1 Thessalonians 5 (BOHCB)
1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba. 4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi. 12 To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi. 13 Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 14 Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa. 15 Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu. 19 Kada ku danne aikin Ruhu. 20 Kada ku rena annabci, 21 amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau, 22 ku ƙi kowace mugunta. 23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata. 25 ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a. 26 Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki. 27 Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa. 28 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.
In Other Versions
1 Thessalonians 5 in the ANGEFD
1 Thessalonians 5 in the ANTPNG2D
1 Thessalonians 5 in the BBPNG
1 Thessalonians 5 in the BBT1E
1 Thessalonians 5 in the BNTABOOT
1 Thessalonians 5 in the BNTLV
1 Thessalonians 5 in the BOATCB
1 Thessalonians 5 in the BOATCB2
1 Thessalonians 5 in the BOBCV
1 Thessalonians 5 in the BOCNT
1 Thessalonians 5 in the BOECS
1 Thessalonians 5 in the BOGWICC
1 Thessalonians 5 in the BOHCV
1 Thessalonians 5 in the BOHLNT
1 Thessalonians 5 in the BOHNTLTAL
1 Thessalonians 5 in the BOICB
1 Thessalonians 5 in the BOILNTAP
1 Thessalonians 5 in the BOITCV
1 Thessalonians 5 in the BOKCV
1 Thessalonians 5 in the BOKCV2
1 Thessalonians 5 in the BOKHWOG
1 Thessalonians 5 in the BOKSSV
1 Thessalonians 5 in the BOLCB
1 Thessalonians 5 in the BOLCB2
1 Thessalonians 5 in the BOMCV
1 Thessalonians 5 in the BONAV
1 Thessalonians 5 in the BONCB
1 Thessalonians 5 in the BONLT
1 Thessalonians 5 in the BONUT2
1 Thessalonians 5 in the BOPLNT
1 Thessalonians 5 in the BOSCB
1 Thessalonians 5 in the BOSNC
1 Thessalonians 5 in the BOTLNT
1 Thessalonians 5 in the BOVCB
1 Thessalonians 5 in the BOYCB
1 Thessalonians 5 in the DGDNT
1 Thessalonians 5 in the GGMNT
1 Thessalonians 5 in the IRVM2
1 Thessalonians 5 in the IRVT2
1 Thessalonians 5 in the KBT1ETNIK
1 Thessalonians 5 in the MKNFD
1 Thessalonians 5 in the MRS1T
1 Thessalonians 5 in the NBVTP
1 Thessalonians 5 in the NIV11
1 Thessalonians 5 in the PDDPT
1 Thessalonians 5 in the SBIAS
1 Thessalonians 5 in the SBIBS
1 Thessalonians 5 in the SBIBS2
1 Thessalonians 5 in the SBICS
1 Thessalonians 5 in the SBIDS
1 Thessalonians 5 in the SBIGS
1 Thessalonians 5 in the SBIHS
1 Thessalonians 5 in the SBIIS
1 Thessalonians 5 in the SBIIS2
1 Thessalonians 5 in the SBIIS3
1 Thessalonians 5 in the SBIKS
1 Thessalonians 5 in the SBIKS2
1 Thessalonians 5 in the SBIMS
1 Thessalonians 5 in the SBIOS
1 Thessalonians 5 in the SBIPS
1 Thessalonians 5 in the SBISS
1 Thessalonians 5 in the SBITS
1 Thessalonians 5 in the SBITS2
1 Thessalonians 5 in the SBITS3
1 Thessalonians 5 in the SBITS4
1 Thessalonians 5 in the SBIUS
1 Thessalonians 5 in the SBIVS
1 Thessalonians 5 in the SBT1E
1 Thessalonians 5 in the SUSU2
1 Thessalonians 5 in the TBIAOTANT
1 Thessalonians 5 in the TBT1E
1 Thessalonians 5 in the TBT1E2
1 Thessalonians 5 in the TFTIP
1 Thessalonians 5 in the TGNTATF3T
1 Thessalonians 5 in the TNTIK
1 Thessalonians 5 in the TNTIL
1 Thessalonians 5 in the TNTIN
1 Thessalonians 5 in the TNTIP
1 Thessalonians 5 in the TNTIZ
1 Thessalonians 5 in the TTENT