Romans 3 (BOHCB)

1 To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya? 2 Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah. 3 Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? 4 Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana,ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.” 5 Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.) 6 Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shari’anta duniya? 7 Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?” 8 In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su. 9 To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. 10 Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya; 11 babu wani mai fahimta,babu wani mai neman Allah. 12 Duk sun kauce gaba ɗaya,sun zama marasa amfani;babu wani mai aikata nagarta,babu ko ɗaya.” 13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,harsunansu suna yin ƙarya.”“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.” 14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.” 15 “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini; 16 hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu, 17 ba su kuma san hanyar salama ba.” 18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.” 19 Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah. 20 Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi. 21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu. 27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya. 28 Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba. 29 Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma, 30 da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin. 31 To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.

In Other Versions

Romans 3 in the ANGEFD

Romans 3 in the ANTPNG2D

Romans 3 in the AS21

Romans 3 in the BAGH

Romans 3 in the BBPNG

Romans 3 in the BBT1E

Romans 3 in the BDS

Romans 3 in the BEV

Romans 3 in the BHAD

Romans 3 in the BIB

Romans 3 in the BLPT

Romans 3 in the BNT

Romans 3 in the BNTABOOT

Romans 3 in the BNTLV

Romans 3 in the BOATCB

Romans 3 in the BOATCB2

Romans 3 in the BOBCV

Romans 3 in the BOCNT

Romans 3 in the BOECS

Romans 3 in the BOGWICC

Romans 3 in the BOHCV

Romans 3 in the BOHLNT

Romans 3 in the BOHNTLTAL

Romans 3 in the BOICB

Romans 3 in the BOILNTAP

Romans 3 in the BOITCV

Romans 3 in the BOKCV

Romans 3 in the BOKCV2

Romans 3 in the BOKHWOG

Romans 3 in the BOKSSV

Romans 3 in the BOLCB

Romans 3 in the BOLCB2

Romans 3 in the BOMCV

Romans 3 in the BONAV

Romans 3 in the BONCB

Romans 3 in the BONLT

Romans 3 in the BONUT2

Romans 3 in the BOPLNT

Romans 3 in the BOSCB

Romans 3 in the BOSNC

Romans 3 in the BOTLNT

Romans 3 in the BOVCB

Romans 3 in the BOYCB

Romans 3 in the BPBB

Romans 3 in the BPH

Romans 3 in the BSB

Romans 3 in the CCB

Romans 3 in the CUV

Romans 3 in the CUVS

Romans 3 in the DBT

Romans 3 in the DGDNT

Romans 3 in the DHNT

Romans 3 in the DNT

Romans 3 in the ELBE

Romans 3 in the EMTV

Romans 3 in the ESV

Romans 3 in the FBV

Romans 3 in the FEB

Romans 3 in the GGMNT

Romans 3 in the GNT

Romans 3 in the HARY

Romans 3 in the HNT

Romans 3 in the IRVA

Romans 3 in the IRVB

Romans 3 in the IRVG

Romans 3 in the IRVH

Romans 3 in the IRVK

Romans 3 in the IRVM

Romans 3 in the IRVM2

Romans 3 in the IRVO

Romans 3 in the IRVP

Romans 3 in the IRVT

Romans 3 in the IRVT2

Romans 3 in the IRVU

Romans 3 in the ISVN

Romans 3 in the JSNT

Romans 3 in the KAPI

Romans 3 in the KBT1ETNIK

Romans 3 in the KBV

Romans 3 in the KJV

Romans 3 in the KNFD

Romans 3 in the LBA

Romans 3 in the LBLA

Romans 3 in the LNT

Romans 3 in the LSV

Romans 3 in the MAAL

Romans 3 in the MBV

Romans 3 in the MBV2

Romans 3 in the MHNT

Romans 3 in the MKNFD

Romans 3 in the MNG

Romans 3 in the MNT

Romans 3 in the MNT2

Romans 3 in the MRS1T

Romans 3 in the NAA

Romans 3 in the NASB

Romans 3 in the NBLA

Romans 3 in the NBS

Romans 3 in the NBVTP

Romans 3 in the NET2

Romans 3 in the NIV11

Romans 3 in the NNT

Romans 3 in the NNT2

Romans 3 in the NNT3

Romans 3 in the PDDPT

Romans 3 in the PFNT

Romans 3 in the RMNT

Romans 3 in the SBIAS

Romans 3 in the SBIBS

Romans 3 in the SBIBS2

Romans 3 in the SBICS

Romans 3 in the SBIDS

Romans 3 in the SBIGS

Romans 3 in the SBIHS

Romans 3 in the SBIIS

Romans 3 in the SBIIS2

Romans 3 in the SBIIS3

Romans 3 in the SBIKS

Romans 3 in the SBIKS2

Romans 3 in the SBIMS

Romans 3 in the SBIOS

Romans 3 in the SBIPS

Romans 3 in the SBISS

Romans 3 in the SBITS

Romans 3 in the SBITS2

Romans 3 in the SBITS3

Romans 3 in the SBITS4

Romans 3 in the SBIUS

Romans 3 in the SBIVS

Romans 3 in the SBT

Romans 3 in the SBT1E

Romans 3 in the SCHL

Romans 3 in the SNT

Romans 3 in the SUSU

Romans 3 in the SUSU2

Romans 3 in the SYNO

Romans 3 in the TBIAOTANT

Romans 3 in the TBT1E

Romans 3 in the TBT1E2

Romans 3 in the TFTIP

Romans 3 in the TFTU

Romans 3 in the TGNTATF3T

Romans 3 in the THAI

Romans 3 in the TNFD

Romans 3 in the TNT

Romans 3 in the TNTIK

Romans 3 in the TNTIL

Romans 3 in the TNTIN

Romans 3 in the TNTIP

Romans 3 in the TNTIZ

Romans 3 in the TOMA

Romans 3 in the TTENT

Romans 3 in the UBG

Romans 3 in the UGV

Romans 3 in the UGV2

Romans 3 in the UGV3

Romans 3 in the VBL

Romans 3 in the VDCC

Romans 3 in the YALU

Romans 3 in the YAPE

Romans 3 in the YBVTP

Romans 3 in the ZBP