1 Peter 4 (BOHCB)

1 Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3 Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4 Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. 5 Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu. 6 Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu. 7 Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa. 9 Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba. 10 Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam. 11 In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin. 12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku. 15 In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi. 16 Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna. 17 Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah? 18 Kuma,“In da ƙyar masu adalci su kuɓuta,me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?” 19 Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

In Other Versions

1 Peter 4 in the ANGEFD

1 Peter 4 in the ANTPNG2D

1 Peter 4 in the AS21

1 Peter 4 in the BAGH

1 Peter 4 in the BBPNG

1 Peter 4 in the BBT1E

1 Peter 4 in the BDS

1 Peter 4 in the BEV

1 Peter 4 in the BHAD

1 Peter 4 in the BIB

1 Peter 4 in the BLPT

1 Peter 4 in the BNT

1 Peter 4 in the BNTABOOT

1 Peter 4 in the BNTLV

1 Peter 4 in the BOATCB

1 Peter 4 in the BOATCB2

1 Peter 4 in the BOBCV

1 Peter 4 in the BOCNT

1 Peter 4 in the BOECS

1 Peter 4 in the BOGWICC

1 Peter 4 in the BOHCV

1 Peter 4 in the BOHLNT

1 Peter 4 in the BOHNTLTAL

1 Peter 4 in the BOICB

1 Peter 4 in the BOILNTAP

1 Peter 4 in the BOITCV

1 Peter 4 in the BOKCV

1 Peter 4 in the BOKCV2

1 Peter 4 in the BOKHWOG

1 Peter 4 in the BOKSSV

1 Peter 4 in the BOLCB

1 Peter 4 in the BOLCB2

1 Peter 4 in the BOMCV

1 Peter 4 in the BONAV

1 Peter 4 in the BONCB

1 Peter 4 in the BONLT

1 Peter 4 in the BONUT2

1 Peter 4 in the BOPLNT

1 Peter 4 in the BOSCB

1 Peter 4 in the BOSNC

1 Peter 4 in the BOTLNT

1 Peter 4 in the BOVCB

1 Peter 4 in the BOYCB

1 Peter 4 in the BPBB

1 Peter 4 in the BPH

1 Peter 4 in the BSB

1 Peter 4 in the CCB

1 Peter 4 in the CUV

1 Peter 4 in the CUVS

1 Peter 4 in the DBT

1 Peter 4 in the DGDNT

1 Peter 4 in the DHNT

1 Peter 4 in the DNT

1 Peter 4 in the ELBE

1 Peter 4 in the EMTV

1 Peter 4 in the ESV

1 Peter 4 in the FBV

1 Peter 4 in the FEB

1 Peter 4 in the GGMNT

1 Peter 4 in the GNT

1 Peter 4 in the HARY

1 Peter 4 in the HNT

1 Peter 4 in the IRVA

1 Peter 4 in the IRVB

1 Peter 4 in the IRVG

1 Peter 4 in the IRVH

1 Peter 4 in the IRVK

1 Peter 4 in the IRVM

1 Peter 4 in the IRVM2

1 Peter 4 in the IRVO

1 Peter 4 in the IRVP

1 Peter 4 in the IRVT

1 Peter 4 in the IRVT2

1 Peter 4 in the IRVU

1 Peter 4 in the ISVN

1 Peter 4 in the JSNT

1 Peter 4 in the KAPI

1 Peter 4 in the KBT1ETNIK

1 Peter 4 in the KBV

1 Peter 4 in the KJV

1 Peter 4 in the KNFD

1 Peter 4 in the LBA

1 Peter 4 in the LBLA

1 Peter 4 in the LNT

1 Peter 4 in the LSV

1 Peter 4 in the MAAL

1 Peter 4 in the MBV

1 Peter 4 in the MBV2

1 Peter 4 in the MHNT

1 Peter 4 in the MKNFD

1 Peter 4 in the MNG

1 Peter 4 in the MNT

1 Peter 4 in the MNT2

1 Peter 4 in the MRS1T

1 Peter 4 in the NAA

1 Peter 4 in the NASB

1 Peter 4 in the NBLA

1 Peter 4 in the NBS

1 Peter 4 in the NBVTP

1 Peter 4 in the NET2

1 Peter 4 in the NIV11

1 Peter 4 in the NNT

1 Peter 4 in the NNT2

1 Peter 4 in the NNT3

1 Peter 4 in the PDDPT

1 Peter 4 in the PFNT

1 Peter 4 in the RMNT

1 Peter 4 in the SBIAS

1 Peter 4 in the SBIBS

1 Peter 4 in the SBIBS2

1 Peter 4 in the SBICS

1 Peter 4 in the SBIDS

1 Peter 4 in the SBIGS

1 Peter 4 in the SBIHS

1 Peter 4 in the SBIIS

1 Peter 4 in the SBIIS2

1 Peter 4 in the SBIIS3

1 Peter 4 in the SBIKS

1 Peter 4 in the SBIKS2

1 Peter 4 in the SBIMS

1 Peter 4 in the SBIOS

1 Peter 4 in the SBIPS

1 Peter 4 in the SBISS

1 Peter 4 in the SBITS

1 Peter 4 in the SBITS2

1 Peter 4 in the SBITS3

1 Peter 4 in the SBITS4

1 Peter 4 in the SBIUS

1 Peter 4 in the SBIVS

1 Peter 4 in the SBT

1 Peter 4 in the SBT1E

1 Peter 4 in the SCHL

1 Peter 4 in the SNT

1 Peter 4 in the SUSU

1 Peter 4 in the SUSU2

1 Peter 4 in the SYNO

1 Peter 4 in the TBIAOTANT

1 Peter 4 in the TBT1E

1 Peter 4 in the TBT1E2

1 Peter 4 in the TFTIP

1 Peter 4 in the TFTU

1 Peter 4 in the TGNTATF3T

1 Peter 4 in the THAI

1 Peter 4 in the TNFD

1 Peter 4 in the TNT

1 Peter 4 in the TNTIK

1 Peter 4 in the TNTIL

1 Peter 4 in the TNTIN

1 Peter 4 in the TNTIP

1 Peter 4 in the TNTIZ

1 Peter 4 in the TOMA

1 Peter 4 in the TTENT

1 Peter 4 in the UBG

1 Peter 4 in the UGV

1 Peter 4 in the UGV2

1 Peter 4 in the UGV3

1 Peter 4 in the VBL

1 Peter 4 in the VDCC

1 Peter 4 in the YALU

1 Peter 4 in the YAPE

1 Peter 4 in the YBVTP

1 Peter 4 in the ZBP