
Revelation 6 in the BONCB
Revelation 6 in the BONLT
Revelation 6 in the BONUT2
Revelation 6 in the BOPLNT
Revelation 6 in the BOSCB
Revelation 6 in the BOSNC
Revelation 6 in the BOTLNT
Revelation 6 in the BOVCB
Revelation 6 in the BOYCB
Revelation 6 in the BPBB
Revelation 6 in the BPH
Revelation 6 in the BSB
Revelation 6 in the CCB
Revelation 6 in the CUV
Revelation 6 in the CUVS
Revelation 6 in the DBT
Revelation 6 in the DGDNT
Revelation 6 in the DHNT
Revelation 6 in the DNT
Revelation 6 in the ELBE
Revelation 6 in the EMTV
Revelation 6 in the ESV
Revelation 6 in the FBV
Revelation 6 in the FEB
Revelation 6 in the GGMNT
Revelation 6 in the GNT
Revelation 6 in the HARY
Revelation 6 in the HNT
Revelation 6 in the IRVA
Revelation 6 in the IRVB
Revelation 6 in the IRVG
Revelation 6 in the IRVH
Revelation 6 in the IRVK
Revelation 6 in the IRVM
Revelation 6 in the IRVM2
Revelation 6 in the IRVO
Revelation 6 in the IRVP
Revelation 6 in the IRVT
Revelation 6 in the IRVT2
Revelation 6 in the IRVU
Revelation 6 in the ISVN
Revelation 6 in the JSNT
Revelation 6 in the KAPI
Revelation 6 in the KBT1ETNIK
Revelation 6 in the KBV
Revelation 6 in the KJV
Revelation 6 in the KNFD
Revelation 6 in the LBA
Revelation 6 in the LBLA
Revelation 6 in the LNT
Revelation 6 in the LSV
Revelation 6 in the MAAL
Revelation 6 in the MBV
Revelation 6 in the MBV2
Revelation 6 in the MHNT
Revelation 6 in the MKNFD
Revelation 6 in the MNG
Revelation 6 in the MNT
Revelation 6 in the MNT2
Revelation 6 in the MRS1T
Revelation 6 in the NAA
Revelation 6 in the NASB
Revelation 6 in the NBLA
Revelation 6 in the NBS
Revelation 6 in the NBVTP
Revelation 6 in the NET2
Revelation 6 in the NIV11
Revelation 6 in the NNT
Revelation 6 in the NNT2
Revelation 6 in the NNT3
Revelation 6 in the PDDPT
Revelation 6 in the PFNT
Revelation 6 in the RMNT
Revelation 6 in the SBIAS
Revelation 6 in the SBIBS
Revelation 6 in the SBIBS2
Revelation 6 in the SBICS
Revelation 6 in the SBIDS
Revelation 6 in the SBIGS
Revelation 6 in the SBIHS
Revelation 6 in the SBIIS
Revelation 6 in the SBIIS2
Revelation 6 in the SBIIS3
Revelation 6 in the SBIKS
Revelation 6 in the SBIKS2
Revelation 6 in the SBIMS
Revelation 6 in the SBIOS
Revelation 6 in the SBIPS
Revelation 6 in the SBISS
Revelation 6 in the SBITS
Revelation 6 in the SBITS2
Revelation 6 in the SBITS3
Revelation 6 in the SBITS4
Revelation 6 in the SBIUS
Revelation 6 in the SBIVS
Revelation 6 in the SBT
Revelation 6 in the SBT1E
Revelation 6 in the SCHL
Revelation 6 in the SNT
Revelation 6 in the SUSU
Revelation 6 in the SUSU2
Revelation 6 in the SYNO
Revelation 6 in the TBIAOTANT
Revelation 6 in the TBT1E
Revelation 6 in the TBT1E2
Revelation 6 in the TFTIP
Revelation 6 in the TFTU
Revelation 6 in the TGNTATF3T
Revelation 6 in the THAI
Revelation 6 in the TNFD
Revelation 6 in the TNT
Revelation 6 in the TNTIK
Revelation 6 in the TNTIL
Revelation 6 in the TNTIN
Revelation 6 in the TNTIP
Revelation 6 in the TNTIZ
Revelation 6 in the TOMA
Revelation 6 in the TTENT
Revelation 6 in the UBG
Revelation 6 in the UGV
Revelation 6 in the UGV2
Revelation 6 in the UGV3
Revelation 6 in the VBL
Revelation 6 in the VDCC
Revelation 6 in the YALU
Revelation 6 in the YAPE
Revelation 6 in the YBVTP
Revelation 6 in the ZBP