Revelation 8 (BOHCB)

1 Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin sa’a. 2 Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai. 3 Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. 4 Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan. 5 Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa. 6 Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su. 7 Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone. 8 Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini, 9 kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka. 10 Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa 11 sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa. 12 Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare. 13 Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!”

In Other Versions

Revelation 8 in the ANGEFD

Revelation 8 in the ANTPNG2D

Revelation 8 in the AS21

Revelation 8 in the BAGH

Revelation 8 in the BBPNG

Revelation 8 in the BBT1E

Revelation 8 in the BDS

Revelation 8 in the BEV

Revelation 8 in the BHAD

Revelation 8 in the BIB

Revelation 8 in the BLPT

Revelation 8 in the BNT

Revelation 8 in the BNTABOOT

Revelation 8 in the BNTLV

Revelation 8 in the BOATCB

Revelation 8 in the BOATCB2

Revelation 8 in the BOBCV

Revelation 8 in the BOCNT

Revelation 8 in the BOECS

Revelation 8 in the BOGWICC

Revelation 8 in the BOHCV

Revelation 8 in the BOHLNT

Revelation 8 in the BOHNTLTAL

Revelation 8 in the BOICB

Revelation 8 in the BOILNTAP

Revelation 8 in the BOITCV

Revelation 8 in the BOKCV

Revelation 8 in the BOKCV2

Revelation 8 in the BOKHWOG

Revelation 8 in the BOKSSV

Revelation 8 in the BOLCB

Revelation 8 in the BOLCB2

Revelation 8 in the BOMCV

Revelation 8 in the BONAV

Revelation 8 in the BONCB

Revelation 8 in the BONLT

Revelation 8 in the BONUT2

Revelation 8 in the BOPLNT

Revelation 8 in the BOSCB

Revelation 8 in the BOSNC

Revelation 8 in the BOTLNT

Revelation 8 in the BOVCB

Revelation 8 in the BOYCB

Revelation 8 in the BPBB

Revelation 8 in the BPH

Revelation 8 in the BSB

Revelation 8 in the CCB

Revelation 8 in the CUV

Revelation 8 in the CUVS

Revelation 8 in the DBT

Revelation 8 in the DGDNT

Revelation 8 in the DHNT

Revelation 8 in the DNT

Revelation 8 in the ELBE

Revelation 8 in the EMTV

Revelation 8 in the ESV

Revelation 8 in the FBV

Revelation 8 in the FEB

Revelation 8 in the GGMNT

Revelation 8 in the GNT

Revelation 8 in the HARY

Revelation 8 in the HNT

Revelation 8 in the IRVA

Revelation 8 in the IRVB

Revelation 8 in the IRVG

Revelation 8 in the IRVH

Revelation 8 in the IRVK

Revelation 8 in the IRVM

Revelation 8 in the IRVM2

Revelation 8 in the IRVO

Revelation 8 in the IRVP

Revelation 8 in the IRVT

Revelation 8 in the IRVT2

Revelation 8 in the IRVU

Revelation 8 in the ISVN

Revelation 8 in the JSNT

Revelation 8 in the KAPI

Revelation 8 in the KBT1ETNIK

Revelation 8 in the KBV

Revelation 8 in the KJV

Revelation 8 in the KNFD

Revelation 8 in the LBA

Revelation 8 in the LBLA

Revelation 8 in the LNT

Revelation 8 in the LSV

Revelation 8 in the MAAL

Revelation 8 in the MBV

Revelation 8 in the MBV2

Revelation 8 in the MHNT

Revelation 8 in the MKNFD

Revelation 8 in the MNG

Revelation 8 in the MNT

Revelation 8 in the MNT2

Revelation 8 in the MRS1T

Revelation 8 in the NAA

Revelation 8 in the NASB

Revelation 8 in the NBLA

Revelation 8 in the NBS

Revelation 8 in the NBVTP

Revelation 8 in the NET2

Revelation 8 in the NIV11

Revelation 8 in the NNT

Revelation 8 in the NNT2

Revelation 8 in the NNT3

Revelation 8 in the PDDPT

Revelation 8 in the PFNT

Revelation 8 in the RMNT

Revelation 8 in the SBIAS

Revelation 8 in the SBIBS

Revelation 8 in the SBIBS2

Revelation 8 in the SBICS

Revelation 8 in the SBIDS

Revelation 8 in the SBIGS

Revelation 8 in the SBIHS

Revelation 8 in the SBIIS

Revelation 8 in the SBIIS2

Revelation 8 in the SBIIS3

Revelation 8 in the SBIKS

Revelation 8 in the SBIKS2

Revelation 8 in the SBIMS

Revelation 8 in the SBIOS

Revelation 8 in the SBIPS

Revelation 8 in the SBISS

Revelation 8 in the SBITS

Revelation 8 in the SBITS2

Revelation 8 in the SBITS3

Revelation 8 in the SBITS4

Revelation 8 in the SBIUS

Revelation 8 in the SBIVS

Revelation 8 in the SBT

Revelation 8 in the SBT1E

Revelation 8 in the SCHL

Revelation 8 in the SNT

Revelation 8 in the SUSU

Revelation 8 in the SUSU2

Revelation 8 in the SYNO

Revelation 8 in the TBIAOTANT

Revelation 8 in the TBT1E

Revelation 8 in the TBT1E2

Revelation 8 in the TFTIP

Revelation 8 in the TFTU

Revelation 8 in the TGNTATF3T

Revelation 8 in the THAI

Revelation 8 in the TNFD

Revelation 8 in the TNT

Revelation 8 in the TNTIK

Revelation 8 in the TNTIL

Revelation 8 in the TNTIN

Revelation 8 in the TNTIP

Revelation 8 in the TNTIZ

Revelation 8 in the TOMA

Revelation 8 in the TTENT

Revelation 8 in the UBG

Revelation 8 in the UGV

Revelation 8 in the UGV2

Revelation 8 in the UGV3

Revelation 8 in the VBL

Revelation 8 in the VDCC

Revelation 8 in the YALU

Revelation 8 in the YAPE

Revelation 8 in the YBVTP

Revelation 8 in the ZBP