Romans 5 (BOHCB)
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu. 6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu. 9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! 10 Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! 11 Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu. 12 Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi. 13 Gama kafin a ba da doka, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a lissafin zunubi inda babu doka. 14 Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa. 15 Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa! 16 Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne, Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi. 17 Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi. 18 Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane. 19 Gama kamar yadda ta wurin rashin biyayyar mutum guda, mutane masu yawa suka zama masu zunubi, haka kuma ta wurin biyayyar mutum guda, mutane da yawa za su zama masu adalci. 20 An ba da dokar don mu ga yadda laifi yake da girma. Amma da zunubi ya ƙaru, sai alheri ya ƙaru sosai, 21 domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.
In Other Versions
Romans 5 in the ANGEFD
Romans 5 in the ANTPNG2D
Romans 5 in the AS21
Romans 5 in the BAGH
Romans 5 in the BBPNG
Romans 5 in the BBT1E
Romans 5 in the BDS
Romans 5 in the BEV
Romans 5 in the BHAD
Romans 5 in the BIB
Romans 5 in the BLPT
Romans 5 in the BNT
Romans 5 in the BNTABOOT
Romans 5 in the BNTLV
Romans 5 in the BOATCB
Romans 5 in the BOATCB2
Romans 5 in the BOBCV
Romans 5 in the BOCNT
Romans 5 in the BOECS
Romans 5 in the BOGWICC
Romans 5 in the BOHCV
Romans 5 in the BOHLNT
Romans 5 in the BOHNTLTAL
Romans 5 in the BOICB
Romans 5 in the BOILNTAP
Romans 5 in the BOITCV
Romans 5 in the BOKCV
Romans 5 in the BOKCV2
Romans 5 in the BOKHWOG
Romans 5 in the BOKSSV
Romans 5 in the BOLCB
Romans 5 in the BOLCB2
Romans 5 in the BOMCV
Romans 5 in the BONAV
Romans 5 in the BONCB
Romans 5 in the BONLT
Romans 5 in the BONUT2
Romans 5 in the BOPLNT
Romans 5 in the BOSCB
Romans 5 in the BOSNC
Romans 5 in the BOTLNT
Romans 5 in the BOVCB
Romans 5 in the BOYCB
Romans 5 in the BPBB
Romans 5 in the BPH
Romans 5 in the BSB
Romans 5 in the CCB
Romans 5 in the CUV
Romans 5 in the CUVS
Romans 5 in the DBT
Romans 5 in the DGDNT
Romans 5 in the DHNT
Romans 5 in the DNT
Romans 5 in the ELBE
Romans 5 in the EMTV
Romans 5 in the ESV
Romans 5 in the FBV
Romans 5 in the FEB
Romans 5 in the GGMNT
Romans 5 in the GNT
Romans 5 in the HARY
Romans 5 in the HNT
Romans 5 in the IRVA
Romans 5 in the IRVB
Romans 5 in the IRVG
Romans 5 in the IRVH
Romans 5 in the IRVK
Romans 5 in the IRVM
Romans 5 in the IRVM2
Romans 5 in the IRVO
Romans 5 in the IRVP
Romans 5 in the IRVT
Romans 5 in the IRVT2
Romans 5 in the IRVU
Romans 5 in the ISVN
Romans 5 in the JSNT
Romans 5 in the KAPI
Romans 5 in the KBT1ETNIK
Romans 5 in the KBV
Romans 5 in the KJV
Romans 5 in the KNFD
Romans 5 in the LBA
Romans 5 in the LBLA
Romans 5 in the LNT
Romans 5 in the LSV
Romans 5 in the MAAL
Romans 5 in the MBV
Romans 5 in the MBV2
Romans 5 in the MHNT
Romans 5 in the MKNFD
Romans 5 in the MNG
Romans 5 in the MNT
Romans 5 in the MNT2
Romans 5 in the MRS1T
Romans 5 in the NAA
Romans 5 in the NASB
Romans 5 in the NBLA
Romans 5 in the NBS
Romans 5 in the NBVTP
Romans 5 in the NET2
Romans 5 in the NIV11
Romans 5 in the NNT
Romans 5 in the NNT2
Romans 5 in the NNT3
Romans 5 in the PDDPT
Romans 5 in the PFNT
Romans 5 in the RMNT
Romans 5 in the SBIAS
Romans 5 in the SBIBS
Romans 5 in the SBIBS2
Romans 5 in the SBICS
Romans 5 in the SBIDS
Romans 5 in the SBIGS
Romans 5 in the SBIHS
Romans 5 in the SBIIS
Romans 5 in the SBIIS2
Romans 5 in the SBIIS3
Romans 5 in the SBIKS
Romans 5 in the SBIKS2
Romans 5 in the SBIMS
Romans 5 in the SBIOS
Romans 5 in the SBIPS
Romans 5 in the SBISS
Romans 5 in the SBITS
Romans 5 in the SBITS2
Romans 5 in the SBITS3
Romans 5 in the SBITS4
Romans 5 in the SBIUS
Romans 5 in the SBIVS
Romans 5 in the SBT
Romans 5 in the SBT1E
Romans 5 in the SCHL
Romans 5 in the SNT
Romans 5 in the SUSU
Romans 5 in the SUSU2
Romans 5 in the SYNO
Romans 5 in the TBIAOTANT
Romans 5 in the TBT1E
Romans 5 in the TBT1E2
Romans 5 in the TFTIP
Romans 5 in the TFTU
Romans 5 in the TGNTATF3T
Romans 5 in the THAI
Romans 5 in the TNFD
Romans 5 in the TNT
Romans 5 in the TNTIK
Romans 5 in the TNTIL
Romans 5 in the TNTIN
Romans 5 in the TNTIP
Romans 5 in the TNTIZ
Romans 5 in the TOMA
Romans 5 in the TTENT
Romans 5 in the UBG
Romans 5 in the UGV
Romans 5 in the UGV2
Romans 5 in the UGV3
Romans 5 in the VBL
Romans 5 in the VDCC
Romans 5 in the YALU
Romans 5 in the YAPE
Romans 5 in the YBVTP
Romans 5 in the ZBP