Acts 15 (BOHCB)

1 Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.” 2 Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana. 3 Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai. 4 Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu. 5 Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.” 6 Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar. 7 Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata. 8 Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu. 9 Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya. 10 To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba? 11 A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.” 12 Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu. 13 Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni. 14 Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa. 15 Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa, 16 “ ‘Bayan wannan zan komain kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe.Kufansa zan sāke gina,in kuma mai da shi, 17 don ragowar mutane su nemi Ubangiji,kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana,in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’ 18 da aka sani tun zamanai. 19 “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah. 20 A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini. 21 Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.” 22 Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ’yan’uwa. 23 Tare da su suka aika da wannan wasiƙa.Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku.Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya.Gaisuwa. 24 Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce. 25 Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus  26 mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi. 27 Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta. 28 Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa. 29 Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa.Ku huta lafiya. 30 Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar. 31 Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa. 32 Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ’yan’uwa. 33 Bayan suka yi ’yan kwanaki a can, sai ’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su. 35 Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji. 36 Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.” 37 Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su, 38 amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba. 39 Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus, 40 amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji. 41 Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

In Other Versions

Acts 15 in the ANGEFD

Acts 15 in the ANTPNG2D

Acts 15 in the AS21

Acts 15 in the BAGH

Acts 15 in the BBPNG

Acts 15 in the BBT1E

Acts 15 in the BDS

Acts 15 in the BEV

Acts 15 in the BHAD

Acts 15 in the BIB

Acts 15 in the BLPT

Acts 15 in the BNT

Acts 15 in the BNTABOOT

Acts 15 in the BNTLV

Acts 15 in the BOATCB

Acts 15 in the BOATCB2

Acts 15 in the BOBCV

Acts 15 in the BOCNT

Acts 15 in the BOECS

Acts 15 in the BOGWICC

Acts 15 in the BOHCV

Acts 15 in the BOHLNT

Acts 15 in the BOHNTLTAL

Acts 15 in the BOICB

Acts 15 in the BOILNTAP

Acts 15 in the BOITCV

Acts 15 in the BOKCV

Acts 15 in the BOKCV2

Acts 15 in the BOKHWOG

Acts 15 in the BOKSSV

Acts 15 in the BOLCB

Acts 15 in the BOLCB2

Acts 15 in the BOMCV

Acts 15 in the BONAV

Acts 15 in the BONCB

Acts 15 in the BONLT

Acts 15 in the BONUT2

Acts 15 in the BOPLNT

Acts 15 in the BOSCB

Acts 15 in the BOSNC

Acts 15 in the BOTLNT

Acts 15 in the BOVCB

Acts 15 in the BOYCB

Acts 15 in the BPBB

Acts 15 in the BPH

Acts 15 in the BSB

Acts 15 in the CCB

Acts 15 in the CUV

Acts 15 in the CUVS

Acts 15 in the DBT

Acts 15 in the DGDNT

Acts 15 in the DHNT

Acts 15 in the DNT

Acts 15 in the ELBE

Acts 15 in the EMTV

Acts 15 in the ESV

Acts 15 in the FBV

Acts 15 in the FEB

Acts 15 in the GGMNT

Acts 15 in the GNT

Acts 15 in the HARY

Acts 15 in the HNT

Acts 15 in the IRVA

Acts 15 in the IRVB

Acts 15 in the IRVG

Acts 15 in the IRVH

Acts 15 in the IRVK

Acts 15 in the IRVM

Acts 15 in the IRVM2

Acts 15 in the IRVO

Acts 15 in the IRVP

Acts 15 in the IRVT

Acts 15 in the IRVT2

Acts 15 in the IRVU

Acts 15 in the ISVN

Acts 15 in the JSNT

Acts 15 in the KAPI

Acts 15 in the KBT1ETNIK

Acts 15 in the KBV

Acts 15 in the KJV

Acts 15 in the KNFD

Acts 15 in the LBA

Acts 15 in the LBLA

Acts 15 in the LNT

Acts 15 in the LSV

Acts 15 in the MAAL

Acts 15 in the MBV

Acts 15 in the MBV2

Acts 15 in the MHNT

Acts 15 in the MKNFD

Acts 15 in the MNG

Acts 15 in the MNT

Acts 15 in the MNT2

Acts 15 in the MRS1T

Acts 15 in the NAA

Acts 15 in the NASB

Acts 15 in the NBLA

Acts 15 in the NBS

Acts 15 in the NBVTP

Acts 15 in the NET2

Acts 15 in the NIV11

Acts 15 in the NNT

Acts 15 in the NNT2

Acts 15 in the NNT3

Acts 15 in the PDDPT

Acts 15 in the PFNT

Acts 15 in the RMNT

Acts 15 in the SBIAS

Acts 15 in the SBIBS

Acts 15 in the SBIBS2

Acts 15 in the SBICS

Acts 15 in the SBIDS

Acts 15 in the SBIGS

Acts 15 in the SBIHS

Acts 15 in the SBIIS

Acts 15 in the SBIIS2

Acts 15 in the SBIIS3

Acts 15 in the SBIKS

Acts 15 in the SBIKS2

Acts 15 in the SBIMS

Acts 15 in the SBIOS

Acts 15 in the SBIPS

Acts 15 in the SBISS

Acts 15 in the SBITS

Acts 15 in the SBITS2

Acts 15 in the SBITS3

Acts 15 in the SBITS4

Acts 15 in the SBIUS

Acts 15 in the SBIVS

Acts 15 in the SBT

Acts 15 in the SBT1E

Acts 15 in the SCHL

Acts 15 in the SNT

Acts 15 in the SUSU

Acts 15 in the SUSU2

Acts 15 in the SYNO

Acts 15 in the TBIAOTANT

Acts 15 in the TBT1E

Acts 15 in the TBT1E2

Acts 15 in the TFTIP

Acts 15 in the TFTU

Acts 15 in the TGNTATF3T

Acts 15 in the THAI

Acts 15 in the TNFD

Acts 15 in the TNT

Acts 15 in the TNTIK

Acts 15 in the TNTIL

Acts 15 in the TNTIN

Acts 15 in the TNTIP

Acts 15 in the TNTIZ

Acts 15 in the TOMA

Acts 15 in the TTENT

Acts 15 in the UBG

Acts 15 in the UGV

Acts 15 in the UGV2

Acts 15 in the UGV3

Acts 15 in the VBL

Acts 15 in the VDCC

Acts 15 in the YALU

Acts 15 in the YAPE

Acts 15 in the YBVTP

Acts 15 in the ZBP